• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rahoton CBN: Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙara bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a 2025

Ashafa Murnai Barkiya by Ashafa Murnai Barkiya
August 6, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Rahoton CBN: Tattalin arzikin Nijeriya ya ƙara bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a 2025
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana cewa tattalin arzikin cikin gida na ƙasar, wato GDP ya ƙara bunƙasa da kashi 3.87 cikin ɗari a shekarar 2025.

Wannan ƙari da aka samu kuwa ya fi na kashi 3.38 cikin ɗari da aka samu a shekarar 2024.

CBN ya bayyana hakan ne a cikin rahoton sa na shekara ta 2025 da aka fitar kwanan nan.

A rahoton na CBN, wannan bunƙasa mai faɗi ta samo asali ne daga ci gaba da aiwatar da jerin sauye-sauyen tattalin arziki a muhimman fannoni, tare da sake fasalin yadda ake ƙididdige tattalin arzikin ƙasa domin haɗa sabbin ƙananan sassa da suka fara taka muhimmiyar rawa.

Bankin ya ce hauhawar farashin kayayyaki ya ragu zuwa kashi 15.15 cikin ɗari a watan Disamba na 2025, wato daga kashi 34.80 cikin ɗari da aka samu a ƙarshen shekarar 2024.

Ya bayyana cewa hakan ya samu ne sakamakon haɗakar tsauraran matakan manufofin kuɗi, daidaituwar canjin kuɗaɗen waje, da kuma sake fasalin hanyar da ake amfani da ita wajen ƙididdige Ma’aunin Farashin Kayan Masarufi, watau ‘Consumer Price Index’, wanda aka fi sani da CPI.

“Sabuwar hanyar ƙididdigar ta sabunta nauyin abubuwan da ake la’akari da su a cikin kwandon CPI, domin ya fi nuna yadda gidaje ke kashe kuɗin su a halin yanzu.

“Haka kuma, yanayin kuɗaɗen gwamnati ya nuna alamun ingantuwa a shekarar 2025, inda kuɗaɗen shiga na Asusun Tarayya suka ƙaru da kashi 33.67 cikin ɗari, sakamakon ƙarin kuɗaɗen shiga daga fannin mai da kuma sauran fannoni waɗanda ba na mai ba.

Wannan rahoto ya ci gaba da bayyana cewa, “saboda haka, rabon kuɗaɗen da ake bai wa matakan gwamnati uku ya ƙaru, lamarin da ya ƙarfafa ɗorewar tsarin kuɗaɗen gwamnati.”

CBN ya kuma ce yawan harajin da gwamnati ke tarawa idan aka kwatanta da girman tattalin arzikin ƙasa (GDP) ya ƙaru zuwa kashi 7.15 cikin ɗari a shekarar 2025, daga kashi 5.41 cikin ɗari a shekarar 2024.

Ya ce wannan ƙarin ya samo asali ne daga ƙaruwar kuɗaɗen harajin ribar man fetur, harajin ƙimar kaya (VAT), da kuma harajin kuɗaɗen shigar kamfanoni.

“Zuwa ƙarshen watan Satumba na 2025, jimillar bashin gwamnati ta kai Naira tiriliyan 153.29, wanda ya kai kashi 35.55 cikin ɗari na GDP. Duk da haka, wannan adadi yana ƙasa da iyakar kashi 60 cikin ɗari da ƙasa ta gindaya, da kuma iyakar kashi 70 cikin ɗari da ake ba da shawara ga ƙasashen da ke samun damar karɓar bashi daga kasuwannin duniya (Market-Access Countries),” inji rahoton.

CBN ya ce tattalin arzikin duniya ya ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali a shekarar 2025, duk da ƙalubalen rashin tabbas da suka ƙaru.

“Ko da yake bunƙasar tattalin arzikin duniya ya ci gaba da kasancewa a kashi 3.30 cikin ɗari, ci gaban bai kasance iri ɗaya ba a dukkan yankuna.

“A ƙasashen da suka ci gaba, bunƙasar tattalin arziki ta ragu zuwa kashi 1.70 cikin ɗari daga kashi 1.80 cikin ɗari, sakamakon raguwar buƙatu.

“Amma a ƙasashe masu tasowa da kuma kasuwanni masu bunƙasa (EMDEs), bunƙasar tattalin arziki ta ƙaru zuwa kashi 4.40 cikin ɗari, idan aka kwatanta da kashi 4.30 cikin ɗari a shekarar 2024, sakamakon ci gaba da aiwatar da manufofin tallafa wa tattalin arziki,” inji rahoton na CBN.

Haka kuma CBN ya ce hauhawar farashin kayayyaki a duniya ta ragu zuwa kashi 4.20 cikin ɗari, sakamakon saukar farashin makamashi da kayan abinci, da kuma tasirin tsauraran manufofin kuɗi da aka aiwatar tun da farko.

“A ƙasashen da suka ci gaba, hauhawar farashin kayayyaki ta ɗan ragu zuwa kashi 2.50 cikin ɗari, daga kashi 2.60 cikin ɗari a shekarar 2024.

“Amma a ƙasashe masu tasowa da kasuwanni masu bunƙasa, raguwar ta fi sauri, inda hauhawar farashin kayayyaki ta sauka zuwa kashi 5.20 cikin ɗari, daga kashi 7.90 cikin ɗari.

“Ƙasashe da dama sun rage yawan kuɗin ruwa a shekarar 2025, bayan hauhawar farashin kayayyaki ta lafa, tare da ƙoƙarin cimma manufofin su na tattalin arziki,” inji CBN.

Har ila yau, CBN ya ce yanayin manufofin kuɗaɗen gwamnati a duniya ya ci gaba da fuskantar ƙalubale, saboda yawan bashin da ƙasashe ke ɗauke da shi da kuma ƙarin kashe kuɗaɗe a fannin tsaro.

A cewar CBN, yanayin kasuwannin kuɗi na duniya a lokacin da rahoton ya shafa ya samu tasiri daga sauye-sauyen siyasa da rikice-rikicen ƙasa da ƙasa, da kuma abubuwan da suka faru a manyan tattalin arzikin duniya.

Bankin ya ce kasuwannin hannayen jari sun kasance cikin yanayi mai kyau, abin da ke nuna ƙarfi a ribar kamfanoni da kuma sauyin hasashen manufofin tattalin arziki.

“Haka kuma, farashin kayayyaki a kasuwannin duniya ya ragu gaba ɗaya, inda matsakaicin farashin gangar ɗanyen man Bonny Light ya sauka zuwa dala 70.93 kan kowace ganga, daga dala 82.56 a shekarar 2024, sakamakon yawaitar ɗanyen mai a kasuwar duniya.”

Tags: rahoto
Previous Post

Tinubu ya yaba wa hukumar NELFUND kan ƙoƙarin faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ga matasa

Next Post

Taron Bauchi: CBN ya buƙaci cibiyoyin hadahadar kuɗi su bunƙasa hanyoyin biyan kuɗi na zamani domin haɓaka tattalin arziki

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Dalla-Dalla: Yadda CBN ya bankaɗo ‘yan damfara ta intanet, masu ƙoƙarin kutsen satar kuɗaɗen ajiyar kwastomomin bankuna

Taron Bauchi: CBN ya buƙaci cibiyoyin hadahadar kuɗi su bunƙasa hanyoyin biyan kuɗi na zamani domin haɓaka tattalin arziki

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!