• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabuwar dokar daidaita harkokin kadarorin Intanet

Wakilin Mu by Wakilin Mu
July 17, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cika shekara uku a mulki: Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun fara haifar da ɗa mai ido
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya sanya hannu kan Sabuwar Dokar Shugaban Ƙasa kan Daidaita Harkokin Kadarorin Intanet (Virtual Assets Coordination Executive Order, 2026), domin haɗa kai tsakanin hukumomin gwamnati wajen sa ido kan harkokin kuɗaɗen intanet da sauran kadarorin zamani. Dokar ta fara aiki nan take bayan sanya hannu.

A cewar sanarwar Fadar Shugaban Ƙasa, dokar za ta magance matsalolin rashin daidaiton ayyukan hukumomi daban-daban, wanda ya bai wa wasu masu damfara damar yaudarar ‘yan ƙasa. Haka kuma, za ta taimaka wajen yaƙi da safarar kuɗaɗe ba bisa ƙa’ida ba, tallafa wa ta’addanci ta hanyar kuɗi, barazanar tsaron intanet, da kuma kare bayanan masu amfani.

Sabuwar dokar ta kafa Majalisar Kula da Kadarorin Intanet, wadda Babban Bankin Najeriya (CBN) zai jagoranta.

Hukumar Haraji ta Nijeriya (NRS) da Hukumar Kasuwar Hannayen Jari (SEC) za su kasance mataimakan shugabanni, yayin da Hukumar NFIU da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) za su kasance mambobi. Haka kuma, an kafa Ofishin Kula da Kadarorin Intanet, wanda zai kasance ƙarƙashin CBN domin gudanar da ayyukan yau da kullum.

Sanarwar ta bayyana cewa dokar ba ta kafa sabuwar hukuma ba, kuma ba ta ƙwace ikon kowace hukuma ba. Maimakon haka, za ta tabbatar da haɗin kai tsakanin hukumomin domin sauƙaƙe rajistar masu gudanar da harkokin kadarorin intanet, tare da rufe gibin da masu gudanar da ayyukan ba bisa ƙa’ida ba ke amfani da shi wajen guje wa sa ido.

Haka zalika, CBN zai ƙaddamar da Regulatory Sandbox domin bai wa kamfanonin fasahar kuɗi damar gwada sabbin kayayyaki da ayyukan blockchain ƙarƙashin kulawa kafin a fitar da su kasuwa.

Ita ma Hukumar Haraji ta Nijeriya za ta fitar da manufofin haraji kan kadarorin intanet, yayin da Majalisar da aka kafa aka umurce ta da ta samar da tsarin aiwatar da dokar cikin kwanaki 30 domin tabbatar da fara aiki cikin gaggawa.

Tags: dokaharajiintanet
Previous Post

Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya

Next Post

Hajjin 2027: Jihohi sun fara karɓar kuɗin ajiyar farko ta Naira miliyan 4

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Hajjin 2027: Jihohi sun fara karɓar kuɗin ajiyar farko ta Naira miliyan 4

Hajjin 2027: Jihohi sun fara karɓar kuɗin ajiyar farko ta Naira miliyan 4

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!