• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gangamin CBN a Lokoja: An samu raguwar hauhawar farashi da tumbatsar ajiyar kuɗaɗen waje, wanda adadin sa ya haura hasashen CBN

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
August 25, 2026
in Labarai
A A
0
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

A ci gaba rangadin gangamin wayar da kai da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ke yi a faɗin jihohi, bankin ya bayyana yadda hauhawar farashi ta ɗan ragu sakamakon tsauraran manufofin kuɗi da haɗaɗɗen tsarin canjin bai-ɗaya na kuɗin ƙasashen waje, tsakanin watan Yuni da Yuli na wannan shekara.

Gwamnan CBN Olayemi Cardoso ne ya bayyana haka, ta bakin Daraktar Riƙo a Sashen Sadarwa da Hulɗa da Masu Zuba Jari ta CBN, Hajiya Hakama Sidi-Ali.

Hakama ta bayyana hakan a ranar Alhamis yayin bikin ‘CBN Fair’ da aka gudanar a Lokoja, babban birnin Jihar Kogi.

An gudanar da taron ne ƙarƙashin taken: “Amfani da Hanyoyin Biyan Kuɗi na Zamani a Sinadaran Ƙara Yawan Mutanen da ke Amfani da Harkokin Kuɗi, Bunƙasa Tattalin Arziƙi da Hanzarta Ci gaban Ƙasa.”

Manufar wannan gangami ita ce jaddada muhimmancin haɗin gwiwar da ake buƙata domin samun daidaiton manufofin kuɗi, farashi da tsarin harkokin kuɗi.

A cewar Daraktar, bikin na daga cikin hanyoyin da CBN ya tsara domin hulɗa da jama’a da kuma wayar da su kan manufofi da shirye-shiryen bankin.

Ta ƙara da cewa, manufar bikin ita ce inganta ci gaba mai ɗorewa a tattalin arzikin ƙasa, tare da samar da damar jin ra’ayoyin masu ruwa da tsaki kan ƙarin hanyoyin inganta rayuwa da hanyoyin dogaro da kai ga ’yan Nijeriya.

Daraktar wadda Mista Zubairu Abdulrahman Salihu, Mai Kula da Reshen CBN na Lokoja, ya wakilta, ta bayyana cewa a ƙarƙashin jagorancin Olayemi Cardoso, shugabancin bankin ya ci gaba da tabbatar da daidaiton manufofin kuɗi da farashi, tare da gudanar da wasu muhimman ayyuka da suka fara haifar da sakamako mai kyau.

Hakama Sidi Ali ta ce raguwar hauhawar farashi, ci gaba da ƙaruwa da ajiyar kuɗaɗen waje da kuma daidaiton kasuwar canjin kuɗin waje a yanzu, na nuna cewa matakan da bankin ke ɗauka sun fara haifar da sakamako mai kyau.

Sai ta ce: “Sabbin bayanan Hukumar Kididdiga ta Ƙasa (NBS) sun nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki gabaɗaya ta ɗan ragu daga kashi 15.91 a watan Yuni 2026 zuwa kashi 15.43 a watan Yuli 2026.

“Haka kuma, hauhawar farashin kayayyakin abinci da sauran kayayyaki na game-gari ta ragu a wannan lokaci, abin da ke nuna tasirin tsauraran manufofin kuɗi, haɗaɗɗen tsarin canjin kuɗin waje da kuma ingantaccen bayyanar bayanai a kasuwa.

“Naira na ci gaba da samun ƙarfi, yayin da tazarar da ke tsakanin farashin canjin hukuma da na kasuwar ‘yan canji ta ragu da kashi biyu. Ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya na ci gaba da kasancewa sama da dala biliyan 52.5 na Amurka a watan Yuli 2026, abin da ya kai ta adadi mafi girma cikin shekaru 17, wanda da zarce hasashen shekara-shekara da CBN ya yi a baya.”

Saboda haka CBN ya yi kira ga ’yan Nijeriya da sauran mutane da su mutunta Naira tare da kiyaye tsaftar ta, tana mai jaddada cewa: “Kada a kekketa naira, kada a yi tallace-tallacen titi da ita, kada a lalata ta, kuma kada a buga jabun naira. Naira ta zamo kawai muhimmiyar alama ce ta ƙasa ba, har ila yau alfarmar mu ce ta bai-ɗaya a matsayin al’umma.”

Tun da farko, Mai Kula da Reshen CBN na Lokoja, wanda Mista Friday Abah ya wakilta, ya bayyana cewa Jihar Kogi tana cikin kyakkyawan matsayi na cin moriyar damar da harkokin kuɗi na zamani ke samarwa, kasancewar jihar wata babbar hanyar zirga-zirga da ta haɗa Arewacin Nijeriya da Kudancin ƙasar, tare da kasancewar ta cibiyar kasuwanci da ke tasowa.

Ya ce: “Don haka, ina ƙarfafa ’yan kasuwa, manoma, masu sana’o’i, ɗalibai, masu harkokin kasuwanci da sauran jama’a da su yi cikakken amfani da bayanai, nune-nunen ayyuka da tattaunawar da ake gudanarwa a yayin wannan taro.”

A nasa ɓangaren, Gwamnan Jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo, ya bayyana ‘CBN Fair’ a matsayin wani abu da ya wuce tattaunawa kan fasahar banki ko hanyoyin biyan kuɗi, domin ya shafi jama’a da ci gaba.

Gwamnan ya yi alƙawarin tallafa wa shirye-shiryen da za su inganta ilimin jama’a kan harkokin kuɗi na zamani, faɗaɗa damar samun ayyukan kuɗi a yankunan karkara, bunƙasa ƙanana da matsakaitan masana’antu (MSMEs), samar da kuɗaɗen tallafin noma, ƙarfafa harkokin kasuwancin matasa, inganta mu’amalolin gwamnati ta hanyar dijital da kuma kare haƙƙin masu amfani da ayyukan kuɗi.

Tags: CBNgangamiLokoja
Previous Post

Maulidi: Tinubu na so Musulmi su yi koyi da koyarwar Annabi (SAW)

Next Post

Maulidi: Minista ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi koyi da koyarwar Annabi Muhammadu (SAW)

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Martanin Nijeriya ga Amurka: Muna nan daram, muna samun cigaba a fannin tsaro

Maulidi: Minista ya yi kira ga ’yan Nijeriya da su yi koyi da koyarwar Annabi Muhammadu (SAW)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!