• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

ALI KANO by ALI KANO
September 9, 2026
in Tsaro
A A
0
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Waɗanda ake zargin, Alhaji Jaye da Buba Bello, zaune a hannun jami'an tsaro

Waɗanda ake zargin, Alhaji Jaye da Buba Bello, zaune a hannun jami'an tsaro

Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS), wato Magireshin, ta kama wasu mutane biyu a Jihar Adamawa da ake zargi da kasancewa membobin wata ƙungiyar masu garkuwa da mutane, tare da ƙwato kuɗin fansa har Naira miliyan 34 a wani samame da ta gudanar a jihar.

Waɗanda ake zargin su ne Alhaji Jaye, mai shekara 55, da Buba Bello, mai shekara 34. An kama su ne a ranar 6 ga Satumba, 2026, bayan jami’an hukumar sun gudanar da wani samame.

A yayin fara yi musu tambayoyi, waɗanda ake tsare da su sun shaida wa jami’an shige da fice cewa kuɗin Naira miliyan 34 ɗin an tanade su ne domin biyan kuɗin fansa don a saki ɗan’uwan Buba Bello.

Kwanturola-Janar na Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya ya bayar da umurnin miƙa waɗanda ake zargin da kuɗin da aka ƙwato ga Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa domin su ci gaba da gudanar da bincike da ɗaukar matakan da suka dace.

Tarin kuɗin da aka kama

A wani samamen na daban, jami’an hukumar sun kuma tare wasu baƙin haure 17 da suka shiga Nijeriya ba bisa ƙa’ida ba a Rumde Baru, cikin Ƙaramar Hukumar Yola ta Kudu, bayan samun sahihan bayanan sirri.

An gano baƙin hauren ne a wani gida mai ɗakuna uku mallakar wani mutum. Binciken farko da aka gudanar ya nuna cewa 13 daga cikin su ’yan ƙasar Kamaru ne, waɗanda suka ƙunshi maza takwas da mata biyar, yayin da sauran huɗu ’yan ƙasar Chadi ne, dukkan su maza.

Baƙin haure da aka kama a Adamawa

Rundunar hukumar ta Adamawa ta ce za ta ci gaba da ƙarfafa tsarin kula da ƙaura, tsaron iyakokin ƙasa da kuma kare yankin ƙasa, tare da kira ga jami’an ta da su kasance cikin shiri da taka-tsantsan tare da bayar da bayanan sirri cikin lokaci kan sababbin barazanar tsaro da ke kunno kai.

👉 Ku biyo New Citizen Hausa domin samun ƙarin labarai.

Tags: Hukumar Kula da Shige da Fice ta Nijeriya (NIS)Magireshin
Previous Post

Asusun ajiyar kuɗaɗen wajen Nijeriya ya cika maƙil da dala biliyan 54, cika mafi yawa cikin shekaru 18 – CBN

Next Post

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

September 1, 2026
Tsaro

‘Yan sanda sun tabbatar da sace masallata a Neja

August 22, 2026
Next Post
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta'addanci

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!