Ministan Tsaro, Janar Christopher Gwabin Musa (mai ritaya), ya yi kira ga ‘yan Nijeriya masu fasahar ƙirƙire-ƙirƙire, sababbin kamfanonin farawa, da masu bincike da su karkata ƙwarewar su wajen samar da hanyoyin magance matsalolin tsaron ƙasa da aka samar a cikin gida.
Da yake jawabi a Taron Omniverse Africa 3.0 da aka gudanar a Legas, Musa ya ce tsaron ƙasa a ƙarni na 21 ba zai iya ci gaba da dogaro da kayan yaƙi na gargajiya kaɗai ba.
Yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi kan taken, “Dokar 70/30: Dalilin da ya sa manufofin tsaro da ƙirƙire-ƙirƙire na Nijeriya suke zama aiki guda na ƙasa,” ya jaddada buƙatar Nijeriya ta sauya daga mai amfani da fasahar tsaro zuwa mai ƙera ta.
Ministan ya ce: “Makomar gaba tana buƙatar mu haɗa jarumtaka da fasaha, hangen nesa, ƙarfin masana’antu, da ƙirƙire-ƙirƙire. Dole ne mu kare ƙasa a yau, amma kuma dole ne mu gina ƙwarewar da za ta kare ƙasar a gobe.”

Musa ya bayyana cewa Ma’aikatar Tsaro na sake fasalin manufofin ta, hanyoyin saye da samar da kayan aiki, da kuma horaswa domin bai wa fannoni kamar na’urorin da ba sa buƙatar matuƙi da na’urorin mutum-mutumi (robotics), fasahohin sa ido, tsaron yanar gizo da juriyar tsarin sadarwa, hanyoyin sadarwa masu tsaro, tsarin tafiyar da fasahar basirar zamani (AI), kayan yanke shawara da ke amfani da bayanai, da kuma cigaban masana’antun cikin gida fifiko.
Ya danganta wannan yunƙuri da Ajandar Sabunta Fata (Renewed Hope Agenda) ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta bunƙasa masana’antu, yana mai cewa manufar sauye-sauyen da ake aiwatarwa a Hukumar Masana’antun Tsaro ta Nijeriya (DICON) ita ce samar da yanayin da zuba jari a fannin tsaro zai haifar da bunƙasar tattalin arziki, ayyukan yi masu amfani da fasaha, binciken jami’o’i, da sababbin kasuwanni na kasuwanci.
Ministan ya kuma ƙaddamar da shirin Defence Futures Lab Pathway, wani taro na musamman da kamfanin Kryterion ya shirya domin ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin sojoji da masu fasaha.
Ya shaida wa mahalarta taron cewa wannan ba zaman sayen kayayyaki ba ne, illa wata dama ta bunƙasa ƙwarewa da tsara dabarun gaba.
Ya ce, “Wannan wata dama ce ta yin tunani kan gaba, inganta tsari, da kuma binciko hanyoyi masu amfani na ƙarfafa tsarin tsaro gaba ɗaya.”
Mataimakiya ta Musamman kan Yaɗa Labarai ga Ministan Tsaro, Leah Katung-Babatunde, ta bayyana a cikin wata sanarwar manema labarai cewa mahalarta zaman tattaunawar sun amince za su sake haɗuwa cikin watanni uku domin tantance cigaban da aka samu, duba sababbin ra’ayoyin fasaha da aka gabatar, da kuma daidaita matakan da dabarun gwamnatin tarayya na bunƙasa fasahar tsaro ta cikin gida.







