Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya yi gargaɗin cewa duk wani yunƙuri na dawo da tallafin man fetur zai iya mayar da nasarorin tattalin arzikin da Nijeriya ta samu tun bayan cire tallafin a shekarar 2023 baya.
Idris ya ce kiraye-kirayen dawo da tallafin man fetur da ake yi a yanzu na buƙatar a yi la’akari da illolin da hakan zai haifar ga tattalin arziki da kuma kuɗaɗen gwamnati.
Ya tunatar da cewa Nijeriya ta kashe kusan dala biliyan 10 wajen tallafin man fetur a shekarar 2022, a lokacin da ƙasar ke fama da raguwar hako ɗanyen mai da kuma ƙarancin kuɗaɗen shiga.
Ya ce Bankin Duniya ya kuma yi gargaɗin cewa tallafin na cinye kuɗaɗen da da an iya karkatar da su zuwa harkokin ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da kuma tallafa wa marasa ƙarfi.
Ministan ya ce gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta gaji wannan tsarin, kuma ta ɗauki matakin yin garambawul a cikinsa domin tabbatar da ɗorewar tattalin arzikin ƙasar nan gaba.
Idris ya ce bayanan da gwamnatin tarayya ta fitar kwanan nan a cikin rahoton Nigeria’s Reform Scorecard: The Benefits, Costs and Harms Prevented sun nuna cewa kuɗaɗen da aka samu sakamakon cire tallafin sun samar da naira tiriliyan 15.8 ga Tarayya tsakanin watan Yunin 2023 da Disambar 2025.
Ya bayyana cewa daga cikin wannan kuɗi, kusan naira tiriliyan 5.43 sun tafi ga Gwamnatin Tarayya, yayin da jihohi suka samu naira tiriliyan 6.52, ƙananan hukumomi kuma suka samu naira tiriliyan 3.88.
Sai dai ministan ya bayyana cewa bai kamata a fahimci naira tiriliyan 15.8 ɗin a matsayin kuɗin da ke zaune a wani asusun gwamnati na musamman da ake kira “kuɗaɗen da aka tanada daga tallafi” ba.
A maimakon haka, ya ce adadin yana wakiltar kuɗaɗen da aka saki a cikin tsarin kuɗaɗen gwamnati, waɗanda aka samar da damar rarrabawa tsakanin matakan gwamnati uku.
A cewarsa, ƙarin kuɗaɗen da jihohi da ƙananan hukumomi suka samu ya ƙarfafa musu damar biyan albashi da fansho, tare da zuba jari a harkokin kiwon lafiyar matakin farko, ilimin bai-daya, tituna da sauran muhimman ayyuka.
A matakin tarayya kuwa, ya ce faɗaɗar damar kashe kuɗaɗen gwamnati da sauye-sauyen suka haifar ta taimaka wajen gudanar da manyan ayyuka da nauyin gwamnati waɗanda da wuya a iya ɗaukar su a ƙarƙashin tsohon tsarin tallafin.
Idris ya ce rahoton Reform Scorecard ya nuna cewa an kashe kusan naira tiriliyan 6.47 a ƙarin kuɗaɗen ayyukan more rayuwa na manyan tsare-tsare, waɗanda suka haɗa da harkokin sufuri, gidaje, noma, tsaro da sauran ayyukan ƙasa.
Ya lissafa Babbar Hanyar Lagos zuwa Calabar, Babbar Hanyar Sokoto zuwa Badagry da Trans-Sahara Superhighway cikin manyan ayyukan da suka amfana da ƙarin damar kuɗaɗen da aka samu.
Ministan ya kuma ce sauye-sauyen sun samar da damar ƙara zuba jari a harkokin bunƙasa ɗan Adam da tallafin jinƙai, inda sama da gidaje miliyan 10 suka amfana da tallafin kuɗi.
Ya ƙara da cewa gwamnatin ta ware sama da naira biliyan 400 ga wasu manyan shirye-shiryen tallafin jama’a, ciki har da naira biliyan 223.8 ga Asusun Ba da Lamunin Ilimi na Nijeriya (NELFUND), naira biliyan 150 ga Asusun Zuba Jari a Gidaje na MOFI (MREIF), da naira biliyan 50 ga Kamfanin Ba da Lamunin Amfani na Nijeriya (CREDICORP).
Idris ya ce sauye-sauyen sun kuma taimaka wajen ƙara amincewar masu zuba jari a cikin gida da wajen ƙasa, inda ya ce kasuwar hannayen jarin Nijeriya ta zama kasuwar da ta fi kowacce a duniya samun kyakkyawan aiki a shekarar 2026.
Ya kuma ce ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar ya kai matsayi mafi girma cikin kusan shekaru 20, yayin da hako ɗanyen mai ya ƙaru har ya zarce adadin da OPEC ta ware wa Nijeriya a karon farko cikin shekaru.
A cewarsa, ƙarin damar kuɗaɗen gwamnati ya taimaka wajen biyan ƙarin albashi, aiwatar da mafi ƙarancin albashi da kuma biyan fansho, tare da faɗaɗa damar gwamnati wajen saka hannun jari a ilimi, kiwon lafiya, noma, wutar lantarki, tsaro da sauran muhimman sassa.
