Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada cewa gwamnatin sa tana ci gaba da aiwatar da manyan sauye-sauye da nufin tabbatar da tsaro, inganta ilimi, bunƙasa tattalin arziki da samar da ingantattun ababen more rayuwa domin gina Nijeriya mai ɗorewa.
Shugaban ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin taron tunawa da cika shekara uku da rasuwar marigayi Janar Hassan Usman Katsina, wanda aka gudanar a Arewa House da ke Kaduna.
Tinubu, wanda Mataimakin sa na Musamman kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Masari, ya wakilta, ya ce gwamnatin Renewed Hope Agenda ta himmatu wajen ci gaba da gina kan tubalan da magabatan ƙasa suka shimfiɗa, tare da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.
Cigaba a Fannin Tsaro
Shugaban ya bayyana kwarin gwiwarsa cewa matsalar rashin tsaro, musamman a Arewacin Nijeriya, na dab da zama tarihi.
“Muna aiki dare da rana domin tabbatar da tsaron ƙasarmu, kuma da yardar Allah ba da jimawa ba za mu shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi Arewacin Nijeriya,” inji shi.
Sama da Ɗalibai Miliyan Ɗaya Sun Amfana da NELFUND
A ɓangaren ilimi, Tinubu ya ce sama da ɗalibai miliyan ɗaya sun riga sun ci gajiyar shirin NELFUND, wanda ya sauƙaƙa wa matasa samun ilimi ba tare da matsin lambar kuɗi ba.
Ya kuma ce gwamnati ta dawo da zaman lafiya a jami’o’i ta hanyar cire su daga tsarin IPPIS, tare da dawo musu da cikakken ikon amfani da kuɗaɗen shiga na cikin gida.
Haka kuma, ya bayyana cewa ta hannun TETFund, gwamnati na gina sababbin ajujuwa, ɗakunan kwanan ɗalibai, cibiyoyin bincike da kimiyya, tare da amincewa da sabon tsarin karatu da kuma faɗaɗa ilimin fasaha da sana’o’i.
Manyan Ayyukan Tituna na Cigaba
Tinubu ya ce ana ci gaba da aikin sake gina titin Abuja–Kaduna–Zariya–Kano, da kuma gagarumin aikin Babban Titin Sakkwato zuwa Badagiri.
Ya ƙara da cewa ana kuma gudanar da ayyukan titunan Sokoto–Zamfara–Kaduna da Akwanga–Jos–Bauchi–Gombe, domin sauƙaƙa zirga-zirga da bunƙasa tattalin arziki.
Inganta Ɓangaren Wutar Lantarki
Shugaban ya ce Gwamnatin Tarayya na aiwatar da manyan ayyukan samar da wutar lantarki a arewacin Nijeriya, waɗanda suka haɗa da:
- Tashar Wutar Kaduna.
Aikin Kumbotso 40MW High Voltage Power Project. - Samar da Solar Mini-Grids a yankunan karkara.
- Farfaɗo da Kaduna Power Plant mai ƙarfin megawatt 215 (215MW)
Ya kuma bayyana cewa College of Petroleum and Energy Studies da ke Kaduna an mayar da ita jami’a mai suna Gen. Hassan Usman Katsina University, inda aikin ya kai sama da kashi 90 cikin 100, kuma an riga an fara karatu.
Bugu da ƙari, ya ce aikin tashar samar da lantarki ta Gwagwalada mai ƙarfin megawatt 1,350 (1,350MW) na ci gaba, tare da aiwatar da wasu ayyukan makamashi a Kaduna da jihohin da ke maƙwabtaka da ita.
Cigaba da Ayyukan Layukan Dogo da Metro Rail
Tinubu ya ce aikin layin dogo na Kaduna–Kano da kuma Kano–Maradi suna tafiya yadda aka tsara.
Ya bayyana cewa gwamnati ta tanadi kuɗaɗe domin aiwatar da ayyukan Kaduna Light Rail da Kano Light Rail, yayin da ake ci gaba da gyaran Abuja Metro Rail.
Haka kuma, ya ce gwamnatin ta amince da inganta zirga-zirgar jirgin ƙasan Abuja–Kaduna, domin sauƙaƙa safarar fasinjoji da kayayyaki.
Gwamnati Na Gina Tattalin Arziki Mai Ƙarfi
Shugaban ya ce gwamnatin sa ta samu cigaba mai ma’ana a fannoni daban-daban da suka haɗa da noma, tabbatar da wadatar abinci, ƙarfafa matasa da aiwatar da shirye-shiryen jinƙai.
A cewar sa, duk waɗannan sauye-sauyen na da nufin samar da damarmaki ga al’umma, ƙara yawan ayyukan yi da kuma tabbatar da cigaba mai ɗorewa ga dukkan ‘yan Nijeriya.
Tinubu ya yi kira ga al’ummar ƙasar nan da su ci gaba da haɗa kai tare da bai wa gwamnati cikakken goyon baya domin gina Nijeriya mai zaman lafiya, cigaba, da wadata.







