• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Cewar CBN: Har yanzu takardar Naira 100 ta ainihi halastacciya ce, ba a haramta hadahadar kuɗi da ita ba

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
July 8, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Cewar CBN: Har yanzu takardar Naira 100 ta ainihi halastacciya ce, ba a haramta hadahadar kuɗi da ita ba
Tsohuwar takardar naira

Tsohuwar takardar naira

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙaryata raɗe-raɗi da rahotanni masu yayata cewa ya sanar da daina amfani da takardar Naira 100 ta ainihi.

Cikin wata sanarwar da CBN ya fitar a ranar Laraba, 8 ga Yuli 2026, mai ɗauke da sa hannun Daraktar Riƙo ta Sashen Hulɗa da Jama’a da Sadarwa, Hajiya Hakama Sidi Ali, bankin ya yi ƙarin haske kan matsayin takardar kuɗin Naira ₦100 a matsayin halastacciya abin ci gaba da karɓa da yin hadahadar kuɗin biyan buƙatun yau da kullum.

Kan haka, CBN ya ja hankalin jama’a kan su yi watsi da rahotannin da ke nuna cewa wasu daga cikin jama’a, ‘yan kasuwa da sauran masu ruwa da tsaki suna ƙin karɓar tsohuwar takardar kuɗin Naira 100, bisa zargin cewa ta daina kasancewa halastacciyar takardar kuɗi.

Domin kawar da duk wata shakka, CBN yana sake jaddada cewa takardar kuɗin Naira 100 ta musamman, wadda aka fito da ita daga baya da kuma takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullum, wato wancan ta farko, har yanzu halastattun takardun kuɗi ne a Nijeriya, kuma dole ne a karɓe su wajen dukkan mu’amaloli a faɗin Nijeriya.

“Takardar Naira 100 ta musamman, wadda aka fitar domin bikin cika shekaru 100 da kafuwar Nijeriya, ba ta maye gurbin tsohuwar takardar N100 ta yau da kullum ba.

“CBN na gargaɗin mutane, ‘yan kasuwa, cibiyoyin kuɗi da sauran masu gudanar da harkokin tattalin arziki ceqa kada su ƙi karɓar takardar kuɗin Naira 100 ta yau da kullum. Domin yin hakan ya saɓa wa tanade-tanaden Dokar CBN kuma yana raunana amincewar jama’a da kuɗin ƙasar nan.”

CBN ya yi gargaɗin cewa ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar matakan dokar da suka dace kan duk wani mutum ko hukuma da aka samu da laifi ba.

“CBN ya ci gaba da jajircewa wajen kare mutuncin Naira, tabbatar da amincewa da dukkan takardun kuɗi da aka fitar bisa doka, tare da inganta zagayawar kuɗi cikin sauƙi a faɗin Nijeriya.”

Sanarwar ta ci gaba da yin bayani cewa, “ana kira ga dukkan ‘yan Nijeriya su riƙa karɓa tare da gudanar da mu’amala da dukkan takardun kuɗin da Babban Bankin Nijeriya ya fitar bisa doka.”

Domin samun ƙarin bayani, an kuma shawartar jama’a da su tuntuɓi CBN ta hanyoyin sadarwar hukuma na bankin.

Previous Post

Gani Ya Kori Ji: Aikin layin dogo na Kano-Maraɗi zai sauya tattalin arzikin Arewa — Jami’ai

Next Post

Gani Ya Kori Ji: Aikin titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato zai bunƙasa tattalin arziki da kasuwancin Arewa – Jami’ai

Related Posts

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Shawarar CBN ga gwamnatocin jihohi: “A kiyaye bin ƙa’idojin kashe kuɗaɗe, a daina ciwo bashin alaƙaƙai
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara ba da fifikon sa-ido wajen daƙile hadahadar kuɗaɗen ɗaukar nauyin ta’addanci

September 9, 2026
Next Post
Gani Ya Kori Ji: Aikin titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato zai bunƙasa tattalin arziki da kasuwancin Arewa – Jami’ai

Gani Ya Kori Ji: Aikin titin Zariya–Funtuwa–Gusau–Sakkwato zai bunƙasa tattalin arziki da kasuwancin Arewa - Jami'ai

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!