Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi riƙo da koyarwar Annabi Muhammadu (SAW) ta hanyar kyautatawa, zaman lafiya da haɗin kai, tare da ƙin ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Idris ya yi wannan kiran ne a cikin saƙon sa na Maulidin Annabi a ranar Talata, inda ya taya Musulmi a faɗin Nijeriya da duniya murnar zagayowar ranar tare da yi musu fatan alheri.
Ministan ya ce wannan lokaci wata dama ce ta yin tunani kan rayuwar Annabi Muhammadu (SAW) da koyarwar sa, musamman saƙon sa na zaman lafiya, tausayi, haƙuri, adalci, tawali’u da girmama juna.
Ya ce waɗannan kyawawan halaye suna da matuƙar muhimmanci a daidai lokacin da Nijeriya take ci gaba da fuskantar sauye-sauye da farfaɗowar tattalin arziki.
Idris ya ce Gwamnatin Tarayya, ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ta himmatu wajen gina Nijeriya mai ƙarfi da wadata ta hanyar sauye-sauyen ƙarfafa tattalin arziki, inganta tsaro, zuba jari a ababen more rayuwa da faɗaɗa damar samun ilimi, koyon sana’o’i da kasuwanci.
Ya ce cigaban da ake samu yana buƙatar haƙuri, sadaukarwa da haɗin kan dukkan ’yan Nijeriya, inda ya buƙaci ’yan ƙasa da su ci gaba da mara wa ƙoƙarin gina ƙasa mai tsaro, kwanciyar hankali da wadata baya, tare da tabbatar da cewa ba a bar kowa a baya ba.
Ministan ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su tuna da marasa galihu, su kuma taimaka wa masu buƙata.
Ya yi addu’ar Allah ya sa wannan lokaci mai albarka ya ƙarfafa imanin Musulmi, ya ƙarfafa zaman lafiya da haɗin kai, tare da kawo albarka ga iyalai da al’ummomi.
Haka kuma, Idris ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa shugabannin ƙasar nan jagora, kuma ya sa Nijeriya ta samu zaman lafiya, tsaro da wadata mai ɗorewa.







