• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa yayin da ya doshi dala tiriliyan ɗaya

WAKILIN MU by WAKILIN MU
September 1, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa yayin da ya doshi dala tiriliyan ɗaya
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Tattalin arzikin Nijeriya ya ci gaba da nuna alamun bunƙasa a zangon na biyu na shekarar 2026, inda aka samu ƙaruwar kashi 4.43 cikin 100 na Babban Haɗaɗɗen Kuɗin Shiga Ƙasa (GDP), a cewar Ma’aikatar Kuɗi ta Tarayya.

Wannan adadi ya zarce kashi 4.23 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2025, haka kuma ya haura kashi 3.89 cikin 100 da aka samu a zangon farko na shekarar 2026.

Ma’aikatar Kuɗin Tarayya ta bayyana cewa wannan ci gaba ya ɗaga matsakaicin bunƙasar tattalin arzikin ƙasar a farkon rabin shekarar 2026 zuwa kashi 4.16 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 3.68 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2025.

Ta kuma ce bunƙasar tattalin arzikin ta fara yaɗuwa zuwa sassa daban-daban na ƙasar, inda sassa 27 na tattalin arzikin suka samu bunƙasar da ta haura kashi uku cikin 100 a zangon na biyu na shekarar 2026, idan aka kwatanta da sassa 23 da suka samu irin wannan bunƙasar a shekarar da ta gabata.

A ɓangaren samar da kayayyaki, masana’antu sun samu bunƙasar kashi 3.24 cikin 100, daga kashi 1.60 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2025.

Haka kuma, ɓangaren noma ya bunƙasa da kashi 4.39 cikin 100, idan aka kwatanta da kashi 2.82 cikin 100 da aka samu a shekarar da ta gabata.

A gefe guda kuma, ɓangaren ayyuka, wanda shi ne mafi girman ɓangaren tattalin arzikin Nijeriya, ya samu bunƙasar kashi 4.60 cikin 100, daga kashi 3.94 cikin 100 da aka samu a makamancin lokacin shekarar 2025.

Ma’aikatar ta kuma bayyana cewa ƙarin darajar da naira ta samu, tare da daidaituwar kasuwar canjin kuɗaɗen waje, sun taimaka wajen ƙara darajar tattalin arzikin Nijeriya idan aka auna shi da dalar Amurka.

A cewar ma’aikatar, naira ta samu ƙarin daraja da sama da kashi 12 cikin 100 tsakanin farkon rabin shekarar 2025 da makamancin lokacin shekarar 2026. Wannan ya taimaka wajen ƙara darajar tattalin arzikin ƙasar da kusan kashi 17 cikin 100 idan aka auna shi da dalar Amurka.

Ma’aikatar Kuɗin Tarayya ta ce waɗannan alkaluma na nuna cewa Najeriya na kan turbar cimma burin Gwamnatin Tarayya na mayar da tattalin arzikin ƙasar zuwa dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030.

Ta ƙara da cewa Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF) ya sanya Nijeriya cikin ƙasashe 10 da ake sa ran za su fi bayar da gagarumar gudunmawa wajen bunƙasar tattalin arzikin duniya a shekarar 2026.

Sai dai gwamnati ta jaddada muhimmancin ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki domin tabbatar da cewa bunƙasar da ake samu ta kasance mai ɗorewa, tare da sauƙaƙa rayuwar talakawa da sauran ‘yan ƙasar.

Previous Post

Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 60

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!