• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
July 17, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Mista Olayemi Cardoso

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Mista Olayemi Cardoso, ya bayyana yadda sauye-sauyen da aka aiwatar a fannin sarrafa kasuwar musayar kuɗaɗen waje, manufofin kuɗi da kuma tabbatar da ƙarfafa tsarin kuɗi suka fara inganta yanayin tattalin arzikin Nijeriya.

Cardoso ya yi bayanin ne filla-filla a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026, wanda jaridar BusinessDay ta shirya.

Muhimman abubuwan da ya bayyana sun haɗa da:

Jimillar adadin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya, wanda yanzu ya ƙaru zuwa dala biliyan 52.

“Haka kuma, adadin ajiyar kuɗaɗen waje na ainihi ya kai kusan dala biliyan 40, lamarin da ya ƙara ƙarfafa matsayin tattalin arzikin Nijeriya da kuma amincewar masu zuba jari.”

CBN na ci gaba da ƙudirin cimma burin samun dala biliyan 1 a kowane wata daga kuɗaɗen da ‘yan Nijeriya mazauna ƙasashen waje ke aikowa gida nan da ƙarshen shekarar 2026.

Wani sashe na mahalartan Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026, wanda jaridar BusinessDay ta shirya

Ya kuma ce kasuwar musayar kuɗaɗen waje ta samu isasshen kuɗi, har ta kai ga ba ta buƙatar yawan tsoma bakin CBN.

Shirin ƙara ƙarfi da yawan jarin bankuna ya haifar da ƙaruwar samun sabon jari da ya kai kusan Naira tiriliyan 4.65, lamarin da ya ƙara ƙarfafa tsarin bankunan Nijeriya ta hanyar ingantaccen sa-ido da ƙa’idoji.

Amincewar jama’a da tsarin biyan kuɗi na Nijeriya ta ƙaru sosai, inda yanzu ‘yan Nijeriya ke iya amfani da katin cire kuɗi na banki cikin sauƙi wajen gudanar da mu’amaloli a ƙasashen waje.

Yayin da hauhawar farashi ke raguwa, kuma ribar ruwa ke fara sauƙaƙa a hankali, CBN na sa ran bankuna za su ƙara bayar da rance ga sassan da ke samar da ci gaba, musamman ƙanana da matsakaitan masana’antu (SMEs), tare da ci gaba da kiyaye ƙa’idojin gudanar da haɗarin bashi.

“CBN zai ci gaba da aiki kafaɗa da kafaɗa da cibiyoyin kuɗi domin ƙara ƙarfafa ƙarfin su tare da daidaita tsarin bankunan Nijeriya da ƙa’idojin da ake bi a duniya,” cewar Cardoso.

Mista Olayemi Cardoso, yana jawabi a taron

Da yake jawabi ga shugabannin kamfanoni, Cardoso ya buƙace su da su yi amfani da damar da ingantuwar yanayin tattalin arzikin ƙasar ke samarwa, maimakon ci gaba da zama masu kallo.

“A matakin da muka kai yanzu, mun samu kwanciyar hankali ne bayan ƙoƙari mai yawa. Idan akwai kwanciyar hankali, akwai damar zuba jari, kuma idan aka samu zuba jari, ci gaba zai biyo baya. Don haka ina kira ga dukkan shugabannin kamfanonin mu na cikin gida da su kasance cikin wannan tafiya ta ci gaba da ƙasar nan ke yi”, inji Cardoso.

Tags: Babban Bankin Nijeriya (CBN)BusinessDayMista Olayemi CardosoTaron Shugabannin Kamfanoni na 2026
Previous Post

Ɗan Goodluck Jonathan, Ariwera, ya yi bikin kammala karatun jami’a a Birtaniya

Next Post

Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabuwar dokar daidaita harkokin kadarorin Intanet

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Cika shekara uku a mulki: Tinubu ya ce sauye-sauyen tattalin arziki sun fara haifar da ɗa mai ido

Gwamnatin Tarayya ta fitar da sabuwar dokar daidaita harkokin kadarorin Intanet

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!