• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN zai rage yawan takardun naira da ke hannun jama’a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 nan da 2028

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 2, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
CBN zai rage yawan takardun naira da ke hannun jama’a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 nan da 2028

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Olayemi Cardoso, ya bayyana shirin rage yawan takardun kuɗaɗen da ake hadahada a hannun jama’a, daga kusan kashi 90 cikin 100 zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 nan da shekarar 2028.

Wannan gagarumin shiri dai wani ɓangare ne na ƙoƙarin bunƙasa tattalin arziki ta tsarin hadahadar zamani, wato dijital na ƙasa da kuma ƙarfafa tasirin manufofin kuɗi.

Cardoso ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a Abuja yayin ƙaddamar da Tsarin Biyan Kuɗi na Nijeriya 2028 (Nigeria Payments Systems Vision 2028, PSV 2028), wanda wata sabuwar manufa da aka tsara domin sabunta tsarin biyan kuɗi, faɗaɗa ƙasa haɗa jama’a cikin harkokin kuɗi, da kuma ƙarfafa amincewa da mu’amalolin dijital.

A taƙaice shiri domin ganin kusan kowane ɗan Nijeriya ya komawa tsarin hadahada ta asusun bankin sa kai-tsaye.

Sabon rahoton ƙididdigar kuɗi da lamuni na CBN dai ya tabbatar da cewa a yanzu haka kuɗin da ke yawo a hannun jama’a ya kai naira tiriliyan 5.65 a watan Afrilu 2026, yayin da naira tiriliyan 5.08 daga cikin wannan adadi ke wajen tsarin banki.

Wannan na nufin cewa kusan naira 90 daga cikin kowace naira 100 na takardun kuɗin da ke yawo a halin yanzu ba su shiga cikin bankuna.

Da yake nuna damuwa kan wannan yanayi, Cardoso ya ce CBN na da niyyar rage yawan kuɗaɗen da ke yawo a wajen hanyoyin kuɗi na hukuma cikin shekaru uku masu zuwa.

Ya ce, “Ina son ganin an rage kuɗaɗen da ke wajen tsarin banki zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 na kuɗin da ke yawo a hannun jama’a.”

Gwamnan CBN ya bayyana cewa rage dogaro da kuɗin takarda zai taimaka wajen inganta tasirin manufofin kuɗi, ƙara gaskiya a harkokin kuɗi, da kuma saurin sauya Nijeriya zuwa tsarin biyan kuɗi na zamani mai inganci.

Haka kuma Cardoso ya nuna damuwar sa kan yadda har yanzu ake ci gaba da dogaro da kuɗin takarda duk da saurin bunƙasar hanyoyin biyan kuɗi na zamani a faɗin ƙasar nan.

Yayin da yake tuna abin da ya gani a lokacin bikin Sallah da ya gabata, ya ce har yanzu ’yan kasuwa da dama ba su karɓar biyan kuɗi ta katin banki wato ATM, lamarin da ya nuna buƙatar ƙara gina amincewar jama’a ga tsarin biyan kuɗi na dijital.

Ya ce: “Ba na zargin su. Mu ne ya kamata mu zargi kan mu. Dole ne mu yi aiki sosai domin gina amincewa tare da tabbatar da cewa mutane sun yi imani cewa suna hulɗa da tsarin biyan kuɗi mai ƙarfi sannan kuma abin dogaro.”

Ya jaddada cewa gyaran tsarin biyan kuɗi ya kamata ya kawo sauyi mai amfani ga rayuwar talakawan Nijeriya, ba kawai ƙara yawan mu’amaloli ba.

Cardoso ya kuma bayyana wata manufa mai faɗi ta kaiwa kashi 95 cikin 100 na haɗa jama’a cikin harkokin kuɗi nan da shekarar 2028, daga kusan kashi 74 cikin 100 da ake da shi a halin yanzu. Hakan na nufin ana buƙatar ganin kowane ɗan Nijeriya yana da asusun banki, kuma ya kasance ta hanyar asusun yake hadahada da mu’amalar kuɗaɗen sa.

Bayanan cibiyar EFInA sun nuna cewa haɗa jama’a cikin harkokin kuɗi ya ƙaru daga kashi 68 cikin 100 a shekarar 2020 zuwa kashi 74 cikin 100 a shekarar 2023, sakamakon faɗaɗar hadahadar kuɗi ta hanyar amfani da wayar hannu, fasahohin fintech da kuma cibiyoyin wakilan banki.

