Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya taya Dakta Omoniyi Ibietan murnar sake zaɓen sa a matsayin Sakatare Janar na Ƙungiyar Masu Hulɗa da Jama’a ta Afrika (wato African Public Relations Association, APRA), inda ya bayyana cewa hakan wata shaida ce ta ƙwarewar sa, jajircewar sa da gagarumar gudunmawar da yake bayarwa ga fannin hulɗa da jama’a a nahiyar Afrika.
An sake zaɓen Dakta Ibietan ne a yayin Babban Taron APRA da aka gudanar a birnin Swakopmund na ƙasar Namibiya. Haka kuma, an zaɓi Mista Arik Karani na ƙasar Kenya a matsayin Shugaban Ƙungiyar, yayin da aka zaɓi Farfesa Michele Mekeme daga Kamaru a matsayin Mataimakiyar Shugaba.
A cikin saƙon taya murna da ya aike, ministan ya ce sake zaɓen Dakta Ibietan ya nuna irin amincewar da ƙwararrun masu hulɗa da jama’a a faɗin Afrika suke da ita ga jagorancin sa da kuma ƙwarewar sa wajen ciyar da manufofin ƙungiyar gaba.
Ministan ya ce: “A madadin Gwamnatin Tarayya, ina taya Dakta Omoniyi Ibietan murnar sake zaɓen sa a matsayin Sakatare Janar na APRA. Wannan karramawa ba wai kawai amincewa ce da ƙwarewar sa ta fannin aiki ba ce, abin alfahari ne ga Nijeriya da ɗaukacin al’ummar masu aikin sadarwa.”
Idris ya bayyana jin daɗin cewa Dakta Ibietan zai ci gaba da bayar da jagoranci nagari yayin da APRA ke ƙara ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen Afrika tare da tallafa wa ajandar sauyin fasahar dijital ta nahiyar.
Har ila yau, ya yaba wa APRA kan jajircewar ta wajen bunƙasa fannin hulɗa da jama’a da inganta sadarwa bisa ɗa’a a faɗin Afrika.
Ya ce Nijeriya tana ɗokin karɓar baƙuncin Taron APRA na shekara karo na 37 tare da Dandalin Hulɗa da Jama’a na Duniya, waɗanda za a gudanar a Abuja nan gaba a wannan shekara.







