• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro gobe a Abuja

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
August 10, 2026
in Labarai
A A
0
Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro gobe a Abuja
Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana yi wa Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa, marhabin a Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, yau Litinin 

Daga hagu: Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana yi wa Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa, marhabin a Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, Abuja, yau Litinin 

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya (The Muslim World League), tare da haɗin gwiwar ƙungiyar Jama’atu Izalatil Bidiah Wa Iƙamatus Sunnah (JIBWIS), za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro a Abuja ranar Talata, da nufin inganta zaman lafiya, haɗin kan ƙasa da tsaro.

Za a gudanar da taron ne a Cibiyar Taro ta Ƙasa da Ƙasa ta Bola Ahmed Tinubu, inda za a haɗa shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna alaƙar da ke tsakanin zaman lafiya, tsaro da cigaban zamantakewa da tattalin arziki.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin ƙaddamar da wani sabon masallaci da aka gina a Abuja, wanda Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa, ya jagoranta.

Idris, wanda tun da farko ya tarbi Sheikh Al-Issa a Ɓangaren Shugaban Ƙasa na Babban Filin Jirgin Sama na Nnamdi Azikiwe, tare da raka shi zuwa wurin ƙaddamar da masallacin, ya bayyana ziyarar a matsayin wata shaida ta kyakkyawar alaƙar da ke tsakanin Nijeriya, Saudiyya da sauran ƙasashen duniya.

Ya ce taron yana zuwa ne a wani muhimmin lokaci da Nijeriya take ci gaba da ƙarfafa tsarin tsaron ƙasa, tare da aiwatar da sauye-sauye da zuba jari da nufin hanzarta cigaban zamantakewa da tattalin arziki.

Sakatare Janar na Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya kuma Shugaban Ƙungiyar Malaman Addinin Musulunci ta Duniya, Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa, tare da jami’an gwamnatin Nijeriya da na Izala cikin masallacin ƙungiyar da aka ƙaddamar yau a Abuja

Ministan ya sake jaddada aniyar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da zaman lafiya tsakanin al’ummomi, daidaituwar addinai da haɗin kan ƙasa, yana mai cewa zaman lafiya da tsaro su ne ginshiƙan wadata da zaman lafiyar Nijeriya da Afrika.

Idris ya ce: “Shugaban Ƙasa ya ƙudiri aniyar tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali ba a Nijeriya kaɗai ba, har ma a faɗin duniya. Wannan wata bayyananniyar shaida ce ta hanyar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu yake bi.”

Ya ce Nijeriya, kasancewar ta ƙasa mafi yawan al’umma a Afrika, tana da babban nauyi da ya rataya a wuyan ta na inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali a faɗin nahiyar, yana mai cewa Nijeriya mai zaman lafiya da tsaro za ta yi tasiri mai kyau a Yammacin Afrika da nahiyar baki ɗaya.

A cewar sa, taron zai samar da wata muhimmiyar kafa da shugabannin addinai da sauran masu ruwa da tsaki za su yi amfani da ita wajen musayar ra’ayoyi da samar da hanyoyin da za su taimaka wajen ƙarfafa zaman lafiya tsakanin al’ummomi, tsaro da fahimtar juna.

Idris ya yaba wa Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya, JIBWIS, Gwamnatin Saudiyya da sauran masu ruwa da tsaki bisa sauƙaƙa ziyarar Sheikh Al-Issa da kuma kafa masallacin.

Ya yi godiya ga Sheikh Al-Issa bisa ci gaba da jajircewar sa wajen inganta zaman lafiya, tattaunawa da fahimtar juna tsakanin al’ummomin mabiya addinai daban-daban.

Tun da farko, Sheikh Al-Issa ya yaba wa ƙoƙarin Shugaba Tinubu na inganta zaman lafiya tsakanin Musulmi da waɗanda ba Musulmi ba, yana mai cewa zaman lafiya da daidaito a Nijeriya za su bayar da gagarumar gudunmawa wajen tabbatar da kwanciyar hankali a Yammacin Afrika da sauran sassan duniya.

Sheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-Issa yana jagorantar sallah a masallacin da ya ƙaddamar yau a Abuja

Sakatare Janar ɗin ya ce ziyarar sa ta ta’allaƙa ne kan zaman lafiya da zaman lafiya tsakanin al’ummomi, yana mai bayyana ƙwarin gwiwar cewa taron zai samar da muhimmiyar kafa wajen ciyar da tattaunawa da fahimtar juna gaba a Nijeriya da duniya baki ɗaya.

Ana sa ran taron zai haɗa shugabannin addinai, masu tsara manufofi da sauran masu ruwa da tsaki a wuri guda.

Daga cikin waɗanda suka tarbi Sheikh Al-Issa a filin jirgin saman akwai Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmad Aliyu Sokoto; Ministan Lafiya da Jin Daɗin Jama’a, Farfesa Muhammad Ali Pate; Ministan Ƙwadago da Ayyukan Yi, Muhammad Maigari Dingyaɗi; Sanata Aliyu Magatakarda Wamakko, mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Sakkwato ta Arewa; Sanata Mohammed Ɗanjuma Goje, mai wakiltar Mazaɓar Sanatan Gombe ta Tsakiya; Sanata Ahmed Sani Yerima, da sauran manyan baƙi.

Masallacin The Muslim World League da aka ƙaddamar yau a Abuja
Tags: masallaciMohammed IdrisSheikh Mohammed Bin Abdulkarim Al-IssataroThe Muslim World League
Previous Post

Tsinkayar Cardoso Da Okonjo-Iweala: Damarmakin da suka kamata ƙasashen Afrika su runguma yayin da duniya ke fuskantar jijjigar tattalin arziki

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar talla

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar talla

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar talla

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!