Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana matuƙar alhinin sa kan rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya, wanda ya rasu yayin da yake tsare a hannun ’yan ta’adda a Jihar Katsina.
A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar, Tinubu ya ce ya yi matuƙar kaɗuwa da mutuwar tsohon jami’in sojan, tare da miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan sa da suka yi rashin.
Marigayi Abubakar, wanda ya kasance babban jami’in soja kuma ya yi ritaya bayan gagarumar hidima da ya yi wa Rundunar Sojojin Najeriya, tare da matar sa da direban suna kan hanyar su ta zuwa garin su ne lokacin da wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi.
An tabbatar da rasuwar sa ne a ranar Asabar, yayin da matar sa ke ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwar.
Shugaban Ƙasar ya jajanta wa iyalan marigayin, musamman matar sa da har yanzu take tsare a hannun masu garkuwar.
Haka kuma ya miƙa ta’aziyyar sa ga Gwamnatin Jihar Katsina da kuma Rundunar Sojojin Najeriya.
Tinubu ya sake jaddada matsayar gwamnatin sa cewa ba za ta taɓa tattaunawa ko yin sulhu da ’yan ta’adda ba, kuma ba za ta amince da buƙatar sakin wasu masu laifi da ke tsare domin musanya su da waɗanda aka yi garkuwa da su ba.
Ya ce: “Ko da yake ’yan ta’addar sun aikata abu mafi muni da za su iya yi, ya kamata su sani cewa gwamnati ba za ta taɓa lanƙwasawa ga buƙatar su ta a saki ’yan ƙungiyar su da hukumomin tsaro ke tsare da su ba.”
Yayin da yake sake jaddada kalaman da ya yi a bikin Ranar Dimokiraɗiyya ta 12 ga Yuni, Shugaban Ƙasar ya yi gargaɗi ga ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci da su miƙa wuya ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin ikon ƙasar nan.
Ya ce: “’Yan bindiga, masu garkuwa da mutane da masu ɗaukar nauyin ta’addanci su miƙa wuya yanzu ko kuma su fuskanci cikakken ƙarfin Jamhuriyar Tarayyar Nijeriya. Wannan damar miƙa wuya ba za ta kasance a buɗe har abada ba, kuma ba za a nuna jinƙai ga waɗanda suka mayar da jinin ’yan Nijeriya sana’a ba.”
Shugaban Ƙasar ya buƙaci ’yan Nijeriya da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai tare da yin imani da cewa ƙasar nan za ta yi nasara a kan matsalar rashin tsaro.
Ya ce: “A matsayin mu na ’yan Nijeriya, dole ne mu kasance tsintsiya maɗaurin ki ɗaya, kuma mu tabbatar wa da kan mu cewa maƙiyan ƙasar mu ba da jimawa ba za su zama tarihi. Za mu yi nasara a kan ta’addanci kuma mu ci gaba da gina ƙasa mai wadata.”
Da yake bayyana rasuwar Janar Abubakar a matsayin wani muhimmin darasi a yaƙin da ƙasar take yi da ta’addanci da tayar da ƙayar baya, Tinubu ya jaddada cewa dole ne a riƙa kallon ’yan ta’adda a matsayin maƙiyan ƙasa, kuma kada a taɓa yi masu wani rangwame.
Ya ƙara da cewa: “Ya kamata rasuwar Janar Abubakar ta zama wani muhimmin mataki a yaƙin mu da ’yan ta’adda da masu tayar da ƙayar baya, wanda zai ƙara tabbatar mana da cewa ba za mu taɓa tattaunawa da su ko yin sulhu da su ta kowace hanya ba. Dole ne mu ci gaba da ɗaukar su a matsayin manyan maƙiyan ƙasar mu, waɗanda bai kamata a taɓa sassauta masu ba.”
Rasuwar Janar Abubakar ta sake tayar da damuwa kan ƙara tsananta barazanar da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane ke haifarwa a wasu sassan Arewacin Nijeriya, musamman a Jihar Katsina, inda hare-hare kan matafiya da al’ummomin karkara suke ci gaba duk da matakan tsaro da ake ɗauka.






