Ƙorafe-ƙorafen da kwastomomin bankuna suka shigar kan cibiyoyin kuɗi sun kai 23,129 a shekarar 2025, wanda ya nuna ƙarin kashi 11 cikin ɗari idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata. Hakan ya sa Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ba da umurnin a mayar wa kwastomomin da abin ya shafa naira biliyan 19.12 da kuma dala miliyan 329.3 duk a cikin 2025.
Ba a nan kaɗai CBN ya tsaya ba, ya kuma ci tarar cibiyoyin kuɗi naira biliyan 1.69 saboda karya ƙa’idoji, rashin kula da ƙorafe-ƙorafen kwastomomi yadda ya kamata, da kuma gaza bin umarnin bankin. Hakan na ƙunshe ne cikin Rahoton Shekara-shekara na CBN na 2025.
CBN ya bayyana cewa ƙaruwar ƙorafe-ƙorafen ba su nuna taɓarɓarewar ayyukan bankuna ba ne, sai dai sun samo asali ne daga yadda jama’a suka ƙara sanin tsarin kare haƙƙin masu amfani da harkokin kuɗi tare da ƙara amincewa da tsarin warware ƙorafe-ƙorafen da bankin ya tanada.
Rahoton ya ce: “CBN ya karɓi jimillar ƙorafe-ƙorafe 23,129 daga masu amfani da harkokin kuɗi a shekarar 2025, wanda ya nuna ƙarin kashi 10.53 cikin ɗari idan aka kwatanta da adadin 20,925 da aka samu a shekarar 2024.
Wannan ya nuna cewa jama’a sun fi wayewa tare da ƙara amincewa da tsarin warware ƙorafe-ƙorafen masu amfani da harkokin kuɗi na bankin.”
Rahoton ya ƙara da cewa, “an warware jimillar ƙorafe-ƙorafe 18,824, wanda ya nuna ƙarin kashi 9.36 cikin ɗari idan aka kwatanta da adadin 17,213 da aka warware a shekarar 2024.”
Dangane da kuɗaɗen da ake taƙaddama a kan su, CBN ya ce:
“Jimillar kuɗaɗen da ake nema a cikin kuɗin Nijeriya ya ƙaru zuwa naira biliyan 40.61, daga naira biliyan 17.13 a shekarar 2024. Haka kuma, adadin da ake nema a kuɗin ƙasashen waje ya ƙaru zuwa dala miliyan 344.2, idan aka kwatanta da dala miliyan 1.06 a shekarar da ta gabata.
“Bayan warware ƙorafe-ƙorafen, an mayar wa kwastomomi naira biliyan 19.12 da kuma dala miliyan 329.3 a shekarar 2025, idan aka kwatanta da naira biliyan 9.66 da kuma dala miliyan 0.67 da aka mayar a shekarar 2024.”
CBN ya ce ya ƙara tsaurara matakan hukunta cibiyoyin kuɗin da suka karya ƙa’idoji a cikin shekarar ya kuma bayyana cewa, “a lokacin CBN ya sanya tara guda 11 kan cibiyoyin kuɗi, waɗanda jimillar su ta kai naira biliyan 1.26, saboda laifuffuka da suka haɗa da karya ƙa’idoji da kuma gaza amsa tambayoyin da hukuma ta aike musu.”







