• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Saturday, November 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Hukumar ilimi ta N-SUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 a Neja

WAKILIN MU by WAKILIN MU
August 14, 2026
in Labarai
A A
0
Hukumar ilimi ta N-SUBEB za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 a Neja
Babban Memba na II a N-SUBEB, Hon. Muhammad Mudi, yana jawabi a madadin shugaban hukumar, Dakta Liman Alhaji Ibrahim, a taron

Babban Memba na II a N-SUBEB, Hon. Muhammad Mudi, yana jawabi a madadin shugaban hukumar, Dakta Liman Alhaji Ibrahim, a taron

Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya ta Jihar Neja (N-SUBEB) ta ce za ta dasa bishiyoyi a makarantu 150 da ke faɗin jihar, a wani mataki na rage illolin sauyin yanayi da zaizayar ƙasa da ke barazana ga wasu makarantu.

Shugaban hukumar, Dakta Liman Alhaji Ibrahim, ya bayyana hakan ne yayin wani horo na matakin jiha kan shirin Greening Schools and Climate Change Initiatives (GSCCI) da aka gudanar a zauren taro na N-SUBEB da ke Minna.

Dakta Ibrahim, wanda Babban Memba na II a hukumar, Hon. Muhammad Mudi, ya wakilta, ya ce nufin shirin shi ne samar da makarantu masu aminci da tsafta, tare da inganta yanayin koyo da koyarwa da kuma rage matsalolin muhalli da al’ummomi ke fuskanta.

Ya ce makarantu da dama a jihar suna fuskantar barazanar guguwar iska, zaizayar ƙasa da tsananin zafi, waɗanda ke kawo cikas ga harkokin ilimi tare da lalata gine-ginen makarantu.

Shugaban ya bayyana cewa shirin GSCCI bai taƙaita ga dasa bishiyoyi kawai ba, domin ya kuma ƙunshi shigar da ilimin sauyin yanayi cikin tsarin koyarwa a makarantun firamare.

Ya ce an shirya horon ne domin bai wa jami’an ilimi, shugabannin makarantu da jami’an kula da muhalli ilimi da dabarun da za su taimaka wajen aiwatar da shirin yadda ya kamata a matakin ƙananan hukumomi.

Mahalartan taron

Ya buƙaci mahalarta horon da su ɗauki shirin da muhimmanci, tare da tabbatar da cewa an kula da bishiyoyin da za a dasa a makarantu har sai sun yi ƙarfi kuma sun girma yadda ya kamata.

Dakta Ibrahim ya ƙara da cewa hukumar ta N-SUBEB za ta ci gaba da haɗin gwiwa da Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Neja, Ma’aikatar Aikin Gona, abokan hulɗar cigaba da sauran hukumomin da abin ya shafa domin tabbatar da nasarar shirin.

Tun da farko, sai da Sakatariyar Zartarwa ta Hukumar Ilimin Bai-Ɗaya ta Ƙasa (UBEC), Dakta Aisha Garba, ta bayyana horon a matsayin wani muhimmin mataki na sauye-sauyen da Gwamnatin Tarayya take aiwatarwa a fannin ilimi domin sake fasalin makarantu yadda za su iya fuskantar ƙalubalen muhalli da sauyin yanayi.

Dakta Aisha Garba, wadda Ko’odinetan UBEC na Jihar Kebbi, Dakta Aliyu Cheche, ya wakilta, ta ce tsarin ilimi ya kamata ya samar wa ɗalibai ilimi, ƙwarewa, ɗabi’u da halayen da za su taimaka wajen gina makoma mai ɗorewa da kuma jure wa illolin sauyin yanayi.

Ta buƙaci jami’an ilimi na jihohi da ƙananan hukumomi, masu kula da shirin a jihohi, shugabannin makarantu da masu horaswa da su yi aiki kafaɗa da kafaɗa da UBEC da tawagar fasaha domin tabbatar da nasarar aiwatar da shirin a faɗin ƙasa.

Horarwar ta samu halartar jami’an da ke kula da shirin daga ƙananan hukumomi 25 na Jihar Neja.

A yayin horon, an koyar da mahalarta dabarun dasa bishiyoyi da kula da su, hanyoyin daidaitawa da sauyin yanayi, da kuma dabarun tabbatar da ɗorewar muhalli a makarantu.

Tags: muhalliNeja
Previous Post

Tsaron Cikin Ƙasa: Gwamnatin Tarayya ta ƙudiri aniyar ƙarfafa haɗin gwiwa don zaman lafiya da cigaba – Idris

Next Post

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar tashoshin jiragen ruwa ta 2026

Related Posts

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027
Siyasa

Al’ummar Shinkafi sun yi alƙawarin goyon bayan Tinubu, Dauda Lawal da sauran ’yan takarar APC a 2027

November 28, 2026
Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura
Labarai

Zargin taɓa jikin Baturiya: Gwamnatin Katsina ta bayyana sunayen ‘yan kwamitin binciken Sarkin Daura

November 25, 2026
Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya
Siyasa

Tinubu ya umurci sojoji su ƙara ƙaimi kan ’yan ta’adda a Arewa-Maso-Gabas domin ɗorewar zaman lafiya

November 25, 2026
Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80
Siyasa

Tinubu ya taya Atiku murnar cika shekaru 80

November 25, 2026
Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu
Tsaro

Iƙirarin satar sauraron wayar NSA da na yi kalamin siyasa ne kawai, inji El-Rufai a kotu

November 25, 2026
Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa
Labarai

Gwamnatin Katsina ta dakatar da Sarkin Daura, ta kafa kwamitin binciken zargin cin zarafin Baturiya da ake masa

November 24, 2026
Next Post
Cika shekara uku a mulki: Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun fara haifar da ɗa mai ido

Tinubu ya rattaba hannu kan dokar tashoshin jiragen ruwa ta 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • November 2026
  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!