Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi alƙawarin ci gaba da tallafa wa Gasar Polo ta Ƙasa ta Minna da ake aiwatarwa a kowace shekara.
Gwamnan ya faɗi haka ne a wajen babban wasan ƙarshe na bana na gasar wanda aka gudanar a Filin Polo na Minna a yau Lahadi inda ƙungiyar Profile Polo Team ta lashe babban Kofin IBB bayan ta doke ƙungiyar Malcomines Polo Team.
A wani ɓangare na gasar, ƙungiyar Bago Farms Polo Team, wadda Marwan Mohammed Bago, ɗan gwamnan, yake jagoranta a matsayin kyaftin, ta lashe Kofin Sarkin Minna da kuma Kofin Gwamna. Haka kuma, Profile Polo Club ta zama zakara a Kofin Janar Hassan.

Da yake jawabi bayan kammala gasar, Gwamna Bago, wanda ya kalli wasan ƙarshen, ya nuna farin ciki da gamsuwa kan ingancin gasar da kuma bajintar da ‘yan wasa suka nuna.
Ya taya dukkan ƙungiyoyin da suka shiga gasar murna, tare da yaba wa ‘yan wasan bisa kyakkyawan yanayin wasa da nuna ruhin wasanni a duk tsawon gasar.
Gwamnan, wanda kuma shi ne Shugaban Minna Polo Club, ya yaba wa Mataimakin Shugaban Ƙungiyar na Farko, Mohammed Babangida, saboda jagorancin sa da ƙoƙarin da yake yi wajen tabbatar da ci gaba da bunƙasar wasan polo a Jihar Neja.
Ya sake jaddada aniyar sa ta ci gaba da tallafa wa wasan polo, yana mai tabbatar da cewa gwamnatin sa za ta ci gaba da bayar da duk wani goyon bayan da ya dace domin bunƙasa wasan.
An kammala taron da rabon kofuna da allunan girmamawa ga ƙungiyoyin da suka yi nasara, tare da karrama fitattun ‘yan wasan da suka nuna ƙwazo a lokacin gasar.

Daga cikin manyan baƙi da suka halarci bikin akwai Sarkin Minna, Alhaji Umar Faruk Bahago, da Wakilin Birnin Adamawa, Dakta Umar Usman Bazza, tare da sauran masoya da masu ruwa da tsaki a harkar wasan polo.







