• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya umurci bankuna su gaggauta kulle asusun ajiya da kadarorin waɗanda da ake zargi da tallafa wa ta’addanci

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 25, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN ya umurci bankuna su gaggauta kulle asusun ajiya da kadarorin waɗanda da ake zargi da tallafa wa ta’addanci
Wani ɗan canji yana ƙirga kuɗi

Wani ɗan canji yana ƙirga kuɗi

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya umurci bankuna da sauran cibiyoyin hadahadar kuɗi cewa su kulle dukkan asusu, mu’amaloli da kadarorin waɗansu mutum shida da kamfanoni huɗu na hahahadar canjin kuɗi, wato ‘Bureau De Change’ (BDC) da aka sanya cikin jerin masu hannu wajen tallafa wa ta’addanci.

Wannan umarnin gaggawa ya biyo bayan takunkumin da gwamnatin Amurka ta ƙaƙaba wa Mukhtar Muhammad, wani ɗan canji da ke Legas, da wasu kamfanoni uku da ake zargin suna ƙarƙashin ikon sa.

CBN ya fitar da umarnin ne a cikin wata sanarwa mai lamba CMD/FCS/PUB/CIR/002/011 mai kwanan wata 24 ga Yuni, 2026, inda ya ce an sabunta jerin takunkumin wanda Nijeriya ta fara aiki da shi, tun ranar 18 ga Yuni, 2026, ya zama tilas ga dukkan cibiyoyin da ke ƙarƙashin kulawar sa.

Haka kuma CBN ya ce wannan matakin ya samo asali ne daga sabbin takunkumin da Kwamitin Takunkumin Najeriya (NIGSAC) da Ofishin Kula da Kadarorin Kasashen Waje na Ma’aikatar Baitul Malin Amurka (OFAC) suka fitar ƙarƙashin Dokar Ƙarfin Iko, wato ‘Executive Order 13224’.

Mutanen da aka saka cikin jerin waɗanda za a kulle wa kadarorin su sun haɗa da Muktar Muhammad Adamu, Babangida Muhammed, Adamu Hammajam, Abdullahi Umar Usman Ibrahim, Abubakar Adamu Chiroma, Yakubu Ogirima Ibrahim.

Haka kuma an sanya kamfanonin BDC guda huɗu da suka haɗa da Generation Currency Bureau De Change Limited, Manhattan Bureau De Change Limited, Nine to Nine Exchange Bureau De Change Limited da kuma Abbal Bako & Sons Bureau De Change Limited.

CBN ya umurci cibiyoyin hadahadar kuɗi cewa, “nan take su gaggauta ganowa tare da kulle duk wani kuɗi, kadara ko wata hanya ta tattalin arziki da ke ƙarƙashin mallaka ko ikon waɗanda aka sanya cikin jerin takunkumin.”

Wannan matakin ya zo ne bayan OFAC ta zargi Mukhtar Muhammad, wanda aka fi sani da Mukhtar Adamu Muhammad, da taimakawa wajen gudanar da hadahadar kuɗi da tura kuɗaɗe ga ƙungiyar ISWAP, reshen ƙungiyar ‘Islamic State’ da ke yammacin Afirka.

OFAC ta kuma ƙaƙaba wa kamfanonin Nine To Nine Exchange Bureau De Change Limited, Generation Currency Bureau De Change Limited, da Manhattan Bureau De Change Limited takunkumi, tana zargin an yi amfani da su wajen tura kuɗaɗen ga ƙungiyar.

Umarnin ya shafi duk wasu kamfanoni da ake da kashi 50 ko fiye, kai tsaye ko a fakaice na waɗanda aka sanya cikin jerin.

CBN ya ƙara gargaɗin cibiyoyin kuɗi da kada su samar da wani kuɗi, sabis na hadahadar kuɗi ko wata hanya ta tattalin arziki ga mutanen ko kamfanonin da aka sanya cikin jerin takunkumin.

Previous Post

ICPC ta gurfanar da El-Rufai, Jimi Lawal da kamfanoni biyar kan argin damfarar kwangilar CCTV ta Naira biliyan 8.68

Next Post

An kashe shugaban Miyetti Allah na Binuwai a kwanton ɓauna bayan taron sulhu

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
An kashe shugaban Miyetti Allah na Binuwai a kwanton ɓauna bayan taron sulhu

An kashe shugaban Miyetti Allah na Binuwai a kwanton ɓauna bayan taron sulhu

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!