• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Tuesday, September 29, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN ya ƙara wa’adin cika ƙa’idoji da nisan zangon amfani da PoS

ASHAFA MURNAI BARKIYA by ASHAFA MURNAI BARKIYA
June 1, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Yadda asusun kuɗaɗen waje na Nijeriya zai cika maƙil, bayan CBN ya yi wa naira allurar ƙarin ƙarfin wujijjiga dala a tsakiyar kasuwa
Hedikwatar CBN a Abuja

Hedikwatar CBN a Abuja

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya ƙara wa’adin fara aiwatar da tsarin tantance wurin aiki wanda a Turance ake kira ‘geo-fencing’ na na’urorin PoS zuwa ranar 1 ga Agusta, 2026.

Wannan dai ya ƙunshi ƙara wa’adin cika ƙa’idoji da sharuɗɗan da CBN ya gindaya, tare kuma da ƙara faɗin nisan zangon da za a iya aiki da kowane PoS a faɗin Nijeriya.

CBN ya yi haka ne domin bai wa cibiyoyin kuɗi da masu samar da ayyukan biyan kuɗi ƙarin lokaci su cika sabon sharaɗin doka da aka kafa domin ƙarfafa sa-ido kan hanyoyin biyan kuɗi na zamani.

An bayyana wannan umarni ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar 29 ga Mayu, 2026, wato a ranar Juma’ar da ta gabata, wadda Daraktar Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi ta CBN, Rakiya Mohammed, ce ta sanya hannu a kan sanarwar.

An aika da sanarwar ne zuwa Bankunan Kasuwanci (DMBs), Bankunan Microfinance, Masu Gudanar da Hadahadar Kuɗi ta Kafafen Sadarwar Zamani (Mobile Money Operators), Kamfanonin Canjawa da Sarrafa Ma’amaloli, Masu Samar da Sabis na Na’urorin Biyan Kuɗi, Masu Samar da Hanyoyin Biyan Kuɗi, Super Agents da sauran masu lasisi a tsarin biyan kuɗi na Nijeriya.

Sanarwar ta bayyana cewa an sake duba jadawalin aiwatar da manufar ne bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki da kuma la’akari da ƙalubalen da suka taso wajen aiwatar da wata sanarwa da aka fitar a ranar 25 ga Agusta, 2025, wadda ta shafi sauyawa zuwa tsarin saƙonnin biyan kuɗi na ISO 20022 da kuma wajabta sanya bayanan wurin aiki ga dukkan na’urorin biyan kuɗi.

Idan ba a manta ba, tun a watan Agustan 2025 ne dai CBN ya umarci cewa dukkan na’urorin PoS a faɗin ƙasar nan su kasance an tantace nisan wuraren da za a iya amfani da su, cikin kwanaki 60, a matsayin wani mataki na rage damfara da ƙarfafa sa-ido kan harkokin biyan kuɗi na zamani.

A cikin sabon umarnin, CBN ya sanar da manyan sauye-sauye guda biyu.

Na farko, ya ƙara iyakar nisan da aka amince da domin amfani da kowace na’urar PoS daga mita 10 zuwa mita 70.

Sai na biyu kuma CBN ya ɗage ranar da za a fara tilasta bin dokar ta ‘geo-fencing’ zuwa ranar 1 ga Agusta, 2026.

Sanarwar ta ce: “An ƙara iyakar nisan amfani da PoS daga mita 10 zuwa mita 70.”

Ta kuma ƙara da cewa: “An tsawaita lokacin fara aiwatar da tsarin nisan amfani da na’urorin PoS zuwa ranar 1 ga Agusta, 2026.”

Tsarin ‘geo-fencing’ yana nufin cewa na’urar PoS za ta yi aiki ne kawai a wurin da aka amince, kuma aka danganta shi da ɗan kasuwa ko wakilin da ke amfani PoS ɗin.

An tsara wannan mataki ne domin inganta sa-ido kan ma’amaloli, rage amfani da hanyoyin biyan kuɗi ba bisa ƙa’ida ba, da kuma ƙarfafa sahihanci da tsaron tsarin biyan kuɗi na ƙasa.

CBN ya umurci dukkan cibiyoyin da abin ya shafa da su gabatar da hujjar cewa sun cika waɗannan ka’idoji kafin sabon wa’adin da aka sanya.

Sanarwar ta ce: “Dole ne a aika da hujjar bin waɗannan umarni zuwa ga Daraktan Sashen Kula da Tsarin Biyan Kuɗi ta hanyar adireshin imel paymentdata@cbn.gov.ng kafin ranar 31 ga Yuli, 2026.”

Har ila yau, darakta mai kula da harkokin ta umurci cibiyoyin kuɗi da su warware duk wata matsalar fasaha ko ta gudanarwa da suke fama da su, domin sauƙaƙa aiwatar da wannan manufa.

Sanarwar ta ce: “Ana buƙatar cibiyoyin kuɗi su magance dukkan matsalolin gudanarwa da suke da su cikin wa’adin da aka gindaya domin sauƙaƙa bin dokar.”

Ana sa ran wannan ƙarin wa’adi zai bai wa masu gudanar da ayyukan biyan kuɗi damar kammala inganta tsarin su, daidaita wuraren da na’urorin PoS suke aiki da sabbin ƙa’idojin CBN, tare da magance sauran matsalolin gudanarwa kafin fara aiwatar da dokar a watan Agusta.

Tags: CBNgeopencingPOSwa'adi
Previous Post

Al’ummar Kudancin Kaduna sun karrama Ministan Tsaro da sarautar Sarkin Yaƙi

Next Post

CBN zai rage yawan takardun naira da ke hannun jama’a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 nan da 2028

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Auto Draft
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
CBN zai rage yawan takardun naira da ke hannun jama’a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 nan da 2028

CBN zai rage yawan takardun naira da ke hannun jama'a zuwa ƙasa da kashi 40 cikin 100 nan da 2028

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!