Ofishin Akanta Janar na Tarayya (OAGF) ya wanke Babban Bankin Nijeriya (CBN) daga masu zargin cewa bankin ya buɗe wa hukumar bogi (PFIPC) wadda ɗan harƙalla Adeyemi Mathew ya kafa asusun da har an saka mata kuɗi daga CBN a cikin sa.
Ofishin na Akanta Janar ya bayyana cewa ba a samu nasarar buɗe asusun da Adeyemi ya yi ƙoƙarin buɗe wa hukumar ba a CBN, duk da cewa an ware ‘hukumar’ kuɗi a cikin Dokar Kasafin Kuɗin Tarayya ta shekarar 2026.
Daraktan Yaɗa Labarai da Hulda da Jama’a na OAGF, Bawa Mokwa, ya sanar da hakan ne a ranar Litinin, yana mai ƙarin haske da cewa yinƙurin buɗe asusun da Adeyemi Matthew ya fara bai kammalu ba, saboda ba a gabatar da sunayen mutanen da za su kasance masu sa hannu a asusun ba.
A cewar Mokwa, rashin gabatar da sunayen masu izinin sa hannu ne ya hana buɗe asusun, don haka ba a saka wani kuɗi a cikinsa ba.
Ya ce, “Ba a samu nasarar buɗe asusun CBN ba saboda dole ne idan za a buɗe asusun sai an gabatar da sunayen masu sa hannu a irin wannan asusu, amma ba a yi hakan ba. Saboda haka, ba a biya ko sisin kwabo na kuɗin gwamnati a cikin wannan asusun ba.”
Mokwa ya ci gaba da ƙarin haske cewa, duk da cewa PFIPC ta samu rabon kasafi a cikin kasafin kuɗin gwamnatin tarayya na shekarar 2026, sai a watan Yulin nan ne ma barin aiwatar da kasafin zai fara.
Saboda haka ya ce, “Da wannan halin da ake ciki yanzu, a bayyane yake cewa ba za a iya tura wani kuɗi cikin wannan asusun ba.”
Ya kuma bayyana cewa asusun da aka nemi buɗewa a CBN bai samu amincewar da ake buƙata daga Akanta Janar na Tarayya ba.
Har ila yau, Mokwa ya ce ban da ma’aikatan da OAGF ta tura, babu wasu sabbin ma’aikata da majalisar ta ɗauka ƙarƙashin jagorancin Darakta Janar nata. Ya ƙara da cewa ma’aikatan da aka tura za su kasance shaidu a gaban kotu idan aka fara gurfanar da masu ruwa da tsakin harƙallar.
Wannan labari na nuni da cewa kuɗin da aka ware wa Kwamitin Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Tattalin Arziki na bogi da Mathew da kafa, wato ‘Presidential Economic Advisory Council/Presidential Foreign Intervention Promotion Council, (PFIPC), an ware masa jimillar naira biliyan 1.303 a cikin kasafin kuɗi na 2026, amma kuma CBN bai tura masa ko ƙwandala.






