• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai Siyasa

Bago ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa ta bai wa mata damar shiga harkokin mulki a Neja

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 26, 2026
in Siyasa
A A
0
Bago ya sake jaddada aniyar gwamnatin sa ta bai wa mata damar shiga harkokin mulki a Neja
Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja tare da 'ya'yan Ƙungiyar Mata Masu Ruwa da Tsaki ta Shiyyar C (Zone C) lokacin da suka kai masa ziyarar girmamawa a Fadar Gwamnati da ke Minna

Gwamna Mohammed Umaru Bago na Jihar Neja tare da 'ya'yan Ƙungiyar Mata Masu Ruwa da Tsaki ta Shiyyar C (Zone C) lokacin da suka kai masa ziyarar girmamawa a Fadar Gwamnati da ke Minna

Gwamnan Jihar Neja, Alhaji Mohammed Umaru Bago, ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ci gaba da bai wa mata damar shiga harkokin mulki tare da kasancewa cikin masu yanke muhimman shawarwari a jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne lokacin da ya karɓi baƙuncin Ƙungiyar Mata Masu Ruwa da Tsaki ta Shiyyar C (Zone C) a ziyarar girmamawa da suka kai masa a Fadar Gwamnati da ke Minna.

A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labaran sa, Ibrahim Bologi, ya fitar ranar Juma’a, gwamnan ya yaba wa mata kan irin muhimmiyar gudunmawar da suke bayarwa wajen cigaban siyasa, yana mai cewa su ne ginshiƙin nasarar sa a fagen siyasa.

Ya ce sama da mata miliyan ɗaya da suka yi rajista a jam’iyyar APC daga Shiyyar C babban ƙarfi ne da ba za a yi wasa da shi ba.

Gwamna Bago Neja tare da shugabannin Ƙungiyar Mata Masu Ruwa da Tsaki ta Shiyyar C (Zone C) a lokacin ziyarar

Gwamnan ya kuma yaba wa matan yankin bisa yadda suka ci gaba da nuna jajircewa da biyayya ga APC duk da ƙalubalen tsaro da yankin arewacin jihar yake fuskanta, yana mai cewa hakan abin yabawa ne kuma ya cancanci girmamawa.

Ya buƙace su da su ci gaba da fitowa da yawa wajen mara wa manufofin Ajandar Sabuwar Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma Ajandar Sabuwar Neja (New Niger Agenda) baya.

Bago ya bayyana ƙungiyar a matsayin abin koyi, yana mai cewa ta kafa tarihi tare da zaburar da sauran shiyyoyin jihar da su haɗa kan mata domin ƙarfafa jam’iyyar APC da kuma tallafa wa shirye-shiryen gwamnatin jihar.

Ya ce ya gamsu da yadda ƙungiyar ta tsara kan ta cikin tsari mai kyau, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi la’akari da wasu daga cikin membobin ta wajen cike guraben muƙaman gwamnati idan lokaci ya yi.

Haka kuma, gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnatin sa tana ci gaba da ɗaukar matakai masu ƙarfi domin magance matsalolin tsaro a Ƙaramar Hukumar Borgu da sauran sassan jihar, domin tabbatar da zaman lafiya da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar Neja.

A nata jawabin, jagorar tawagar ƙungiyar, Hajiya Hauwa Baƙo Kontagora, ta yaba wa Bago kan irin goyon bayan da yake bai wa mata a faɗin jihar.

Ta bayyana cewa ƙungiyar ta haɗa tsofaffin masu riƙe da muƙaman gwamnati da masu ci a yanzu, ciki har da kwamishinoni, masu ba da shawara na musamman, darakta-janar-janar, daraktocin zartarwa, mataimakan shugabannin ƙananan hukumomi, shugabannin mata na ƙananan hukumomi, da sauran masu ruwa da tsaki.

A cewar ta, an kafa ƙungiyar ne domin haɗa kan mata, ƙarfafa muryar su ta hanyar faɗaɗa shigar su cikin harkokin mulki, tare da ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnatin jihar wajen bunƙasa shirye-shiryen ƙarfafa mata, inganta tattalin arzikin su da sauran ayyukan cigaba.

Wani sashe na matan ƙungiyar a lokacin ziyarar

Hajiya Hauwa ta ce ƙungiyar tana neman a ƙara bai wa mata damar riƙe muƙaman jagoranci, shiga yanke muhimman shawarwari da kuma taka rawa wajen aiwatar da shirye-shiryen cigaban jihar.

Ta tabbatar wa da gwamnan cewa membobin ƙungiyar za su ci gaba da haɗa kai da gwamnatin sa domin tabbatar da cigaba, zaman lafiya da gina Jihar Neja mai ƙarfi da wadata.

Tags: Gwamna Mohammed Umaru BagoHauwa Baƙo KontagoramataNejaziyaraZone C
Previous Post

Next Post

Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 

Related Posts

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko
Siyasa

Gwamnatin Tarayya ta kare rashin halartar Tinubu a UNGA, ta ce Shettima na da cikakken iko

September 21, 2026
Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu
Siyasa

Ministan Yaɗa Labarai ya buƙaci shugabannin APC na Neja da su goyi bayan sauye-sauyen Tinubu

September 10, 2026
Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027
Siyasa

Ƙungiyar Kiristoci ta goyi bayan Tinubu a zaɓen 2027

September 9, 2026
Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2
Siyasa

Fadar Shugaban Ƙasa ta zargi Atiku da ɗaukar ‘yan barandar siyasa na Amurka aikin farfaganda kan dala miliyan 1.2

September 2, 2026
Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20
Siyasa

Zaɓen 2027: Matawalle ya ce zai sama wa Tinubu ƙuri’u miliyan 20

August 26, 2026
Siyasa

Tinubu ya janye jerin sunayen Majalisar Yaƙin Neman Zaɓen APC – Rahoto

August 25, 2026
Next Post
Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 

Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa - Tinubu 

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!