Yayin da aka fara jigilar mahajjatan Nijeriya zuwa gida daga ƙasar Saudiyya a yau, Hukumar Alhazai ta Ƙasa ta Nijeriya (NAHCON) ta buƙaci mahajjatan da su bi ƙa’idar nauyin kaya da aka amince da ita, wadda ta tanadi jakunkuna biyu na shiga jirgi masu nauyin kilo 23 kowacce, tare da jakar hannu guda ɗaya da ba za ta wuce kilo 8 ba.
Hukumar ta ce ba za a amince da jakunkunan hannu fiye da guda ɗaya ba.
An fara jigilar dawowar ne da tashin mahajjata 560 daga Jihar Nasarawa, wanda ya nuna fara matakin dawo da mahajjatan gida bayan sun shafe kusan kwanaki 30 a Saudiyya yayin gudanar da aikin Hajjin 2026.
A cikin wata sanarwar manema labarai, NAHCON ta bayyana cewa an tsara ƙarin jirage uku na dawo da mahajjata daga baya a yau.
Yayin da aka fara wannan mataki gadan-gadan, hukumar ta ce ya kamata mahajjata su sani cewa za a fara binciken kayan su sa’o’i 48 kafin ranar tashin su.
Sanarwar ta ce: “An tsara hakan ne domin mahajjata su samu kayan su cikin gaggawa da zarar sun isa Nijeriya. Bin waɗannan ƙa’idoji zai sauƙaƙa aikin bincike tare da hanzarta bai wa mahajjata izinin tafiya.”
Ta ƙara da cewa: “Haka kuma, ana tunatar da mahajjata kada su sanya ruwan Zamzam ko wasu abubuwan da aka haramta a cikin kayan su, domin za a ƙwace irin waɗannan abubuwa yayin bincike, lamarin da ka iya sa a buɗe ko a taɓa kayan su.
“Abubuwan da aka haramta sun haɗa da abubuwa masu saurin kamawa da wuta kamar ruwan kunna wuta, batirin lithium da na’urorin ajiyar wuta (power bank) idan an saka su a cikin kayan da aka miƙa don shiga jirgi, feshi (aerosol), ruwa mai yawa fiye da ƙa’ida, da kuma kayan kaifi da aka sanya a cikin jakar hannu.”
A wani labarin kuma, NAHCON ta yaba da haɗin kai, goyon baya da fahimtar da kamfanonin jiragen sama huɗu da aka amince da su suka nuna wajen fara aiki a kan lokaci, duk da tsadar man jiragen sama da ake sa ran za ta yi tasiri.
Hukumar ta tabbatar wa da kamfanonin jiragen saman cewa gwamnati na da niyyar taimakawa domin tabbatar da cewa ba su yi asara ba daga aikin jigilar mahajjatan.
A halin yanzu, Cibiyar Kula da Ayyuka ta NAHCON da ke Makkah ta fitar da jadawalin jigilar mahajjatan da za su dawo gida a yau.
Jadawalin ya nuna cewa jirgin MaxAir mai lamba NGL263 ya tashi daga Jiddah zuwa Abuja da ƙarfe 10:54 na safe ɗauke da mahajjata 560, waɗanda suka haɗa da 559 daga Jihar Nasarawa da kuma mutum 1 daga Jihar Katsina.
Jimillar mahajjatan da aka kwashe zuwa yanzu ta kai 1,546, yayin da adadin jiragen da suka yi jigilar ya kai 3.