Ya ce Nijeriya tana kuma shiga wani sabon zamani a ɓangaren man fetur, sakamakon ƙaruwa mai yawa a ƙarfin tace ɗanyen mai a cikin gida.
Sai dai Idris ya yi gargaɗin cewa sauya wannan manufa a yanzu na iya durƙusar da ci gaban da aka samu a ɓangaren man fetur, tare da haifar da rashin tabbas ga masu zuba jari a lokacin da ya kamata ƙasar ta ƙara ƙarfafa tace man fetur a cikin gida da kuma samar da wadataccen makamashi.
Ministan ya ce rahoton Reform Scorecard ya kuma yi hasashen irin matsalolin tattalin arzikin da Nijeriya za ta iya fuskanta da a ce ba a yi wa tsarin tallafin garambawul ba.
A cewarsa, ƙarancin man fetur zai iya sake dawowa, inda farashin lita ɗaya zai iya haura naira 3,000 a kasuwar bayan fage.
Ya ƙara da cewa bashin da gwamnatin baya ta tara ta hanyar Ways and Means, wanda ya kai kusan naira tiriliyan 30 a watan Mayun 2023 kuma tun daga lokacin aka rage shi, zai iya ninkawa ya kai naira tiriliyan 60 ko fiye.
Idris ya ce matsalolin kuɗaɗen da wasu jihohi ke fuskanta za su ƙara tsananta, yana mai cewa halin da aka gada na jihohi 27 da ke fama da matsalar biyan albashi yadda ya kamata zai ƙara muni ba tare da sauye-sauyen ba.
Ya kuma jawo hankali kan kuɗaɗen tallafin wutar lantarki, inda ya ce Nijeriya ta kashe naira tiriliyan 3.14 wajen tallafin wutar lantarki tsakanin Yunin 2023 da Disambar 2025.
Ministan ya yi hujjar cewa sake dawo da tallafin man fetur, yayin da ake ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki, zai ƙara jefa kuɗaɗen ƙasar cikin matsin lamba.
Ya ce dawo da tallafin man fetur zai mayar da Nijeriya kusan zuwa yanayin tattalin arzikin shekarar 2022, wanda ke tattare da matsin lamba kan kuɗaɗen gwamnati, karkatar da tsarin kasuwa, ƙarancin man fetur da kuma damar yin cinikin riba ta hanyar banbancin farashi.
Ministan ya amince cewa sauye-sauyen sun jawo wa ’yan Nijeriya wahalhalu masu yawa kuma har yanzu ba su magance dukkan matsalolin tattalin arzikin ƙasar ba.
Sai dai ya ce abin da ya dace shi ne a ƙara sauri wajen tabbatar da amfanin sauye-sauyen, maimakon a mayar da su baya.
Ya ce: “Ba muna cewa sauye-sauyen sun magance dukkan ƙalubalen tattalin arzikin Nijeriya ba; har yanzu akwai sauran ayyuka da yawa da ya kamata a yi domin sauya ƙarin damar kuɗaɗen gwamnati zuwa ingantattun ayyuka, samar da guraben aiki, ababen more rayuwa da inganta rayuwar jama’a.”
Ya ce manufar sauye-sauyen ita ce karkatar da kuɗaɗen gwamnati daga tallafa wa amfani da kayayyaki zuwa zuba jari ga ’yan Nijeriya da kuma ginshiƙan samar da ci gaban tattalin arziki na dogon lokaci.
Idris ya kuma bayyana batun dawo da tallafin a matsayin zaɓi tsakanin muhimman abubuwa daban-daban, yana tambayar ko ya kamata ƙasar ta dawo da tallafin man fetur ne a maimakon ci gaba da tallafa wa lamunin karatu, ba da lamunin amfani ga matasa, ƙara wa jihohi da ƙananan hukumomi rabon kuɗaɗe, gina ababen more rayuwa, samar da wutar lantarki, tsaro, kiwon lafiya, ilimi da tallafawa marasa ƙarfi.
Ya ce ƙungiyoyin ’yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki a harkokin tattalin arziki sun kuma yi gargaɗin cewa bai kamata a mayar da sauye-sauyen baya ba, yana mai cewa ɗorewar kuɗaɗen gwamnati, tabbas a manufofi da kuma kasuwar man fetur mai gasa na da muhimmanci wajen jawo zuba jari, samar da ayyukan yi da bunƙasa tattalin arziki.
“Nijeriya ba za ta iya gina tattalin arzikin gobe ta hanyar komawa tsarin tallafin jiya wanda ba ya ɗorewa ba. Mun wuce wannan tsarin,” in ji ministan.
Ya tabbatar wa ’yan Nijeriya cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da mayar da hankali wajen sauya wahalhalun da sauye-sauyen suka haifar zuwa ingantacciyar rayuwa, ingantattun ayyukan gwamnati da kuma ƙarin damar tattalin arziki ga jama’a.







