Mai Taimaka wa Shugaban Ƙasa na Musamman kan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Alhaji Abdulaziz Abdulaziz, ya ce bunƙasar dimokiraɗiyya da cigaban ƙasa suna buƙatar amincewa da haɗin kai tsakanin gwamnati, kafafen yaɗa labarai da kuma al’umma.
Abdulaziz ya bayyana hakan ne a jawabin maraba da ya gabatar a wajen buɗe Taron Manema Labarai na Arewa karon farko na Arewa (Arewa Media Summit) da aka gudanar a yau Litinin a Kano.
Ya ce taron ya haɗa shugabanni, ‘yan jarida, masu ƙirƙirar abubuwan da ake wallafawa a soshiyal midiya, masu tasiri da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a ƙarfafa alaƙar gwamnati da jama’a ta hanyar gaskiya, riƙon amana da ɗabi’ar aikin jarida.
A cewar sa, taken taron, wato “Government-Citizen Accord: Accountability, Responsibility and Ethical Media Practice”, ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar sake gina amincewa tsakanin gwamnati da al’umma.
Ya bayyana cewa gwamnati tana da alhakin buɗe ƙofofin samun bayanai, yayin da al’umma ke da nauyin tabbatar da gaskiya kafin yaɗa bayanai da kuma riƙe gwamnati da alhakin ayyukan ta cikin lumana.
Ya ce kafafen yaɗa labarai su ne gada tsakanin gwamnati da jama’a, yana mai cewa ingantaccen aikin jarida da tabbatar da sahihancin labarai na taimakawa wajen gina zaman lafiya, haɗin kai da cigaban ƙasa.
Abdulaziz ya kuma jaddada cewa masu tasiri a soshiyal midiya sun zama sababbin masu jan ragamar yaɗa bayanai, don haka wajibi ne su riƙa tantance gaskiyar bayanai kafin wallafawa.
“A yau, saƙon da aka wallafa na iya haifar da fata ko kuma tayar da husuma cikin ɗan lokaci. Don haka bai kamata neman farin jini ko yawan masu kallo ya zama sanadin jefa ƙasa cikin rikici ba,” inji shi.
Ya ƙara da cewa yayin da zaɓen shekarar 2027 ke ƙaratowa, akwai buƙatar masu amfani da shafukan sada zumunta su ɗauki kan su a matsayin masu kare zaman lafiyar al’umma, tare da gyara kurakuren su idan sun faru.
Ya bayyana cewa a wani ɓangare na shirye-shiryen taron, an horas da sama da mutum 100 daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar APC da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu kan dabarun yaɗa bayanai da bayyana manufofi da nasarorin gwamnati yadda ya kamata.
Haka kuma ya ce an ƙaddamar da shirin Gani-Ya-Kori-Ji, wanda zai zagaya jihohin Arewacin Nijeriya domin duba da kuma haska ayyukan cigaba da Gwamnatin Tarayya da gwamnatocin jihohi suka aiwatar, musamman waɗanda ba su samu isasshen haske a idon jama’a ba.
Abdulaziz ya ce taron ya nuna irin ƙudirin gwamnatin Tinubu na kare ‘yancin faɗin albarkacin baki, ƙarfafa tattaunawa da kuma bunƙasa dimokiraɗiyya.
Ya bayyana cewa an tsara taron ne domin bai wa mabambantan ra’ayoyi da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na Arewacin Nijeriya damar tattaunawa kan makomar hulɗar gwamnati da jama’a.
A ƙarshe, ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da karɓar baƙuncin taron, yana mai cewa Kano ta ci gaba da kasancewa cibiyar siyasa, kasuwanci da tattaunawa a Nijeriya.
Ya buƙaci mahalarta taron da su fito da sababbin alƙawurra da za su inganta buɗaɗɗen tsarin gudanar da mulki, ƙarfafa ɗabi’ar aikin jarida da kuma inganta alaƙar gwamnati da al’umma.







