Wasu mahara sun kashe Shugaban Ƙungiyar Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) na Jihar Binuwai, Arɗo Risku Muhammad, a wani kwanton ɓauna da suka yi masa a Ƙaramar Hukumar Otukpo ta jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2:00 na rana a jiya Juma’a a kusa da ƙauyen Okudu, inda marigayin da abokin tafiyar sa, Yakubu Isah, suka fuskanci harin yayin da suke dawowa daga wani taron lumana da aka gudanar a maƙwabciyar Ƙaramar Hukumar, wato Ohimini.
Majiyoyi sun ce mutanen biyu sun halarci taron sulhu da tsaron wanda ake zargin Difi’on ‘Yan Sanda (DPO) na Idekpa da ke Ƙaramar Hukumar Ohimini ya kira, kafin su kama hanyar komawa gida.
Rahotanni sun bayyana cewa wasu matasa ɗauke da makamai sun yi musu kwanton ɓauna tare da buɗe musu wuta, lamarin da ya yi sanadin mutuwar su nan take.
Babban ɗan marigayin, Idris Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa an kai wa mahaifin sa da Yakubu Isah hari ne jim kaɗan bayan sun bar wurin taron sulhun.
Ya ce iyalan su sun karɓo gawarwakin mutanen biyu kuma sun kai su Oyangede domin binne su.
Ya ce, “Sun kashe mahaifi na, Ardo, tare da abokin tafiyar sa Yakubu Isah, da misalin ƙarfe 2:00 na rana yayin da suke dawowa daga taron sulhun da DPO na Ohimini ya kira. Mun karɓo gawarwakin su kuma mun kai su Oyangede domin yi musu jana’iza.”
Kisan ya ƙara tayar da hankula a yankin, inda jama’a suke nuna fargabar yiwuwar ɗaukar fansa da kuma sake taɓarɓarewar tsaro.
Shugaban Ƙaramar Hukumar Otukpo, Maxwell Ogiri, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa halin tsaro a yankin da abin ya faru ya yi tsami.
Ya roƙi mazauna yankin da su kwantar da hankalin su, yana mai cewa jami’an ‘yan sanda da sauran hukumomin tsaro sun riga sun fara ɗaukar matakan da suka dace domin hana ɓarkewar rikici.
Ya ce, “A halin yanzu yankin da abin ya faru yana cikin yanayi mai cike da tashin hankali, amma ina roƙon jama’a su kwantar da hankalin su domin jami’an ‘yan sanda suna kan lamarin.”
Shi ma Shugaban Ƙaramar Hukumar Ohimini, Gabriel Adole, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa mariganyi shugaban MACBAN ɗin ya halarci wani taron sulhu inda aka cimma nasara kafin daga bisani a kai masa hari a Otukpo.
Adole ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici, yana mai cewa an sanar da hukumomin tsaro, kuma ana sa ran za su gudanar da bincike domin gano yadda aka aiwatar da kisan.
Ita ma rundunar ‘Yan Sandan Jihar Binuwai ta tabbatar da faruwar lamarin ta bakin kakakin ta, DSP Udeme Edet, wadda ta ce an fara gudanar da bincike.
Edet ta tabbatar wa da jama’a cewa rundunar za ta yi aiki tuƙuru domin gano waɗanda suka kai harin tare da gurfanar da su gaban shari’a, sannan ta buƙaci mazauna yankin su ci gaba da zaman lafiya tare da bai wa masu bincike cikakken haɗin kai.






