• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar talla

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
August 11, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla domin ƙarfafa tsarin gudanar da harkar talla
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana rantsar da alƙalan sabuwar Kotun Laifukan Talla yau a Abuja 

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana rantsar da alƙalan sabuwar Kotun Laifukan Talla yau a Abuja 

Gwamnatin Tarayya ta ƙaddamar da sabuwar Kotun Laifukan Talla, a wani mataki na ƙarfafa tsari da sa ido kan harkar talla, inganta ƙwarewa da tabbatar da bin ƙa’ida a masana’antar talla da sadarwar kasuwanci a Nijeriya.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a ranar Talata a wurin ƙaddamar da kotun a Abuja, yana mai bayyana kafa kotun a matsayin wani muhimmin mataki wajen gina masana’antar talla mai ƙwarewa da ɗaukar nauyi.

Ya ce: “Mu gina masana’antar talla da za ta yi fice wajen ƙirƙire-ƙirƙire, ta samu amincewar jama’a kuma ta kiyaye ɗaukar nauyi.”

Ministan ya ce Dokar Majalisar Kula da Harkokin Talla ta Nijeriya (ARCON) mai lamba 23 ta shekarar 2022 ta faɗaɗa ikon hukumar na tsarawa da sa ido kan harkar talla, tare da tanadar da kafa kotun domin sauraron laifukan da suka shafi dokar da kuma ƙa’idoji da dokokin da suka shafi harkar talla.

Ya buƙaci sabuwar kotun, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Cecilia M. A. Olatoregun, da ta gudanar da ayyukant ta cikin gaskiya, ‘yanci da adalci.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabi a wirin ƙaddamar da Kotun Laifukan Talla yau a Abuja

A cewar sa, “Duk wata shari’a da aka gabatar a gaban ku, ku duba ta bisa hujjojin da ke cikin ta, ba tare da tsoro ko nuna son kai ba, ko ƙauna ko ƙiyayya. Dole kotun ta kasance, kuma a gan ta a matsayin hukuma mai adalci da rashin nuna son kai.”

Idris ya taya shugabar da sauran membobin kotun murna, tare da tabbatar masu da ci gaba da goyon bayan ma’aikatar ga ARCON da ƙoƙarin gina masana’antar talla da za ta iya yin gogayya a duniya.

Tun da farko, Darakta-Janar na ARCON, Dakta Olalekan Olumuyiwa Fadolapo, ya bayyana ƙaddamar da kotun a matsayin wani babban mataki wajen ƙarfafa tsari da bin ƙa’idoji a masana’antar talla.

“Kotun Laifukan Talla wata babbar dama ce ga masana’antar talla ta Nijeriya. Ita ce irin ta ta farko a duniya, domin Nijeriya ta ɗauki matakin hangen nesa, ba wai kawai wajen kafa dokoki kan harkar talla ba, har ma da samar da tsare-tsare da tsarin gudanarwa,” inji Fadolapo.

Shugabar Kotun Laifukan Talla, Mai Shari’a Cecilia M. A. Olatoregun, ta yi alƙawarin cewa sabuwar kotun za ta gudanar da ayyukan ta cikin gaskiya, adalci da ƙwarewa.

“Babban abin alfahari ne a kira mu domin yi wa ƙasar mu hidima, kuma mun ɗauki wannan nauyi da muhimmanci sosai. An buƙace mu da yin aiki cikin gaskiya, kuma wannan shi ne abin da za mu yi,” inji ta.

Membobin kotun sun haɗa da Musa Ahmed Attah, SAN; Merga Tyowanan Kachina, Esq.; Dakta Ken Onyeali Ikpe, FRPA; da Hajiya Sa’a Ibrahim, RPA.

Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai Babbar Sakatare ta Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Binyerem Ukaire; Darakta mai kula da Sadarwar Jama’a da Wayar da Kai na Ƙasa, Henshaw Ogubike; Daraktan Hulɗa da Jama’a da Ƙa’idojin Gudanarwa, Dakta Suleiman Haruna; da Mataimaki na Musamman kan Harkokin Gudanarwa ga Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Dakta Sunday Baba, da sauran manyan baƙi.

Tags: Kotun Laifukan TallaMohammed Idris
Previous Post

Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi ta Duniya za ta gudanar da taron ƙasa da ƙasa kan tsaro gobe a Abuja

Next Post

Nijeriya tana buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Idris

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Nijeriya tana buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Idris

Nijeriya tana buƙatar haɗin kai yanzu fiye da kowane lokaci – Idris

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!