• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Labarai

Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da FreeTV a matsayin tashar talbijin dijital ta ƙasa kyauta

Fati Abdul by Fati Abdul
June 16, 2026
in Labarai
A A
0
Gwamnatin Tarayya za ta ƙaddamar da FreeTV a matsayin tashar talbijin dijital ta ƙasa kyauta
Darakta Janar na Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye ta Ƙasa (NBC), Charles Ebuebu

Darakta Janar na Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye ta Ƙasa (NBC), Charles Ebuebu

Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirin ta na ƙaddamar da FreeTV, wata tashar talbijin ta dijital ta ƙasa da za a kalla ba tare da biyan kuɗin wata-wata ba, a wani ɓangare na ƙoƙarin ta na faɗaɗa damar samun bayanai, nishaɗi da shirye-shiryen ilimi ga ‘yan Nijeriya.

An tsara ƙaddamar da wannan dandali a ranar 17 ga Yuni 2026, kuma yana daga cikin manyan shirye-shiryen Digital Switch-Over (DSO) da Nijeriya take aiwatarwa domin sauya tsarin watsa shirye-shirye gaba ɗaya daga analog zuwa dijital.

A cikin wata sanarwa da gwamnatin ta fitar yau Laraba, ta ce FreeTV zai bai wa ‘yan Nijeriya damar kallon tashoshin talbijin na dijital sama da 100, waɗanda suka haɗa da labarai, wasanni, finafinai, kiɗa, shirye-shiryen ilimi, shirye-shiryen yara da kuma shirye-shiryen da ake watsawa cikin harsunan gida.

Gwamnatin ta ce an ƙirƙiri wannan tsari ne domin ƙara haɗa kowa da kowa cikin harkokin sadarwa, samar da damarmakin tattalin arziki, bunƙasa shirye-shiryen cikin gida da tabbatar da cewa dukkan ‘yan ƙasa, ba tare da la’akari da inda suke zaune ko matsayin su na tattalin arziki ba, sun amfana daga sauyin fasahar dijital da ƙasar ke yi.

A ƙarƙashin wannan sabon tsari, masu kallo za su iya samun tashoshin talbijin na ƙasa, yankuna da jihohi ta hanyar tauraron ɗan’adam (satalayit), hanyoyin watsa shirye-shirye na ƙasa da kuma manhajar wayar salula ta FreeTV.

Ana sa ran wannan sabis ɗin zai kai ga gidaje a manyan birane, ƙananan garuruwa da yankunan karkara, har ma da wuraren da ba su samu cikakken sabis ba a farkon matakan sauyin tsarin talbijin na dijital a Nijeriya.

Jami’an gwamnati sun jaddada cewa ba lallai ne sai ‘yan Nijeriya sun sayi sababbin talbijin ba domin cin gajiyar wannan sabis ɗin. Talbijin ɗin da ake amfani da su a yanzu za su ci gaba da aiki idan suna da na’urorin DVB-T2 ko DVB-S2 masu dacewa, yayin da gidajen da tuni suke da na’urorin free-to-air masu dacewa ba za su buƙaci ƙarin kayan aiki ba.

Da yake magana gabanin ƙaddamar da shirin, Darakta Janar na Hukumar Kula da Watsa Shirye-shirye ta Ƙasa (NBC), Charles Ebuebu, ya bayyana FreeTV a matsayin wani gagarumin shiri na sauyi wanda ya yi daidai da manufar Sabuwar Fata (Renewed Hope) ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce: “FreeTV yana da alaƙa kai-tsaye da hangen nesa na Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Sabuwar Fata, wadda ke da manufar faɗaɗa damar samun ayyuka, samar da damarmaki da kuma tabbatar da cewa kowane ɗan Nijeriya, ko da kuwa inda yake ko matsayin sa na tattalin arziki, zai amfana daga tattalin arzikin dijital.”

Ya ƙara da cewa, “Ta hanyar FreeTV, iyalai a faɗin Nijeriya za su iya kallon ingantattun shirye-shiryen talbijin na dijital ba tare da biyan kuɗin wata-wata ba, yayin da masu shirya finafinai da shirye-shirye, ƙwararrun ma’aikatan fasaha da matasa masu ƙirƙire-ƙirƙire za su samu sababbin dandamali da kuma sababbin guraben ayyukan yi.”

Baya ga samar da talbijin kyauta, gwamnatin ta ce wannan shiri zai taimaka wajen bunƙasa masana’antar ƙere-ƙere da watsa shirye-shirye ta Nijeriya ta hanyar samar da ayyukan yi a fannoni daban-daban na harkokin yaɗa labarai.

Domin tallafa wa samar da shirye-shirye da ƙarfafa abubuwan cikin gida, za a kafa cibiyoyin samar da shirye-shirye a yankuna daban-daban da suka haɗa da Legas, Abuja, Fatakwal, Inugu, Kano da Benin. Ana sa ran cibiyoyin za su samar da ayyukan yi ga masu shirya shirye-shirye, masu gyaran bidiyo, masu ɗaukar hoto, injiniyoyin sauti, ƙwararrun ma’aikatan fasaha da sauran masu sana’o’in ƙirƙire-ƙirƙire.

A halin yanzu, Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada cewa ranar 31 ga Disamba 2028 ita ce ranar ƙarshe da Nijeriya za ta dakatar da tsarin analog gaba ɗaya, tare da shawartar ‘yan ƙasa da su tabbatar da cewa na’urorin su suna dacewa da tsarin, sannan su sauke manhajar FreeTV domin shiryawa ga sauyin.

Tags: Charles EbuebuDigital Switch-Over (DSO)FreeTVNBC
Previous Post

Yadda sojoji suka ceto matar mariganyi Janar Rabe Abubakar daga hannun ‘yan bindiga

Next Post

Sojoji sun lallasa ‘yan ta’addan Lakurawa, sun ƙwace makamai da bamabaman su a Kebbi

Related Posts

Abin da ya sa na fice daga NNPP – Gwamnan Kano
Labarai

Gwamnatin Kano ta hana hawan dawakai da hawan Durbar na sarakuna saboda dalilan tsaro

September 27, 2026
Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta
Labarai

Muhimman abubuwan da Tinubu ya gabatar a zauren Majalisar Ɗinkin Duniya, waɗanda mataimakin sa Kashim Shettima ya karanta

September 25, 2026
Kotu ta amince wa ICPC ta binciki na’urorin da aka ƙwato daga gidan El-Rufa’i
Tsaro

Cewar: El-Rufai Na koyi darussa daga shirun da abokan hulɗa ta suka yi kan halin da nake ciki

September 24, 2026
Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96
Labarai

Nijeriya ta sake jaddada ƙudirin ta na ƙarfafa hulɗa da Saudiyya yayin da Masarautar ke bikin cika shekaru 96

September 24, 2026
Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya
Labarai

Shettima ya wakilci Tinubu a taron Majalisar Ɗinkin Duniya

September 22, 2026
An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya
Tsaro

An sake cafke dillalin miyagun ƙwayoyi ɗan Nijeriya bayan ya tsere daga gidan yari a Laberiya

September 21, 2026
Next Post
Sojoji sun lallasa ‘yan ta’addan Lakurawa, sun ƙwace makamai da bamabaman su a Kebbi

Sojoji sun lallasa 'yan ta'addan Lakurawa, sun ƙwace makamai da bamabaman su a Kebbi

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!