Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da dama a faɗin Nijeriya sun fara karɓar ajiya ta farko mafi ƙaranci ta Naira miliyan 4 daga masu niyyar zuwa aikin Hajjin 2027, sakamakon umurnin da Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON) ta bayar.
Hukumar ta bayyana cewa matakin yana daga cikin shirye-shiryen fara gudanar da aikin Hajjin shekarar 1448H/2027, domin ba da damar tsara muhimman ayyukan hajji tun da wuri.
A cikin wata takarda mai ɗauke da kwanan watan 15 ga Yuni, 2026 mai taken “Fara Shirye-shiryen Hajjin 1448H/2027,” NAHCON ta umurci dukkan Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, hukumomi da kwamitocin hajji, da kuma kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi, da su fara shirye-shiryen aikin hajji nan take bisa ƙa’idojin da Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta gindaya.
NAHCON ta ce an ƙayyade ajiya ta farko mafi ƙaranci ga aikin Hajjin 2027 a kan Naira miliyan 4, tana mai bayyana cewa za a bayyana kuɗin hajjin na ƙarshe ne bayan kammala shawarwari da masu ruwa da tsaki da kuma tattaunawa da masu ba da ayyukan hajji a Masarautar Saudiyya.
Hukumar ta sanya ranar 26 ga Satumba, 2026 a matsayin wa’adin kammala karɓar kuɗaɗen ajiya daga Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi da kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi, domin ba da damar tsara shirye-shirye da ƙulla yarjejeniyoyi cikin lokaci.
Ta ce jihohi da dama sun riga sun fara karɓar kuɗaɗen daga masu niyyar zuwa aikin hajji, yayin da ake ci gaba da shirye-shiryen aikin a sassa daban-daban na ƙasar nan bisa jadawalin da aka amince da shi.
NAHCON ta shawarci masu niyyar zuwa aikin hajji da su biya kuɗin su ne kawai ta hanyar Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na jihohin su ko kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi idan ya dace.
Haka kuma ta buƙace su da su tabbatar sun karɓi takardar shaidar biyan kuɗi a duk lokacin da suka biya kuɗi.
A cewar hukumar, fara karɓar ajiya tun da wuri zai taimaka wajen tsara muhimman fannoni na aikin hajji kamar masauki, sufuri, ciyarwa, kiwon lafiya da sauran harkokin gudanarwa.
Ta ƙara da cewa yin rajista da wuri daga maniyyata zai taimaka wajen gudanar da aikin Hajjin 2027 cikin tsari da nasara.
NAHCON ta sake jaddada aniyar ta ta ci gaba da aiki tare da Hukumomin Jin Daɗin Alhazai na Jihohi, kamfanonin yawon buɗe ido masu lasisi da sauran masu ruwa da tsaki domin tabbatar da an gudanar da Hajjin 1448H/2027 cikin sauƙi, inganci da nasara.
Haka kuma ta buƙaci jihohin da ba su fara karɓar kuɗaɗen ajiya ba da su hanzarta kammala shirye-shiryen su bisa jadawalin da aka amince da shi.







