• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Monday, September 28, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
July 27, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, da Darakta Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, da Darakta Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, da Darakta Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala

Gwamnan CBN, Cardoso da Okonjo-Iweala Za Su Jagoranci Tattaunawar Ƙarfafa Juriyar Tattalin Arzikin Afrika a Abuja

Daga Ashafa Murnai Barkiya

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, da Darakta Janar ta Hukumar Kasuwanci ta Duniya (WTO), Dakta Ngozi Okonjo-Iweala, za su jagoranci muhimmin zama na musamman a Taron Africa Emerging Markets Forum (AEMF) karo na bakwai, wanda za a gudanar a Abuja a ranakun 29 da 30 ga Yuli, 2026.

A cewar wata sanarwa da CBN ya fitar ranar Lahadi, taron na kwanaki biyu zai gudana ne a hedikwatar bankin da ke Abuja, tare da haɗin gwiwar Emerging Markets Forum (EMF) da kuma Cibiyar Nazarin Tattalin Arzikin Afrika (CSEA).

An tsara taron ne domin haɗa masu tsara manufofi, gwamnonin manyan bankunan ƙasashe, ministoci, manyan jami’an gwamnati, shugabannin kamfanoni masu zaman kan su, masana tattalin arziki da abokan hulɗar ci gaba daga Afrika da sauran sassan duniya domin tattauna hanyoyin da nahiyar za ta ƙarfafa juriyar tattalin arzikin ta a yayin da duniya ke cigaba da fuskantar rashin tabbas.

Za a gudanar da taron ne ƙarƙashin taken “Gina Tattalin Arziki Mai Juriyar Fuskantar Ƙalubale da Sauye-sauyen Tattalin Arzikin Duniya.”

Sanarwar ta bayyana cewa tattaunawar da Cardoso da Okonjo-Iweala za su jagoranta za ta mayar da hankali kan yadda ƙasashen Afrika za su ƙarfafa juriyar tattalin arzikin su, ci gaba da aiwatar da sauye-sauyen tattalin arziki, zurfafa haɗin gwiwar kasuwanci tsakanin ƙasashen nahiyar da kuma samar da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa duk da ƙalubalen da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.

CBN ya ce zaman tarurrukan zai kuma duba manufofin da za su taimaka wa ƙasashe masu tasowa su jure wa girgizar tattalin arziki daga waje, tabbatar da daidaiton tattalin arziki da kuma ci gaba da sauye-sauyen da za su haɓaka cigaba.

Daga cikin waɗanda ake sa ran za su gabatar da muhimman jawabai akwai Ministan Kuɗi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Taiwo Oyedele, da Ministan Kimiyya, Fasaha da Ƙirkire-ƙirkire, Dakta Kingsley Udeh.

Masu shirya taron sun bayyana cewa halartar ministocin na nuna muhimmancin daidaita manufofin kuɗi, kasafin kuɗi da kuma manufofin kimiyya da ƙirkire-ƙirkire domin tabbatar da bunƙasar tattalin arzikin Afrika na dogon lokaci.

Sauran fitattun mahalarta taron sun haɗa da Babban Masanin Tattalin Arziki kuma Babban Mataimakin Shugaban Bankin Duniya mai kula da Tattalin Arziki da Ci Gaba, Indermit Gill; wanda ya kafa kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Emerging Markets Forum, Harinder Kohli; da Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Adamu Ahmed.

Haka kuma, ana sa ran manyan jami’an gwamnati, masana, shugabannin kasuwanci da abokan hulɗar ci gaba daga sassa daban-daban na duniya za su halarci taron.

A cewar CBN, mahalarta za su tattauna batutuwa da suka haɗa da daidaiton tattalin arziki, haɗin gwiwar tattalin arziki tsakanin ƙasashen Afrika, tsarin biyan kuɗi tsakanin ƙasashe, fasahar kuɗi (FinTech), bunƙasa ababen more rayuwa, zuba jarin kai-tsaye daga ƙasashen waje (FDI), musayar fasaha, basirar wucin-gadi (AI), hauhawar farashin abinci, hauhawar farashi gaba ɗaya da kuma tasirin manufofin kuɗi musamman ga ƙasashe masu rauni ko masu farfaɗowa daga rikice-rikice.

Masu shirya taron sun ce manufar taron ita ce ƙarfafa tattaunawa tsakanin gwamnatoci, cibiyoyin kuɗi da abokan hulɗar ci gaba, tare da samar da shawarwari masu amfani da suka dace da buƙatun ƙasashe masu tasowa.

Sanarwar ta ce taron na da nufin ƙarfafa buɗaɗɗiyar tattaunawa kan manyan batutuwan da suka shafi ƙasashe masu tasowa, tare da samar da hanyoyin warware matsalolin tattalin arziki da za a iya daidaita su gwargwadon yanayin kowace ƙasa.

CBN ya ƙara da cewa taron wani ɓangare ne na ƙoƙarin bankin da abokan hulɗar sa na ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen yankin, inganta tsara manufofi bisa hujjoji da bayanai, da kuma haɓaka sababbin dabarun da za su ƙarfafa juriyar tattalin arzikin Afrika tare da tabbatar da bunƙasa mai ɗorewa.

Previous Post

Muna samun nasarori a tsaro, ilimi da ababen more rayuwa – Tinubu 

Next Post

Ba mu da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki – Minista

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Ba mu da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki – Minista

Ba mu da shirin ƙara kuɗin wutar lantarki - Minista

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!