• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam

ALI KANO by ALI KANO
September 1, 2026
in Tsaro
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙara ɗaukar sabbin dabarun kawo ƙarshen rashin tsaro, yayin da Matawalle ya ziyarci Kano kan harin Garun Malam
Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a lokacin ziyarar a Kano ranar Litinin

Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf a lokacin ziyarar a Kano ranar Litinin

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada ƙudirin ta na kawo ƙarshen rashin tsaro a faɗin ƙasar nan, ta hanyar ƙara mayar da hankali kan gudanar da ayyukan tsaro cikin gaggawa, tsara dabarun tsaro na dogon lokaci da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa da gwamnatocin jihohi.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ta’aziyya da tantance halin da ake ciki da ya kai Jihar Kano a ranar Litinin, bayan harin da ‘yan bindiga suka kai ƙauyen Chiroma da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam a ranar 29 ga Agusta, 2026.

Matawalle, wanda ya ziyarci Fadar Gwamnatin Jihar Kano, ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta himmatu wajen kawo ƙarshen rashin tsaro da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a faɗin Nijeriya.

Ya ce Gwamnatin Tarayya na ƙaddamar da sabbin dabaru domin tunkarar ƙalubalen tsaro, ciki har da shirin samar da Tsarin Tsaro da Kare Ƙasa na tsawon shekaru biyar.

“Shugaban Ƙasa ya kafa wani kwamiti domin tsara Tsarin Tsaro da Kare Ƙasa na shekaru biyar. Wannan zai jagoranci tsarin mu na dogon lokaci wajen tunkarar barazanar tsaro a faɗin ƙasar,” inji ministan.

Ƙaramin Ministan Tsaro, Dakta Bello Muhammad Matawalle, tare da Gwamna Abba Kabir Yusuf jami’an soja a lokacin ziyarar a Kano ranar Litinin

Matawalle ya bayyana cewa bayan harin, Kwamandan Birged ta 3 da ke Kano, Birgediya Janar Jimoh, ya jagoranci wani samame na haɗin gwiwa domin ceto waɗanda aka yi garkuwa da su, tare da jami’an Rundunar Haɗin Gwiwa ta JTF daga sansanonin Hawan-Kwano da Kwanar Dangora.

Ya ce aikin ya yi nasarar ceto waɗanda aka yi garkuwa da su a yankunan gadar ‘Yankifi da Marabar Kwari da ke Ƙaramar Hukumar Garun Malam.

Ministan ya yaba wa dakarun saboda jajircewar su da kuma gaggawar da suka yi wajen mayar da martani, yana mai tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta ci gaba da ƙarfafa ƙarfin aiki na Rundunar Sojin Nijeriya da sauran hukumomin tsaro.

“Za mu ci gaba da yin duk mai yiwuwa domin tallafa wa hukumomin tsaron mu don tabbatar da cewa ƙasar mu tana cikin aminci. Ina tabbatar muku cewa nan ba da jimawa ba rashin tsaro zai zama tarihi, kuma dukkan mu za mu rayu cikin zaman lafiya da wadata,” inji shi.

Matawalle ya jaddada cewa samun nasara mai ɗorewa a yaƙi da rashin tsaro na buƙatar haɗin gwiwar kowane mataki na gwamnati da al’umma baki ɗaya.

“Yaƙi da wannan matsalar rashin tsaro na buƙatar haɗin gwiwar ƙananan hukumomi da gwamnatocin jihohi da kuma Gwamnatin Tarayya. Haka kuma muna buƙatar samun sahihan bayanai cikin lokaci daga jama’a zuwa hukumomin tsaro,” inji shi.

Ya kuma tabbatar wa gwamnatin Jihar Kano cewa Gwamnatin Tarayya za ta ƙara mata tallafi, ciki har da tura ƙarin motocin yaƙi, makamai da sauran kayan aiki domin ƙarfafa ayyukan tsaro a jihar.

Tun da farko, Matawalle ya gudanar da wani taron tsaro a ƙulle tare da kwamandojin Birged ta 3 da sauran rundunonin tsaro da ke Kano, inda ya umurce su da su ci gaba da ƙarfafa ayyukan da ake gudanarwa tare da ƙara ƙaimi wajen kare al’ummomi.

Ministan ya sake nanata ƙudirin Gwamnatin Tarayya na samar da dukkan kayan aiki da tallafin da ake buƙata domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a da kuma tabbatar da cikakken ikon Nijeriya kan yankunan ta.

A nasa jawabin, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya gode wa ministan bisa ziyarar da ya kai jihar, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya wajen yaƙi da rashin tsaro.

“Muna da cikakken yaƙini da jagorancin ku. A matakin jiha, za mu ci gaba da yin duk abin da ya kamata domin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a Kano,” in ji gwamnan.

“Mun ji ƙudirin Shugaban Ƙasa na tabbatar da tsaro a Nijeriya, kuma za mu tabbatar da cewa wannan annobar rashin tsaro ba ta ci gaba da zama a yankin mu.”

Tags: Bello Muhammad MatawalleGarun MalamGwamna Abba Kabir YusufKanotsaroziyara
Previous Post

Tattalin arzikin Nijeriya na ci gaba da bunƙasa yayin da ya doshi dala tiriliyan ɗaya

Next Post

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

Related Posts

Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya taya Kiristoci murnar bikin Ista
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta jajanta wa al’ummar Neja kan rasuwar mutane a Wushishi, ta bayar da umarnin bincike

September 18, 2026
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja
Tsaro

Gwamnatin Tarayya ta dakatar da Kwamandan NSCDC na Neja

September 18, 2026
Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa
Tsaro

Hukumar Shige da Fice ta kama wasu da ake zargi da satar mutane biyu, ta ƙwato Naira miliyan 34 a Adamawa

September 9, 2026
Tsaro

‘Yan sanda sun tabbatar da sace masallata a Neja

August 22, 2026
Next Post
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar 'yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!