• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da gangamin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
August 31, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da gangamin sama wa ƙwararrun ’yan Nijeriya aiki a ƙasashen waje
Ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati a taron manema labarai na ƙaddamar da kamfen ɗin “Hire for Nigeria” a ranar 31 ga Agusta, 2026, a Abuja. (Hoto daga: Khalid Ahmed/FMINO)

Ministoci da sauran manyan jami'an gwamnati a taron manema labarai na ƙaddamar da kamfen ɗin “Hire for Nigeria” a ranar 31 ga Agusta, 2026, a Abuja. (Hoto daga: Khalid Ahmed/FMINO)

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da wani shiri mai suna “Hire from Nigeria” (wato ‘A ɗauki ma’aikata daga Nijeriya’) domin bai wa ’yan ƙasar nan damar yi wa kamfanoni da masu ɗaukar ma’aikata na ƙasashen waje aiki.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a wani taron manema labarai da aka yi a ofishin sa a Abuja.

Ya ce: “Ƙaddamar da wannan shiri wani muhimmin mataki ne a ƙoƙarin da Nijeriya take yi na sanya ɗaya daga cikin manyan kadarorin ƙasar mu, wato mutanen mu, a sahun gaba wajen hulɗar tattalin arzikin mu da duniya.”

Ya ce yawan matasan Nijeriya, da ɗimbin ƙwararrun ma’aikatan ta da kuma bunƙasar fasahar zamani sun ba ƙasar damar yin gogayya da sauran ƙasashe a fagen tattalin arzikin duniya.

Idris ya ce: “Makomar tattalin arzikin Nijeriya za ta ƙara dogara ne kan ƙwarewa, ƙirƙire-ƙirƙire, fasaha da kuma ƙwazon jama’ar mu. A shirye Nijeriya take ta yi gogayya a fagen duniya. A shirye ƙwararrun ’yan Nijeriya suke su yi aiki, kuma ya kamata duniya ta mayar da hankali kan Nijeriya.”

Ya ƙara da cewa gangamin ya haɗa ma’aikatun tarayya na Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari da na Ilimi, NATEP, iDICE da kamfanoni masu zaman kan su domin haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu neman ƙwararrun ma’aikata a duniya.

Ya ce shirin ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da kuma burin Gwamnatin Tarayya na samar da guraben aiki miliyan ɗaya ta hanyar fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje.

“Ba sai matashi ɗan Nijeriya ya bar ƙasar ba kafin ya samu damar shiga harkokin tattalin arzikin duniya. Idan aka ba shi ƙwarewar da ta dace, ababen more rayuwa, ƙa’idojin sana’a da damar shiga kasuwanni, ’yan Nijeriya za su iya rayuwa, su yi aiki kuma su samu kuɗi a nan gida, yayin da suke samar da ayyuka ga abokan ciniki da masu ɗaukar ma’aikata a faɗin duniya,” inji shi.

Shi kuma Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce ma’aikatar sa tana inganta ƙwarewar ’yan Nijeriya ta hanyar inganta tsarin koyarwa, koyar da sana’o’i da dabarun fasahar zamani, da kuma horar da su bisa buƙatun masana’antu.

“Manufar Ma’aikatar Ilimi ita ce, a duk inda ake neman ma’aikata a duniya, muna son ’yan Nijeriya su samu horo, su samu takardar shaidar ƙwarewa kuma su kasance a shirye don a ɗauke su aiki,” inji shi.

A nata ɓangaren, Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole, ta ce gangamin zai taimaka wajen samar da ayyukan yi ga matasan Nijeriya, da ƙara fitar da ayyuka zuwa ƙasashen waje da jawo zuba jari.

“Shirin ‘Hire from Nigeria’ ya wuce kamfen na wayar da kai kawai; shiri ne na ƙasa da aka tsara domin bunƙasa tattalin arziki,” inji Oduwole.

 

Ta ce za a gabatar da kamfen ɗin a taron Majalisar Ɗinkin Duniya karo na 81, inda Nijeriya za ta bayyana fa’idar ɗaukar ’yan Nijeriya aiki ga masu ɗaukar ma’aikata na duniya.

 

Tun da farko, Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Sadarwa ta Dabaru da NATEP, Misis Olajumoke Dan-Okayi, ta ce shirin zai magance matsalolin da ke hana ƙwararrun ’yan Nijeriya samun damar aiki a duniya.

Ta ce: “Ba ƙwarewa ce matsalar ba, kuma ba buri ba ne. Matsalar ita ce yadda za a gano ƙwararrun ’yan Nijeriya, amincewa da su da kuma samun damar shiga kasuwannin duniya. Don haka, shirin ‘Hire from Nigeria’ yana da ayyuka uku masu sauƙi: ya sauƙaƙa wa duniya gano Nijeriya, ya sauƙaƙa amincewa da ƙwararrun ’yan Nijeriya, sannan ya sauƙaƙa ɗaukar ’yan Nijeriya aiki.”

Ana sa ran kamfen ɗin zai haɗa ƙwararrun ’yan Nijeriya da masu ɗaukar ma’aikata, kamfanoni masu neman ma’aikata, masu zuba jari da kasuwannin ƙasashen waje.

HOTO:

Daga hagu: Darakta-Janar na Hukumar Talbijin ta Nijeriya (NTA), Kwamared Salihu Abdulhamid Dembos; Shugaba kuma wanda ya kafa Tech4Dev, Joel Ogunsola; Ministan Ilimi, Dakta Maruf Olatunji Alausa; Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris; Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole; Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Sadarwar Jama’a, Sunday Dare; Darakta-Janar na FRCN, Dakta Mohammed Bulama; da Babbar Mataimakiya ta Musamman kan Sadarwa ta Dabaru da NATEP a Ofishin Ministar Masana’antu, Kasuwanci da Zuba Jari, Olajumoke Dan-Okayi, a wurin taron manema labarai na ƙaddamar da kamfen ɗin “Hire for Nigeria” a ranar 31 ga Agusta, 2026, a Abuja. (Hoto daga: Khalid Ahmed/FMINO)

Tags: Mohammed Idrissamar da aikiƙasashen waje
Previous Post

Nasarorin tattalin arziki: ‘Yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje sun aiko da dala miliyan 947 a Yuli – CBN

Next Post

Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 60

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 60

Tinubu ya taya Shettima murnar cika shekaru 60

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!