• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Wednesday, September 30, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Halin da ‘yan Nijeriya suke ciki a yau ya fi na 2023 kyau – Omokri 

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
June 21, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Halin da ‘yan Nijeriya suke ciki a yau ya fi na 2023 kyau – Omokri 
Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Tsohon mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kuma Jakaden Nijeriya da aka naɗa zuwa ƙasar Meziko, Reno Omokri, ya kare ayyukan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana cewa tattalin arzikin Nijeriya ya fi ƙarfi a yanzu idan aka kwatanta shi da lokacin da shugaban ya hau mulki a shekarar 2023.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, Omokri ya kawo wasu alƙaluman tattalin arziki da shirye-shiryen gwamnati waɗanda ya ce sun nuna cigaba a tattalin arzikin ƙasar da kuma walwalar al’ummar Nijeriya.

A cewar sa, hauhawar farashin kayayyaki a Nijeriya, wadda take kashi 23 cikin ɗari kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki, ta ragu zuwa kashi 15.9 cikin ɗari a halin yanzu. Haka kuma, ya ce mafi ƙarancin albashi a ƙasar nan ya tashi daga N30,000 zuwa N70,000 a ƙarƙashin gwamnatin Tinubu.

Omokri ya ƙara da cewa kuɗaɗen da ake raba wa jihohi da ƙananan hukumomi duk wata ta hannun Kwamitin Rabon Kuɗi ga Asusu na Tarayya (FAAC) sun ƙaru sosai.

Ya ce, “Kafin Shugaba Tinubu ya hau mulki, FAAC na raba kimanin naira biliyan 700 a duk wata ga jihohi da ƙananan hukumomi. A yau kuwa, adadin ya kai kusan naira tiriliyan 2.1 a wata.”

Ya bayyana cewa wannan ƙarin kuɗin da ake rabawa ya inganta ƙarfin tattalin arzikin gwamnatocin jihohi, yana mai cewa yayin da jihohi da dama suka sha fama da biyan albashi a shekarar 2022, a yanzu dukkan jihohin ƙasar nan suna iya biyan albashin ma’aikatan su.

Jakaden da aka naɗa ya kuma yi magana kan ajiyar kuɗaɗen ƙasar nan a ƙasashen waje, inda ya ce sun kai dala biliyan 51.04, wanda ya bayyana a matsayin mafi girman adadin da aka samu cikin shekaru 17 da suka gabata.

A ɓangaren ilimi kuwa, Omokri ya yaba da aikin Hukumar Bada Lamuni ga Ɗalibai (NELFUND), yana mai cewa kusan kashi ɗaya bisa uku na ɗaliban jami’o’in Nijeriya su miliyan 3.1 sun amfana da tsarin bashin karatu da gwamnatin Tinubu ta ƙaddamar.

Ya kuma yi nuni da kwanciyar hankali da aka samu a jami’o’in ƙasar nan, inda ya ce cikin shekaru uku da suka gabata ba a samu yajin aiki na ƙasa baki ɗaya daga Ƙungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU) ba.

Ya ce, “A wannan gwamnati, kwas na shekaru huɗu yana ci gaba da kasancewa kwas na shekaru huɗu.”

Omokri ya kuma yaba da ayyukan gine-ginen manyan hanyoyi da gwamnatin ke yi, yana mai ambaton ayyukan tituna kamar Babban Titin Bakin Teku na Legas zuwa Kalaba, Babban Titin Illela zuwa Sakkwato zuwa Badagiri da Hanyar da ta yankin Sahara a matsayin hujjojin ƙoƙarin gwamnati na inganta hanyoyin sufuri da haɗa sassa daban-daban na ƙasar nan.

Har ila yau, ya yi nuni da cewa Nijeriya ta sauya daga kasancewa ƙasa mafi yawan shigo da man fetur da aka tace a Afrika a shekarar 2022 zuwa zama mafi yawan mai fitar da irin wannan man a yankin Yammacin Afrika.

A cewar sa, tattalin arzikin ƙasar ya samu cigaban GDP da kuma rarar ciniki a jere har tsawon kwata 12, abin da ya taimaka wajen ƙara ƙarfin masana’antun cikin gida.

Omokri ya buƙaci ‘yan Nijeriya da su yi la’akari da cigaban ƙasar bisa ga alƙaluman tattalin arziki da abubuwan da ake gani a fili.

Ya ce, “Ina kira ga ‘yan Nijeriya da su sanya al’amurra a ma’aunin su na gaskiya, kuma kada su bari masu yaɗa bayanan da ba su da tushe su ruɗe su. Babu shakka, Nijeriya ta fi yadda take a yau idan aka kwatanta ta da shekarar 2023.”

Wannan furuci nasa yana zuwa ne a yayin da ake ci gaba da muhawara a tsakanin al’umma kan tasirin sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin Tinubu ta aiwatar, musamman dangane da tsadar rayuwa da kuma walwalar ‘yan Nijeriya baki ɗaya.

Tags: MexicoReno OmokriShugaba Bola Ahmed Tinubutattalin arziki
Previous Post

Gwamnatin Tarayya ta raba buhunan taki 100,800 ga manoma 25,200 a Arewa-maso-yamma

Next Post

An haska bidiyon hirar El-Rufai kan zargin satar sauraren wayar Ribaɗu a kotu yayin da Deji Adeyanju ya ba DSS hujja

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
ICPC ta ƙalubalanci sabuwar buƙatar beli da El-Rufai ya gabatar yayin da kotu ta ɗage sauraron ƙarar zuwa 13 ga Mayu

An haska bidiyon hirar El-Rufai kan zargin satar sauraren wayar Ribaɗu a kotu yayin da Deji Adeyanju ya ba DSS hujja

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!