Gwamnan Jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya gudanar da wani muhimmin taro da ƴan takarar Jam’iyyar APC da kuma waɗanda suka nemi takara amma ba su yi nasara ba a zaɓen fidda gwani da aka gudanar a sassa daban-daban na jihar.
Taron, wanda aka yi a Babban Ɗakin Taro na Gidan Gwamnatin Jihar da ke Minna a ranar Asabar, ya mayar da hankali kan ƙarfafa haɗin kai a tsakanin mambobin jam’iyyar da kuma tsara dabarun tabbatar da nasarar dukkan ƴan takarar APC a babban zaɓen shekarar 2027.
A cikin wata sanarwa da Babban Sakataren Yaɗa Labarai na Gwamnan Jihar, Bologi Ibrahim, ya fitar, Gwamna Bago ya buƙaci dukkan ƴan takara da waɗanda suka nemi takara da su rungumi sakamakon zaɓen cikin ruhin wasa, tare da ci gaba da jajircewa wajen ciyar da manufofin Jam’iyyar APC gaba.
Ya kuma yi kira gare su da su mara wa shirin “Renewed Hope” na Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kuma ajandar “New Niger” ta gwamnatin jihar baya, yana mai cewa haɗin kai ne ginshiƙin nasarar jam’iyyar.
Gwamnan ya jaddada muhimmancin biyayya ga jam’iyya da haɗin kai tsakanin mambobinta, yana mai cewa lokaci ya yi da kowa zai ajiye bambance-bambance a gefe domin a haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen tabbatar da nasarar APC da kuma ci gaba da isar da romon dimokuraɗiyya ga al’ummar Jihar Neja.
Har ila yau, taron ya bai wa mambobin APC daga sassa daban-daban na jihar damar tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jam’iyyar, tare da gabatar da shawarwari kan hanyoyin ƙara ƙarfafa shirye-shiryenta da dabarun tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.







