• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu: Iƙirarin dawo da tallafin mai na nuna jahilci kan shugabanci da tattalin arziki

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 20, 2026
in Siyasa
A A
0
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ce kiran da wasu ‘yan siyasa ke yi na a dawo da tallafin man fetur ya samo asali ne daga “jahilci mai tsanani kan shugabanci da tattalin arziki.”

Tinubu ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis lokacin da Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya kai masa ziyara a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shugaban ya ce kafin zuwan sa kan mulki, jihohi 27 ba sa iya biyan albashin ma’aikatansu, balle kuma biyan kuɗaɗen fansho.

Ya bayyana albashin ma’aikata a matsayin muhimmin ginshiƙi wajen tafiyar da tattalin arzikin jihohi, saboda albashin na taimaka wa iyalai da kuma ƙara yawan kuɗin da ake kashewa a cikin tattalin arzikin ƙasa.

A cewar sa, cire tallafin man fetur ya bai wa gwamnati damar ƙara yawan kuɗaɗen da take rabawa da amfani da su wajen gudanar da ayyukan raya ƙasa, ciki har da gina hanyoyi, gidaje, makarantu da asibitoci.

Tinubu ya ƙara da cewa matakin ya kuma taimaka wajen farfaɗo da harkokin kiwon lafiya da kuma horar da malamai da ma’aikatan lafiya.

Shugaban ya kuma taya Adeleke murnar nasarar da ya samu a zaɓen gwamnan Jihar Osun, yana mai cewa al’ummar jihar sun sake zaɓar sa ne domin ya ci gaba da jagorantar su.

Ya buƙaci ‘yan siyasa su mutunta sakamakon zaɓe tare da mayar da hankali wajen gina haɗin kai da ci gaban al’umma.

“Ba galaba ka yi a kan kowa ba, ka ci zaɓe ne. Wannan shi ne ainihin dimokiraɗiyya,” inji shi.

Previous Post

Fadar Shugaban Ƙasa ta soki Atiku kan alƙawarin dawo da tallafin man fetur

Next Post

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!