Sabon bayanin da ya fito daga Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya nuna yadda asusun ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya haura zuwa dala biliyan $54.08, wanda hakan ya zama cika mafi yawa cikin kusan shekaru 18, tare da zarce hasashen da CBN ya yi na ƙarshen shekarar 2026.
Bayanan na CBN sun nuna cewa asusun ajiyar ya kai dala biliyan $54.08 a ranar 3 ga Satumba, idan aka kwatanta da dala biliyan $53.99 a ranar 2 ga Satumba da kuma dala biliyan $53.90 a ranar 1 ga Satumba.
Wannan sabon matsayi shi ne mafi girma da aka samu tun ranar 22 ga Disamban 2008, lokacin da asusun ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar ya kai ƙimanin dala biliyan $54.21.
Asusun ajiyar ya ƙaru da kusan dala biliyan $1.42 daga dala biliyan $52.66 da aka rattaba a ranar 19 ga Agusta.
Tun daga farkon shekarar nan ta 2026 zuwa yanzu, asusun ya ƙaru da ƙimanin dala biliyan $8.52, daga dala biliyan $45.56 a ranar 2 ga Janairu, wanda ke nuna ƙarin kaso 18.7 cikin 100 cikin sama da watanni takwas kacal.
Wannan sabon hauhawar asusun ajiyar kuɗaɗen waje ya biyo bayan ci gaba da ƙaruwar asusun ajiyar a watan Agusta, inda ya fara haura dala biliyan $53 a ranar 24 ga Agusta, lokacin da ya kai dala biliyan $53.11.
Daga bisani, ya kai dala biliyan $53.30 a ranar 26 ga Agusta, sannan dala biliyan $53.51 a ranar 28 ga Agusta, da kuma dala biliyan $53.81 a ranar 31 ga Agusta.
Asusun ajiyar ya tsaya kan dala biliyan $53.90 a ranar 1 ga Satumba, kafin daga bisani ya haura matakin dala biliyan $54 bayan kwana biyu.
Sabon matsayin ya kuma zarce hasashen CBN na dala biliyan $51.04 na asusun ajiyar kuɗaɗen waje zuwa ƙarshen shekarar 2026 da ƙimanin dala biliyan $3.04.
Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso, ya danganta ci gaba da ƙaruwar asusun ajiyar da ƙaruwar shigar kuɗaɗen musayar waje cikin ƙasar, ciki har da kudaden da ake samu daga haraji masu alaƙa da ɗanyen mai da kuma wasu kuɗaɗen da ke shigowa daga wasu ɓangarori na waje.
Ƙaruwar asusun ajiyar kuɗaɗen waje ta kuma zo daidai da ci gaba da ƙarfin naira a kasuwar musayar kuɗaɗen waje.
Rahoton ya nuna cewa naira ta ƙara daraja zuwa Naira 1,315 kan kowace dala a kasuwar hukuma a ranar Alhamis, wanda shi ne mafi ƙarfin matsayin ta cikin shekaru biyu.
Ƙaruwar asusun ajiyar kuɗaɗen waje na samar wa tattalin arzikin Nijeriya ƙarin kariya da damar tunkarar ƙalubalen kuɗaɗen waje, tare da ƙara wa CBN ƙarfin tabbatar da zaman lafiyar kasuwar musayar kuɗaɗen waje.






