Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya taya Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, murnar cika shekaru 60 da haihuwa, yana bayyana shi a matsayin amintaccen abokin aiki kuma jagoran da ya sadaukar da rayuwar sa wajen yi wa Jihar Borno da Najeriya hidima.
Shettima ya cika shekaru 60 a ranar Laraba, 2 ga Satumba, 2026.
A cikin saƙon taya murnar ranar haihuwar sa, Shugaba Tinubu ya kuma taya uwargidan Mataimakin Shugaban Ƙasa, Nana Shettima, da ’ya’yansa, sauran iyalan sa da abokan siyasar sa murnar wannan gagarumin lokaci.
Shugaban Ƙasar ya bayyana Shettima a matsayin ɗan kishin ƙasa mai jajircewa, haƙuri da sadaukar da kai, tare da yaba wa irin gudunmawar da ya bayar a fannoni daban-daban na rayuwar sa.
Tinubu ya musamman yaba wa rawar da Mataimakin Shugaban Ƙasar ya taka a harkar banki, da kuma irin jagorancin da ya bayar lokacin da yake Gwamnan Jihar Borno.
Ya ce Shettima ya nuna jajircewa, ƙwazo da tausayi wajen inganta rayuwar al’ummar Borno a lokacin da yake gwamna, sannan ya ci gaba da nuna waɗannan halaye a matsayin sa na Mataimakin Shugaban Ƙasar Nijeriya.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba masa bisa biyayyar sa ga jam’iyyar APC da kuma irin goyon bayan da yake bai wa Gwamnatin Tarayya wajen aiwatar da manufofin gwamnatin Renewed Hope.
A cewar Shugaban Ƙasar, Shettima, a matsayin sa na shugaban Majalisar Tattalin Arziki ta Ƙasa (NEC), ya taka muhimmiyar rawa wajen daidaita manufofin tattalin arziki da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi.
Ya ƙara da cewa mutunta kundin tsarin mulki, cibiyoyin dimokiraɗiyya, da kuma salon tattaunawa da tuntuɓar juna da Shettima ke nunawa, sun taimaka wajen ƙarfafa kyakkyawan shugabanci a ƙasar.
Tinubu ya gode wa Mataimakin Shugaban Ƙasar bisa amincin sa da cikakken goyon bayan da yake bayarwa, yana mai tabbatar da cewa za su ci gaba da aiki tare domin cika alƙawurran da gwamnatin Renewed Hope ta ɗauka ga ’yan Nijeriya.
Shugaban Ƙasar ya kuma yi wa Shettima addu’ar samun ƙoshin lafiya, hikima da tsawon rai, tare da roƙon Allah Ya ci gaba da shiryar da shi da kuma ba shi ikon yi wa Nijeriya hidima cikin nasara.







