Sojoji Sun Hallaka ‘Yan Ta’adda da Dama, Sun Ceto Mutanen da Aka Sace a Sabbin Hare-hare a Faɗin Ƙasa
Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya sun samu gagarumar nasara a wasu sabbin hare-hare da suka kai ta sama da ƙasa a jihohin Borno, Yobe, Zamfara, Kogi, Nasarawa da kuma wasu sassan Kudu maso Gabas, inda suka hallaka ‘yan ta’adda da dama, suka ceto mutanen da aka yi garkuwa da su, tare da kama waɗanda ake zargi da hannu a ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.
Hare-haren, waɗanda aka gudanar ƙarƙashin Operation HADIN KAI, Operation FANSAN YAMMA, Operation WHIRL STROKE da Operation UDO KA, sun kuma haifar da ƙwato makamai, alburusai da kayayyakin sadarwa da ake zargin ana amfani da su wajen gudanar da ayyukan ta’addanci.
A Borno, dakarun Bataliya ta 212 sun kama wani da ake zargin mamba ne na ƙungiyar ISWAP a kan hanyar Maiduguri zuwa Monguno. An kama shi da na’urar Starlink, na’urar Wi-Fi mai tashoshi shida, wayar salula da kuma kuɗi.
Haka kuma, dakarun Bataliya ta 82 sun kuɓutar da wasu ‘yan mata biyu a ƙaramar hukumar Gwoza. ‘Yan matan sun bayyana cewa an yi garkuwa da su tun watan Agustan 2025 a kan hanyar Pulka zuwa Ngoshe, kafin daga bisani su tsere daga sansanin ‘yan ta’adda da ke Dutsen Mandara.
A Yobe kuwa, dakarun Brigade ta 27 sun fatattaki ‘yan ta’adda da suka kai hari wani wurin binciken sojoji da ke kan hanyar Buni Yadi zuwa Buni Gari a ƙaramar hukumar Gujba. Sai dai, sojoji biyu sun rasa rayukansu yayin musayar wuta, yayin da aka lalata motar yaƙin da ‘yan ta’addan suka yi amfani da ita.
A wani samame na daban, dakarun Bataliya ta 233 tare da haɗin gwiwar mafarauta sun cafke mutane biyar da ake zargin masu garkuwa da mutane ne a ƙauyen Jegalari da ke ƙaramar hukumar Fune. An kuma ƙwato bindigogi, alburusai da wayoyin hannu daga hannunsu.
Rahotanni sun nuna cewa hare-haren sama da aka kai bisa ingantattun bayanan sirri sun yi wa ‘yan ta’adda mummunar illa. A yankin Kala Balia da ke ƙaramar hukumar Marte ta Borno, jiragen yaƙin sama sun kashe kusan ‘yan ta’adda 15 bayan gano maboyarsu.
Hakazalika, a wani harin dare tsakanin Bama da Maiduguri, jiragen yaƙin sama sun yi luguden wuta kan wasu wurare da aka gano motsin ‘yan ta’adda, lamarin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum takwas daga cikinsu.
A Zamfara, dakarun Operation FANSAN YAMMA sun gwabza faɗa da ‘yan ta’adda a Dutsen Gambada da ke ƙaramar hukumar Gummi, yayin da a Jihar Kogi dakarun Brigade ta 12 suka daƙile wani yunƙurin satar mutane a kan hanyar Kabba zuwa Ayere. Sun ceto mutum shida da aka yi garkuwa da su, waɗanda daga bisani aka kai Asibitin St. Joseph da ke Kabba domin samun kulawar likitoci.
A Nasarawa kuma, dakarun Operation WHIRL STROKE sun kuɓutar da wani mutum da aka yi garkuwa da shi a yankin Tunga na ƙaramar hukumar Awe.
A wani samame da aka kai a yankin Awara Waterside na Kudu maso Gabas, dakarun Operation UDO KA sun bankaɗo maboyar masu aikata laifuka, inda suka ƙwato bindigogin Lee-Enfield da G3 tare da alburusai masu yawa.
Rundunar Sojin Najeriya ta ce nasarorin sun sake nuna tasirin amfani da sahihan bayanan sirri da kuma haɗa hare-haren sama da na ƙasa wajen karya ƙarfin ‘yan ta’adda da masu garkuwa da mutane. Ta kuma tabbatar da cewa za ta ci gaba da matsa musu lamba har sai an murƙushe dukkan ƙungiyoyin masu aikata laifuka a faɗin Nijeriya.






