Fadar Shugaban Ƙasa tana sake nazarin jerin sunayen membobin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC ta 2027, sakamakon wasu kurakurai da aka gano a cikin jerin sunayen, waɗanda ake ganin za su iya jefa yaƙin neman zaɓen cikin abin kunya, inji wani rahoto.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito wata majiya ta faɗa mata cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta sake nazarin jerin sunayen bayan da aka fitar da shi a ranar Asabar, inda ya jawo ce-ce-ku-ce daga cikin jam’iyyar da kuma wajen jam’iyyar.
Wasu daga cikin masu sharhi da ‘yan jam’iyyar sun nuna damuwa kan abin da suka bayyana a matsayin cire wasu muhimman mutane daga cikin jerin, tare da saka wasu sunaye da ake ganin bai kamata a saka ba, inji jaridar.
A tsarin da aka bayyana da farko dai an ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne zai jagoranci majalisar, yayin da Mataimakin sa, Kashim Shettima, da Shugaban APC na Ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, za su kasance Mataimakan Shugaban Majalisar na I da na II.
Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Sanata Abdul’aziz Yari, zai zama Darakta-Janar na majalisar, yayin da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodimma, zai kasance Sakataren majalisar.
Majiyoyi daga cikin APC sun shaida wa Daily Trust cewa Fadar Shugaban Ƙasa ta fara aikin gyara jerin sunayen ne saboda an gano wasu abubuwa da ka iya aika saƙon da bai dace ba game da yadda aka tsara majalisar.
Daga cikin batutuwan da suka jawo ce-ce-ku-ce akwai shigar da wasu mutane da ake zargin suna fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa, da kuma rashin saka wasu mutane da ake ganin ƙwarewar su da gogewar su za su iya taimakawa wajen gudanar da yaƙin neman zaɓen.
Haka kuma, an gano cewa ba a saka wasu sunayen ba bisa kuskure kawai.
Majiyoyi daban-daban daga Fadar Shugaban Ƙasa da APC sun tabbatar wa da jaridar cewa har yanzu ba a bayyana ranar rantsar da majalisar ba, saboda ana buƙatar kammala aikin sake tsara jerin membobin.
Sai dai alamu na nuna cewa gyaran ba zai shafi shugabannin majalisar ba, musamman Darakta-Janar da Sakataren ta.
Wata majiya mai matuƙar kusanci da Fadar Shugaban Ƙasa ta shaida wa wani wakilin jaridar cewa shugabancin majalisar zai ci gaba da kasancewa yadda aka tsara shi, yayin da za a yi sauye-sauye ne kawai a cikin jerin membobin, ta hanyar cire wasu sunaye da kuma ƙara wasu.
Binciken jaridar ya nuna cewa jerin sunayen na farko na fama da manyan matsaloli guda uku, na farko shi ne shigar da sunayen wasu mutane da ake zargin suna da alaƙa da shari’o’in cin hanci da rashawa.
Na biyu shi ne cire wasu mutane da ake ganin ya kamata a saka su saboda gogewar su da ƙwarewar su. Na uku kuma shi ne cire wasu sunaye sakamakon kuskuren da aka yi wajen tattara ko tsara jerin sunayen.
Ana sa ran za a fitar da sabon tsarin membobin Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC ta 2027 bayan an kammala gyare-gyaren da ake yi.