A cewar Cardoso, shirin zai sa ƙarin ’yan Nijeriya miliyan 50 su shiga cikin tsarin kuɗi na hukuma.

Ya ce “A shekarar 2023, adadi mai yawa na manyan ’yan Nijeriya sun samu damar amfani da ayyukan kuɗi. A ƙarƙashin ‘Vision 2028’, ina son ganin wannan ya kai kashi 95 cikin 100.

“Hakan na nufin ƙarin mata masu sana’a a kasuwanni, manoma da matasa miliyan 50 za su mallaki asusun banki ko walat na dijital a sunayen su, tare da lambar BVN da za ta kare su.”

Cardoso ya ce babban bankin yana kuma da burin rage damfarar biyan kuɗi ta dijital zuwa ƙasa da kashi 0.001 cikin 100 na jimillar mu’amaloli nan da shekarar 2028.

Ya ce za a cimma hakan ne ta hanyar ƙarfafa haɗin kai tsakanin tsarin La BVN, da kuma amfani da ƙirƙirar fasahar basirar zamani (AI) wajen gano damfara.

Daga nan sai ya ci gaba da cewa “kamata ya yi kuɗin jama’a su fi zama cikin aminci a tsarin dijital fiye da yadda suke ƙarƙashin katifa. Ƙarfin tsarin biyan kuɗi yana dogara ne da irin amincewar da mutane suke da shi.”

Gwamnan ya kuma bayyana irin damar da tsarin ‘Open Banking’ na Nijeriya ke da ita, yana mai cewa sama da manhajojin haɗin bayanai (APIs) 100 da aka ba lasisi suna nan domin tallafa wa ƙirƙire-ƙirƙire da kuma bunƙasar kamfanonin fintech masu gasa a matakin duniya.

An tsara ‘Payments System Vision 2028’ ne domin inganta ingancin biyan kuɗi, ƙarfafa juriyar tsarin, ƙarfafa ƙirƙire-ƙirƙire, faɗaɗa haɗa jama’a cikin harkokin kuɗi, da kuma zurfafa haɗin Nijeriya da tsarin biyan kuɗi na yankuna da na duniya.

Cardoso ya ce ingantaccen tsarin biyan kuɗi zai rage kuɗin gudanar da mu’amaloli, ƙara gaskiya, taimaka wa kasuwanci wajen shiga sabbin kasuwanni, tare da tallafa wa bunƙasar tattalin arziki.

Ya ce, “yayin da Gwamnatin Tarayya ke gina tituna, makarantu da asibitoci, dole ne mu ma mu gina hanyoyin da ba a gani da ido waɗanda ke motsa kuɗi.”

Da yake bayyana shirin a matsayin aikin ƙasa baki ɗaya, ya yi kira ga bankuna, kamfanonin fintech, masu tsara dokoki, masu samar da fasaha da abokan hulɗar ci gaba da su haɗa kai wajen tabbatar da cimma manufofin sa.

Ya ƙara da cewa: “Vision 2028 ba aikin gwamnati ba ne kaɗai. Aikin Nijeriya ne gaba ɗaya.”

Tun da farko, Daraktan Manufofin Tsarin Biyan Kuɗi na CBN, Musa Jimoh, ya ce sabuwar dabarar ta zama wajibi sakamakon saurin ci gaban fasaha da sauyin buƙatun masu amfani tun bayan ƙaddamar da tsarin farko na biyan kuɗi na Nijeriya a shekarar 2007.

Ya ce PSV 2028 zai ƙara faɗaɗa haɗa jama’a cikin harkokin kuɗi, inganta inganci, ƙarfafa amincewa da biyan kuɗi ta dijital, da kuma ƙara wa Nijeriya ƙarfin gasa a tattalin arzikin dijital na duniya.

Tags: CardosoCBNNigeria Payments Systems Vision 2028PSV 2028
Previous Post

CBN ya ƙara wa’adin cika ƙa’idoji da nisan zangon amfani da PoS

Next Post

An ɗauki masu tsaron daji a jihohi 10 na Arewa, ba a Oyo kaɗai ba, inji Abdulaziz Abdulaziz

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
An ɗauki masu tsaron daji a jihohi 10 na Arewa, ba a Oyo kaɗai ba, inji Abdulaziz Abdulaziz

An ɗauki masu tsaron daji a jihohi 10 na Arewa, ba a Oyo kaɗai ba, inji Abdulaziz Abdulaziz

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!