• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gaskiyar yadda Abacha ya rasu, cewar tsohon jami’in DSS

ALI KANO by ALI KANO
July 21, 2026
in Labarai
A A
0
Gaskiyar yadda Abacha ya rasu, cewar tsohon jami’in DSS
Sabon littafin (a hagu), da kuma Janar Abacha

Sabon littafin (a hagu), da kuma Janar Abacha

Wani tsohon Mataimakin Darakta a Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS), Mista Dennis Amachree, ya bayyana wani sabon bayani kan yadda tsohon Shugaban Mulkin Soja na Nijeriya, Janar Sani Abacha, ya rasu, inda ya ce marigayin ya mutu ne sakamakon bugun zuciya yayin wata mu’amala ta kusanci da wata mata a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Amachree, wanda ya kasance Mataimakin Daraktan Ayyuka da Leƙen Asiri na DSS a Legas lokacin rasuwar Abacha a watan Yuni 1998, ya bayyana hakan ne a cikin sabon littafin labarin rayuwar sa mai suna DSS @40: My Journey Behind the Shield.

Abacha ya mulki Nijeriya daga watan Nuwamba 1993 zuwa rasuwar sa a watan Yuni 1998, an sha yin ce-ce-ku-ce dangane da yadda ya rasu.

A cewar wasu sassan littafin da jaridar The Nation ta wallafa, Amachree ya ce Abacha ya rasu da misalin ƙarfe 4:05 na asubahin ranar a Fadar Shugaban Ƙasa yayin da yake tare da wata mata, wadda daga bisani ta bar wurin tare da hawa jirgin farko zuwa Legas.

Tsohon jami’in DSS ɗin ya ce matar ta isa fadar Aso Rock tare da yayar ta, wadda ya bayyana a matsayin budurwar Abacha. A cewar sa, yayar ta bar ƙanwar ta tare da shugaban ƙasar, ta koma otal ɗin da ta sauka.

Ya ce: “Da misalin ƙarfe 2:40 na dare, jim kaɗan bayan Janar Useni ya tafi gida, budurwar Abacha, wata ‘yar kabilar Igbo (ba a bayyana sunan ta ba), ta isa Gidan Baƙi na Aso Rock daga otal ɗin Nicon Noga Hilton.

“Tare da ita akwai ƙanwar ta, wacce ƙwararriyar mai harhaɗa magunguna ce (pharmacist) kuma ta zo Abuja ne domin halartar wani taro. Shugaban Mulkin Sojan ya riga ya saya wa budurwar tasa sabuwar mota ƙirar SUV, don haka suka yanke shawarar su biya su gaisa da ‘Oga’.

“Abacha ya nuna sha’awar sa ga ƙanwar, kuma bayan ɗan lokaci kaɗan sai budurwar tasa ta koma otal, ta bar ƙanwar mai harhaɗa magungunan ita kaɗai tare da Shugaban Mulkin Sojan.

“Da misalin ƙarfe 4:05 na asuba, yayin da suke jima’i, sai ƙwararriyar mai harhaɗa magungunan ta lura da cewa Abacha ya daina motsi. Ta kira shi, amma bai amsa ba kuma jikin sa ya ƙame. Ta duba bugun zuciyar sa; babu.

“Cikin firgici, ta yi saurin sanya tufafin ta, ta fito daga gidan baƙin, inda ta gaya wa sojan da ke gadi a wurin cewa ‘Oga’ ya ce a samo mata motar da za ta mayar da ita otal.

“Nan take sojan, ba tare da sanin girman abin da ya faru ba, ya shirya mata abin hawa. Ta koma Hilton, kuma bayan ta gaya wa ‘yar’uwar ta abin da ya faru, sai aka hanzarta kai ta Filin Jirgin Sama na Abuja domin ta hau jirgin Okada Airline na ƙarfe 7 na safe zuwa Legas.

“Wannan shi ne labarin da Manjo Al-Mustapha bai sani ba. Lokacin da aka sanar da shi halin da Janar ɗin yake ciki da misalin ƙarfe 5 na safe, sai ya tambayi wanda ya kasance tare da Janar ɗin. Aka gaya masa cewa ƙanwar budurwar sa ce, wadda aka saukar a Hilton ɗazu.

“Nan take aka sanar da Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (SSS), wadda ta tafi Hilton domin kama budurwar, amma ƙwararriyar mai harhaɗa magungunan da suke matuƙar buƙata ta riga ta kama hanyar Legas.”

Amachree ya yi iƙirarin cewa daga bisani ya yi wa matar tambayoyi a unguwar Ogudu da ke Legas, bayan samun umurni daga Daraktan Ayyuka na hedikwatar DSS ta ƙasa.

A cewar sa, kalmomin farko da matar ta furta masa yayin tambayoyin su ne: “Ban kashe shi ba, ya mutu ne a kai na.”

Ya ce bayanin da matar ta bayar ya saɓa wa shaci-faɗi da rabin-gaskiyar da aka riƙa yaɗawa cewa akwai wani makirci da aka ƙulla game da rasuwar Abacha — ciki har da batun wai “an shigo masa da ‘yanmatan Indiya da tuffa mai guba”.

Ya ce: “Tawagar (jami’an tsaro) ta gano inda take, ta kuma kawo ta ofishi na. Ni da kai na ne na yi mata tambayoyi.

“Abu na farko da ta faɗa mini shi ne: ‘Ban kashe shi ba, ya mutu ne a kai na.’ Bayan ta ba da cikakken bayani, sai na kira Daraktan mu da ke Abuja na faɗa masa, kuma nan take aka mayar da ita can ta jirgin sama.

“Bayanin da wannan ƙwararriyar mai harhaɗa magunguna ta bayar, wadda a bisa alama Janar Abacha ya samu bugun zuciya ne yayin tarawa da ita, shi ne ainihin abin da ya faru, kuma ya kawo ƙarshen shaci-faɗin akwai makirci da kuma rabin gaskiyar da aka baza.”

Shi dai Abacha, ya rasu ne a ranar 8 ga Yuni, 1998, bayan ya shafe kusan shekara biyar yana mulkin Nijeriya a matsayin Shugaban Mulkin Soja.

Rasuwar sa ta zo ne ƙasa da wata guda kafin rasuwar Cif Moshood Kashimawo Olawale (MKO) Abiola, wanda aka fi ɗauka a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na ranar 12 ga Yuni, 1993 da aka soke, kuma wanda ya rasu yana tsare a hannun gwamnati yayin da yake fafutukar neman a mayar masa da haƙƙin nasarar sa.

Tags: bugun zuciyaJanar Sani Abachalittafimutuwatarawa
Previous Post

Illolin Kallon Finafinan Batsa A Addini Da Kimiyya

Next Post

Gwamnati Tarayya ta musanta karɓar sabon bashin tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
An Bayyana Waɗanda Ba Za Su Biya Haraji Ba A Nijeriya

Gwamnati Tarayya ta musanta karɓar sabon bashin tiriliyan ₦80 cikin shekaru uku

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!