
Gyaran komaɗar tattalin arziki na gwamnatin Tinubu ya magance matsalar biyan albashi a jihohi 27
.
.
A watan Mayu 2023, lokacin da gwamnatin Tinubu ta hau mulki, jihohi 27 daga cikin 36 na Nijeriya na fuskantar matsaloli wajen biyan albashin ma’aikatan su. Sai dai bayan shekaru uku, lamarin ya sauya, inda a halin yanzu babu wata jiha da ke kasa biyan albashin ma’aikatan ta, bisa alkaluman da gwamnatin tarayya ta fitar a cikin rahoton “Nigeria’s Reform Scorecard.”
An ce wannan sauyi ya samo asali ne daga wasu manyan matakan gyaran tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, ciki har da cire tallafin man fetur da kuma sake fasalin tsarin kasuwar canjin kudaden waje.
Tsakanin Yuni 2023 da Disamba 2025, an samu tanadin Naira tiriliyan 15.8 sakamakon cire tallafin man fetur, inda daga cikin kudaden da aka samu aka raba Naira tiriliyan 10.4 ga jihohi da kananan hukumomi.
Karin kuɗaɗen da jihohi suka samu ya kara musu ƙarfin gudanar da ayyukan su, musamman wajen biyan albashi da daukar nauyin ayyukan raya ƙasa.
A matakin Gwamnatin Tarayya kuma, an ware Naira tiriliyan 9.39 domin biyan karin albashi, aiwatar da sabon mafi karancin albashi da kuma wasu alawus-alawus ga ma’aikatan gwamnati.
Matakan sun kuma taimaka wajen samar da karin kuɗaɗen da suka bai wa gwamnati damar ƙara mafi ƙarancin albashin ma’aikata daga N30,000 zuwa N70,000.
Waɗannan alƙaluma na nuna cewa tasirin gyare-gyaren tattalin arziki bai tsaya ga bayanan kuɗi da kididdigar gwamnati kawai ba, illa ya shafi rayuwar ma’aikata da iyalansu kai-tsaye.
Duk da haka, har yanzu akwai ƙalubalen tsadar rayuwa da kuma buƙatar ƙara inganta walwalar jama’a. Sai dai sauyin da aka samu daga jihohi 27 da ke fama da matsalar biyan albashi a shekarar 2023 zuwa yanzu da babu wata jiha da ke fuskantar irin wannan matsala na daga cikin muhimman alamomin da ke nuna ƙoƙarin sake gina tattalin arzikin Nijeriya.
Yanzu babban kalubalen shi ne tabbatar da cewa amfanin waɗannan gyare-gyare ya wuce matakin gwamnati da ma’aikata, ya kuma isa ga talakawa ta hanyar rage musu radadin tsadar rayuwa da inganta yanayin rayuwar su.






