Shari’ar tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Mal Nasir El-Rufai, kan zargin samun damar sauraren wata tattaunawar waya da ta shafi Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Tsaro (NSA), Nuhu Ribadu, ta ci gaba a yeu a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja.
A yayin zaman kotun, an kunna bidiyon hirar da El-Rufai ya yi da tashar talbijin ta Arise TV a ranar 13 ga Fabrairu, 2026.
Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) ya ruwaito cewa fitaccen lauya kuma mai fafutukar kare haƙƙin jama’a, Deji Adeyanju, wanda kotu ta gayyata ya bayar da shaida, ya bayyana a matsayin shaida ta biyu ga Hukumar Tsaro ta DSS a shari’ar.
A cikin shirin “Prime Time” na Arise TV, El-Rufai ya yi iƙirarin cewa wani mutum ya saurari wayar Nuhu Ribaɗu ba tare da izinin sa ba, lamarin da ya sa aka ji Ribadu yana ba jami’an tsaro umarnin kama shi..
El-Rufai ya ce: “Wani ya saurari wayar sa. Gwamnati tana sauraron kiran mu a kowane lokaci ba tare da umurnin kotu ba. Wani ya saurari wayar sa kuma ya sanar da mu cewa shi ne ya bayar da umurnin kama ni.”
A watan Afrilu ne aka gurfanar da tsohon gwamnan a gaban kotu bisa gyaran tuhume-tuhume guda biyar da suka shafi zargin samun damar sauraren tattaunawar wayar da ta shafi Nuhu Ribadu ba tare da izini ba.
Sai dai El-Rufai ya musanta dukkan tuhume-tuhumen.
Daga baya, a watan Mayu, kotun ta ba shi belin Naira miliyan 100.
Yayin da lauyan DSS, Oluwole Aladedoye, ke yi masa tambayoyi, Adeyanju ya shaida wa kotu cewa tun a ranar 12 ga Fabrairu, rahotanni sun fara yawo cewa ko dai za a kama El-Rufai ko kuma a gayyace shi domin amsa tambayoyi daga hukumomin tsaro.
Ya ce a lokacin ya fito fili yana kira ga El-Rufai da ya miƙa kan sa domin gudanar da bincike, yana mai jaddada cewa lamarin ba shi da alaƙa da siyasa.
Adeyanju ya kuma shaida wa kotun cewa shi ma an gayyace shi zuwa shirin Arise TV a ranar 13 ga Fabrairu, ranar da El-Rufai ya yi hirar sa.
Daga nan ne lauyan DSS ya nemi kotu ta amince a gabatar da bidiyon hirar El-Rufai a matsayin hujja, kuma kotun ta amince tare da kunna bidiyon a gaban kotu.
Bayan an kalli bidiyon, Adeyanju ya tabbatar da cewa wannan ita ce hirar da El-Rufai ya yi a ranar 13 ga Fabrairu.
Har ila yau, DSS ta gabatar da bidiyon hirar Adeyanju da mai gabatar da shirin, Charles Aniagolu, tare da takardar tabbatar da sahihancin sa.
An gabatar da faifan ajiya (flash drive) da takardar a matsayin hujjoji a kotu, inda aka yi musu rajista da lambobin “Shaidu H da H1”.
A cikin bidiyon da aka kunna, Aniagolu ya tambayi Adeyanju ko yana ganin da gaske gwamnati tana da niyyar kama El-Rufai.
Sai Adeyanju ya amsa da cewa idan da hakan ne manufar DSS, da tuni an kama El-Rufai a filin jirgin sama.
Ya ci gaba da cewa bayan shirin talabijin, ya samu wasiƙa daga DSS tana gayyatar sa zuwa ofishin su.
Adeyanju ya ce ya amsa gayyatar, duk da cewa cikin rashin jin daɗi ya rubuta bayanin sa a ofishin DSS.
Ya ƙara da cewa ya tabbatar wa da DSS cewa El-Rufai ne ya yi furucin da ya shafi sauraren tattaunawar wayar NSA.
Daga baya, lauyan El-Rufai, Paul Erokoro, ya yi masa tambayoyi.
Lokacin da aka tambaye shi ko ya ji El-Rufai yana cewa shi ne ya yi kutse ko ya saurari wayar wani, Adeyanju ya amsa da cewa: “Mun saurari tattaunawar su.”
Sai lauyan El-Rufai ya tambaya ko sauraron tattaunawa ta hanyar lasifikar waya, inda wasu suka ji abin da ake faɗa, za a iya ɗaukar sa a matsayin kutse ko satar sauraron waya.
Lauyan DSS ya yi ƙorafi kan irin tambayar, amma lauyan El-Rufai ya ce tambayar tana da muhimmanci wajen fayyace shaidar da aka bayar.
Adeyanju ya ce idan ya kasance a wajen da aka kunna tattaunawar waya ta lasifika, ba zai yi ƙarya game da hakan ba.
Erokoro ya sake tambayar sa ko zai yi mamaki idan NSA ya kasa gano na’urar da ake zargin an yi amfani da ita wajen kutse cikin tattaunawar wayar sa.
Adeyanju ya ce ba shi da wata masaniya ko ra’ayi a kan batun.
Shaidan ya bayyana cewa dalilin da ya sa yake kotu shi ne saboda an gayyace shi ta hanyar sammaci, kuma ba shi da zaɓi face ya halarta.
Mai Shari’a, Joyce Abdulmalik, ta ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 23 ga Yuni domin ci gaba da shari’ar.
Tun da farko a zaman kotun, Adeyanju ya gabatar da sammacin da aka aike masa domin halartar kotun da bayar da shaida, wanda kotun ta karɓa a matsayin hujja.







