Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙaddamar da sababbin gidaje guda 10 na alƙalan Kotun Ɗaukaka Ƙara a Katampe, Abuja, inda ya sake jaddada ƙudirin gwamnatin sa na ƙarfafa ɓangaren shari’a da tabbatar da ‘yancin sa.
Shugaban, wanda Ministan Shari’a kuma Babban Lauyan Nijeriya, Lateef Fagbemi, ya wakilta, ya ce aikin wani muhimmin zuba jari ne wajen tabbatar da doka da inganta dimokiraɗiyya.
Ya bayyana cewa ingantaccen tsarin shari’a ba wai yana buƙatar kulawa da dokoki da alƙalai kaɗai ba, har ma da ababen more rayuwa da muhalli mai kyau.

Tinubu ya ce samar da gidaje masu tsaro da inganci ga alƙalai zai ƙara musu ƙwarin gwiwa da inganta aikin shari’a, yana mai jaddada cewa jin daɗin su zuba jari ne ga ƙasa baki ɗaya.
Ya buƙaci gwamnatocin jihohi da su yi koyi da Gwamnatin Tarayya ta hanyar ƙara zuba jari a ɓangaren aikin shari’a, yana mai cewa nauyin tallafa wa kotuna ba na Gwamnatin Tarayya kaɗai ba ne.
A nasa ɓangaren, Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce samar da irin waɗannan ababen more rayuwa yana kara ƙarfafa ‘yancin ɓangaren shari’a ne, ba rage shi ba.
Shugabar Kotun Ɗaukaka Ƙara, Mai shari’a Monica Dongban-Mensem, ta bayyana aikin a matsayin babban cigaba wajen samar da ingantaccen muhalli ga alƙalai, tana mai cewa hakan zai taimaka wajen inganta aikin shari’a da kare martabar ɓangaren.
An ƙaddamar da aikin ne kwana ɗaya bayan buɗe sabon ginin Kotun Ɗaukaka Ƙara a Abuja, wanda ke nuna yadda gwamnati ke mai da hankali kan bunƙasa ɓangaren shari’a.








