Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta aiwatar da manyan sauye-sauye a fannin fansho cikin shekaru biyu da suka gabata, inda ta kashe Naira biliyan 758 wajen biyan basussukan haƙƙoƙin fansho da suka taru tun daga shekarar 2007, tare da ƙara yawan kuɗin da masu ritaya ke karɓa a kowane wata.
Darakta Janar ta Hukumar Fansho ta Ƙasa (PenCom), Misis Omolola Oloworaran, ita ce ta bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja yau Talata.
Ta ce biyan basussukan ya amfani kusan masu ritaya 957,045, tare da rage jinkirin biyan haƙƙoƙin fansho daga watanni 21 zuwa matsayin da gwamnati ke da tanadin kuɗaɗen biyan fansho na watanni 41 a gaba.
A cewar ta, jimillar kuɗaɗen da ke cikin tsarin fansho ta ƙaru daga Naira tiriliyan 20.79 zuwa Naira tiriliyan 31.48 cikin shekaru biyu, lamarin da ta ce ya nuna ƙaruwar amincewar ma’aikata da tsarin.
Ta ƙara da cewa sama da sabbin ma’aikata 938,000 sun shiga tsarin fansho a cikin wannan lokaci.
Oloworaran ta ce gwamnatin ta ƙaddamar da shirin Pension Boost 1.0, wanda ya ƙara jimillar kuɗin fansho da ake biya kowane wata daga Naira biliyan 12.2 zuwa Naira biliyan 14.9.
Ta bayyana cewa gwamnatin ta amince da ƙarin Naira 32,000 ga dukkan masu ritayar ma’aikatan gwamnatin tarayya da suka yi ritaya kafin ranar 29 ga Yuli, 2024, domin daidaita kuɗin fanshon su da sabon mafi ƙarancin albashi.
Har ila yau, ta ce an yi bitar kuɗin fanshon tsofaffin ma’aikatan NSITF karo na farko cikin shekara 21, inda wasu daga cikin su suka tashi daga karɓar Naira 18,000 zuwa Naira 206,000 a kowane wata, tare da biyan su bashin haƙƙoƙin fansho da ake bin su.
Ta ce matakan da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ɗauka sun taimaka wajen inganta tsarin fansho, da tabbatar da biyan haƙƙoƙin masu ritaya cikin lokaci, tare da ƙara jin daɗin rayuwar su.






