Dakarun Rundunar Sojin Nijeriya ta Birged ta 17 a yau sun ceto Hajiya Fatima Abubakar, matar marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, daga hannun ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da ita.
Majiyoyin soji sun faɗi yadda aka gudanar da aikin ceton a ƙauyen Tunga, inda dakarun suka gano maɓoyar masu garkuwa da mutanen tare da kai samame a yayin wani samamen tsaro da suke yi.
A cewar majiyoyin, ‘yan bindigar sun buɗe wa dakarun wuta yayin da sojojin suke matsowa kusa da wurin da suke. A yayin musayar wutar, an ruwaito cewa masu garkuwar sun harbi Hajiya Fatima kafin su tsere lokacin da suka ga dakarun suna ci gaba da matsowa.
Nan take dakarun suka tabbatar da tsaron yankin, suka ceto matar tare da ba ta agajin gaggawa kafin a garzaya da ita zuwa asibiti domin samun kulawar likitoci.

Mahukuntan soji sun tabbatar da cewa Hajiya Fatima Abubakar ta samu raunukan harbin bindiga kuma tana zubar da jini a lokacin da aka ceto ta. A halin yanzu tana karɓar magani, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin kamo waɗanda suka tsere.
Ceton nata ya zo ne kwanaki kaɗan bayan binne marigayi Manjo Janar Rabe Abubakar, wanda ya rasu yana hannun masu garkuwa da mutane bayan sun yi garkuwa da shi. Mutuwar sa ta jawo martani da Allah-wadai daga sassa daban-daban na ƙasar nan tare da sake tayar da hankalin jama’a kan matsalar tsaro a wasu yankunan Arewacin Nijeriya.
Bayan rasuwar marigayin, Rundunar Haɗin Gwiwa ta Hedikwatar Tsaro a Arewa maso Yamma ƙarƙashin Operation Fansan Yamma ta ƙaddamar da wani gagarumin farmaki kan ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga a Jihar Katsina.
Farmakin, wanda aka sanya wa suna Operation Clean Sweep III, ya fara ne a ranar 14 ga Yuni, 2026, inda aka mayar da hankali kan masu aikata laifuka da ke aiki a Ƙaramar Hukumar Matazu da maƙwabtan ta.
A cewar sojojin, manufar farmakin ita ce gano tare da kawar da waɗanda ke da hannu a harin, rushe hanyoyin sadarwa da cibiyoyin masu aikata laifuka, da kuma dawo da zaman lafiya da tsaro a yankunan da abin ya shafa.







