• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Taron Bauchi: CBN ya buƙaci cibiyoyin hadahadar kuɗi su bunƙasa hanyoyin biyan kuɗi na zamani domin haɓaka tattalin arziki

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
August 7, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Dalla-Dalla: Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara ta intanet, masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗaɗen ajiyar kwastomomin bankuna
Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan CBN

Mista Olayemi Cardoso, Gwamnan CBN

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya buƙaci masu ruwa da tsaki da suka ƙunshi kamfanoni da cibiyoyin ɓangaren kuɗi da bankuna su ƙara bunƙasa hanyoyin biyan kuɗi na zamani domin inganta ci gaban tattalin arzikin ƙasa.

Bankin ya bayyana cewa ya shirya taron masu ruwa da tsaki ne domin wayar da kan jama’a game da manufofi da shirye-shiryen sa, da nufin bunƙasa ci gaba mai ɗorewa a tattalin arziki da kuma inganta rayuwa da hanyoyin samun abin yi ga ‘yan Nijeriya.

Da take jawabi a Bauchi ranar Alhamis, Daraktar Sashen Hulɗa da Jama’a da Harkokin Masu Zuba Jari na CBN, Hajiya Hakama Sidi Ali, ta ce matakan da CBN ke ɗauka wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki suna ci gaba da haifar da sakamako mai kyau. Ta ce hakan na bayyana ne ta hanyar raguwar hauhawar farashin kayayyaki, ƙaruwa a ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje, da kuma daidaituwar kasuwar canjin kuɗaɗen waje.

Hakama ta yi nuni da sabon rahoton Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS), wanda ya nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki gaba ɗaya ya sauka kaɗan daga kashi 15.93 cikin ɗari a watan Mayu na 2026 zuwa kashi 15.91 cikin ɗari a watan Yuni na 2026.

Ta ce, “Haka kuma, hauhawar farashin kayayyaki na asali da na abinci sun ragu a wannan lokaci, sakamakon tsauraran matakan manufofin kuɗi, haɗa tsarin musayar kuɗaɗen waje zuwa tsari guda, da kuma inganta gaskiya a kasuwa.

“Darajar Naira na ci gaba da ƙarfi, inda giɓin da ke tsakanin farashin musayar kuɗi a kasuwar hukuma da ta masu canjin kuɗi ya ragu zuwa ƙasa da kashi biyu cikin ɗari. Har ila yau, ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje na Nijeriya ya haura dala biliyan 52.5 na Amurka zuwa ranar 17 ga Yulin 2026, wanda shi ne adadi mafi yawa cikin shekaru 17, kuma ya zarce abin da CBN ya sa a gaba na shekara a wannan shekara.”

Ta ce, “wannan ya samo asali ne daga ci gaba da shigowar kuɗaɗe da kuma ƙarin amincewar masu zuba jari da shiga kasuwannin kadarori daban-daban a Nijeriya.”

Shi ma Mai Kula da Reshen CBN na Bauchi, Michael Dalyop, ya ce tattalin arzikin Nijeriya ya samu gagarumin ci gaba a muhimman fannoni cikin ‘yan shekarun nan.

Ya bayyana cewa sauye-sauyen da aka aiwatar a kasuwar musayar kuɗaɗen waje sun haɗa farashin canji zuwa tsari guda, sun ƙara wanzar da gaskiya, tare da ƙarfafa amincewa a kasuwa, abin da ya taimaka wajen samun daidaito a farashin musayar kuɗi.

Ya ƙara da cewa ajiyar kuɗaɗen ƙasashen waje ta haura dala biliyan 50, yayin da jarin da masu zuba jari daga ƙasashen waje ke shigowa da shi ke ci gaba da ƙaruwa.

A cewar sa, hauhawar farashin kayayyaki na ci gaba da raguwa yayin da CBN ke aiki tuƙuru domin cimma manufar rage hauhawar tsadar zuwa ƙasa da kashi goma cikin ɗari.

Ya ce, “bayan nasarar kammala shirin ƙarfafa jarin bankuna da aiwatar da wasu manufofi, bankuna da sauran cibiyoyin kuɗi sun ƙara ƙarfi wajen tallafa wa masu gudanar da harkokin kasuwanci da samar da kayayyaki domin bunƙasa sana’o’in su da bayar da gudunmawa ga ci gaban tattalin arzikin ƙasa.”

Dalyop ya bayyana cewa taron ya haɗa manyan masu ruwa da tsaki a tattalin arzikin Nijeriya, ciki har da masu amfani da ayyukan kuɗi, masu samar da ayyukan kuɗi, hukumomin sa-ido, jami’an gwamnati, hukumomin tsaro da sauran masu ruwa da tsaki.

Ya ce manufar taron ita ce wayar da kan jama’a game da hanyoyin biyan kuɗi na zamani da kuma damar da ake da su a cikin tsarin hada-hadar kuɗi a Nijeriya.

A wurin taron, Hukumar Kare Kuɗaɗen Masu Ajiya ta Nijeriya (NDIC) ta shawarci ‘yan Nijeriya da su daina ajiye kuɗaɗe masu yawa a gidajen su ko a wuraren da ba bankuna ba.

Hukumar ta bayyana cewa kamfanonin fasahar kuɗi (fintech) da ƙananan bankunan kuɗi (microfinance banks) da aka ba lasisi suna da kariyar inshorar ajiya, kuma CBN ne ya ba su lasisin gudanar da ayyukan su.

Previous Post

Rahoton CBN: Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙara bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a 2025

Next Post

Gwamnan Neja ya saki Naira biliyan 1.5 don biyan garatutin masu ritaya

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Gwamnan Neja ya saki Naira biliyan 1.5 don biyan garatutin masu ritaya

Gwamnan Neja ya saki Naira biliyan 1.5 don biyan garatutin masu ritaya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!