Manjo Janar Abubakar Rabe (mai ritaya), wanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da shi a Jihar Katsina daidai makonni biyu da suka gabata yayin da yake tafiya tare da matar sa zuwa wani bikin aure, ya rasu a hannun masu garkuwar.
Gwamnatin Jihar Katsina ta tabbatar da mutuwar tsohon jami’in soja a yau Asabar, inda ta bayyana hakan a matsayin babban rashi ba ga iyalan sa da jihar kaɗai ba, har ma da ƙasa baki ɗaya.
An yi garkuwa da Rabe da matar sa ne a yankin Matazu na Jihar Katsina yayin da suke kan hanyar su ta zuwa bikin aure. Tun bayan sace su, hukumomin tsaro da gwamnatin jihar sun ƙara ƙaimi wajen ƙoƙarin tabbatar da an kuɓutar da su.
Kafin bayyanar labarin mutuwar sa, an gan shi a wani faifan bidiyo da ya bazu sosai a kafafen sada zumunta, wanda masu garkuwar suka fitar suna neman a saki wasu ’yan bindiga da ake tsare da su tare da mayar musu da dabbobin da aka ƙwace a matsayin sharaɗin sakin ma’auratan.
A cikin bidiyon mai tsawon minti huɗu da daƙiƙa biyu, an ga Rabe da matar sa a tsaye suna isar da buƙatun masu garkuwar.
A cikin bidiyon, matar tsohon janar ɗin ta roƙi hukumomi da su saki wasu ’yan bindiga uku da ta bayyana sunayen su da Sani, Aminu da Nasiru. A cewar ta, an kama biyu daga cikin su ne a Jiƙamshi, yayin da aka kama na uku a Jihar Kano.
Ta kuma roƙi Gwamnatin Jihar Katsina da shugabannin ƙananan hukumomi biyar da su taimaka wajen cika buƙatun masu garkuwar domin a samu ’yancin su.
Tsohon jami’in sojan, wanda ya yi magana kaɗan a cikin bidiyon, ya yi kira da a ƙara ƙoƙarin samar da zaman lafiya, yana mai cewa masu garkuwar sun nuna sha’awar tattaunawa da zaman tare cikin lumana.
Sai dai fata ta ganin an sake shi ta rushe a ranar Asabar lokacin da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida na Jihar Katsina, Nasiru Mu’azu, ya bayyana cewa tsohon janar ɗin ya rasu yayin da yake hannun masu garkuwa da shi.
A cikin wata sanarwa, Mu’azu ya ce gwamnatin jihar ta karɓi labarin cikin matuƙar baƙin ciki da jimami.
Sanarwar ta ce: “Gwamnatin Jihar Katsina, cikin alhini da babban jimami, tana ba da sanar da al’umma rasuwar Manjo Janar Rabe Abubakar mai ritaya.
“Cikin baƙin ciki mai tsanani muke tabbatar da mutuwar janar ɗin yayin da yake hannun ’yan bindiga. Duk da ƙoƙarin da gwamnatin jihar da hukumomin tsaro daban-daban suka yi ba dare ba rana domin tabbatar da an kuɓutar da shi lafiya, lamarin ya ƙare cikin wannan mummunan yanayi.”
A cewar kwamishinan, tsohon janar ɗin ya mutu ne sakamakon matsalolin rashin lafiya da suka shafi ciwon sukari da hawan jini yayin da yake tsare a hannun masu garkuwar.
“Marigayin ya rasu ne sakamakon matsalolin da suka taso daga ciwon sukari da hawan jini,” inji sanarwar.
Gwamnatin ta bayyana lamarin a matsayin babban rashi ga ƙasar nan baki ɗaya.
“Sace shi da kuma mutuwar sa daga baya ba rashi ba ne ga iyalan sa da Jihar Katsina kaɗai, babban rashi ne ga Nijeriya gaba ɗaya.”
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Raɗɗa, shi ma ya miƙa ta’aziyyar sa ga iyalan marigayin da kuma ’yan Nijeriya baki ɗaya.
A cewar sanarwar, gwamnan ya bayyana wannan ibtila’i a matsayin wani baƙin lokaci da kuma tunatarwa kan buƙatar ɗaukar matakai masu ƙarfi da haɗin gwiwa wajen yaƙi da ayyukan ta’addanci da laifuffuka a cikin al’umma.
“Mai Girma Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, CON, yana miƙa ta’aziyyar sa ta musamman ga iyalan marigayin janar ɗin da kuma ƙasar baki ɗaya.
“Gwamnan ya bayyana wannan lamari a matsayin ‘wani baƙin lokaci’ tare da jaddada cewa ya zama dole a haɗa kai da ƙara ƙaimi wajen yaƙi da miyagun masu tayar da zaune tsaye da ke barazana ga zaman lafiyar al’ummomin mu.”
Gwamnatin ta kuma yi addu’ar Allah Ya jiƙan sa tare da bai wa iyalan sa haƙurin jure wannan babban rashi.
“Tunani da addu’o’in mu suna tare da iyalan da suka yi wannan babban rashi a wannan lokaci mai wuya. Allah Ya gafarta wa marigayi Manjo Janar Rabe Abdulƙadir mai ritaya, Ya sa Aljannar Firdausi ce makomar sa.”
Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, babu tabbas kan halin da matar marigayin take ciki, wadda aka yi garkuwa da ita tare da shi.
Har yanzu gwamnatin jihar ba ta fayyace ko an sake ta ko kuma tana ci gaba da kasancewa a hannun masu garkuwa da mutane ba.







