• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Tinubu na so a yi zaɓen Osun cikin lumana da adalci

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 14, 2026
in Siyasa
A A
0
Tinubu ya umurci ICPC da ta binciki ‘hukumar bogi’, ta gabatar da rahoto cikin kwana 30
Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kira ga Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kan ta ta Ƙasa (INEC) da jami’an tsaro da su tabbatar da an gudanar da zaɓen gwamnan Jihar Osun cikin lumana da tsare gaskiya.

Al’ummar Jihar Osun za su fito rumfunan zaɓe a gobe Asabar, 15 ga Agusta 2026, domin zaɓen wanda zai jagoranci jihar, inda ‘yan takara 15 ke neman kujerar gwamnan.

Daga cikin ‘yan takarar akwai gwamnan jihar mai ci, Ademola Adeleke, na jam’iyyar PDP, da ɗan takarar jam’iyyar APC, Asiwaju Munirudeen Bola Oyebamiji, da kuma ɗan takarar jam’iyyar ADC, Honarabul Najeem Salaam.

Tinubu ya buƙaci masu zaɓe a jihar da su fito su gudanar da haƙƙin da ya rataya a wuyan su na ‘yan ƙasa cikin lumana, tare da guje wa duk wani abu da zai iya kawo cikas ga gudanar da zaɓen.

Ya ce INEC tana da alhakin tabbatar da cewa zaɓen ya gudana cikin tsari, gaskiya, ’yanci da adalci, yana mai buƙatar hukumar ta tabbatar da amincin tsarin zaɓen.

Shugaban Ƙasar ya ce zaɓen Osun shi ne na ƙarshe cikin zaɓukan da ake gudanarwa ba tare da haɗa su da sauran zaɓuka ba kafin babban zaɓen 2027, don haka ya kamata INEC ta yi amfani da shi wajen nuna wa ’yan Nijeriya shirin ta na gudanar da zaɓuka masu inganci.

Haka kuma Shugaban ya buƙaci Sufeto-Janar na ’Yan Sanda da shugabannin sauran hukumomin tsaro da ke cikin aikin zaɓen da su samar da cikakken tsaro a rumfunan zaɓe domin hana masu tayar da hankali kawo cikas ga tsarin.

Ya jaddada cewa dole ne a kare jami’an zaɓe da masu kaɗa ƙuri’a domin su gudanar da ayyukan su ba tare da tsoro ko barazana ba.

Shugaban ya buƙaci masu zaɓe da su fito da yawa domin zaɓar ɗan takarar da suke so, yana mai cewa an ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da gudanar da zaɓen cikin lumana, ’yanci da adalci.

Tinubu ya ce sakamakon zaɓen gwamnan Osun dole ne ya kasance abin da ya bayyana ra’ayin al’ummar jihar.

Tags: Bola TinubugwamnaOsunzaɓe
Previous Post

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar tashoshin jiragen ruwa ta 2026

Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin rasuwar Garkuwan Kontagora Ibrahim Wali

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post

Ministan Yaɗa Labarai ya yi alhinin rasuwar Garkuwan Kontagora Ibrahim Wali

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!