Nijeriya ta samu ƙarin daraja daga kamfanin S&P Global Ratings, wanda hakan alamar ce mai nuna ƙaruwar amincewar da duniya ke ci gaba da yi wa kyawawan manufofin da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya shimfiɗa bisa turbar tattalin arzikin ƙasar.
Sabon ƙarin daraja da ɗaga martabar tattalin arzikin Nijeriya da kamfanin tantance ƙarfin tattalin arzikin ƙasashen duniya, wanda kamfani ne mai tantance daraja ko naƙasun manufofin kuɗi na duniya, S&P Global Ratings ya yi wa ƙasar nan a ranar 16 ga Mayu, ya ƙara tabbatar da cewa shirin gyaran tattalin arzikin ƙasar na samun karɓuwa daga waje, inda gyare-gyaren manufofin kuɗaɗe da kasuwar canjin kuɗaɗen waje suka zama manyan abubuwan da ke ƙara wa tattalin arzikin ƙasa ƙima a idon cibiyoyin duniya.
S&P ya ɗaga darajar dogon lokacin bashin Nijeriya daga matakin “B-” zuwa “B”, yana mai cewa yanayin tattalin arzikin ƙasar na ƙara inganta. Kamfanin ya danganta ƙarin darajar da bunƙasar tattalin arziki da kuma ingantuwar ma’aunin biyan kuɗaɗen ƙasashen waje, wanda ya samu goyon baya daga ƙarin yawan haƙo mai da tashin farashin sa, ƙaruwar tace yawan mai a cikin gida, da kuma sassauta tsarin canjin kuɗaɗen waje da aka fara a shekarar 2023.
S&P ya kuma bayyana cewa yana sa ran kuɗin shiga na kowane ɗan Nijeriya zai riƙa ƙaruwa da matsakaicin kaso 1.4 cikin ɗari a duk shekara har zuwa shekarar 2029, bayan da aka samu raguwar matsakaicin kaso 1 cikin ɗari a kowace shekara cikin shekaru goma da suka gabata.
Wannan sabon ƙarin darajar bai zo shi kaɗai ba. Ya biyo bayan jerin ƙarin darajoji da manyan kamfanonin tantance tattalin arziki na duniya suka yi wa Nijeriya.
Shi ma Kamfanin Fitch Ratings ya ɗaga darajar Nijeriya daga “B-” zuwa “B” a watan Afrilun 2025. Haka kuma Moody’s ya ɗaga darajar Nijeriya daga “Caa1” zuwa “B3” a watan Mayun 2025, yana danganta hakan da ingantuwar matsayin kuɗaɗen waje da kuma tsarin kasafin kuɗin ƙasar.
S&P ya sauya hasashen Nijeriya zuwa abu mai kyau a watan Nuwamban 2025 kafin wannan sabon ƙarin darajar a watan Mayun 2026, yayin da Fitch ya sake tabbatar da darajar Nijeriya a matsayin “B” a watan Afrilu 2026.
A dunƙule, waɗannan matakai na nuna wani babban sauyi mai bayyana cewa gyaran tattalin arzikin Nijeriya ya fara wuce matakin manufofin cikin gida zuwa samun amincewa daga cibiyoyin duniya akai-akai.
Su dai kamfanonin tantance darajar tattalin arziki na duniya, ba sanarwa kaɗai suke dubawa ba, suna kuma duba ko gyare-gyaren na bayyana a zahiri ta fuskar ma’aunin kuɗaɗen waje, juriyar kasafin gwamnati, ƙarfin ajiyar kuɗaɗen waje, amincewar kasuwa da kuma hasashen bunƙasar tattalin arziki na matsakaicin lokaci.
Rawar da CBN ke takawa ta fi bayyana a ɓangaren alamomin tattalin arzikin ƙasashen waje da ke ƙara wa Nijeriya ƙima. Gyare-gyaren kasuwar canjin kuɗaɗen waje da bankin ya aiwatar, biyan bashin kuɗaɗen waje da aka tara a baya, ƙara ajiyar kuɗaɗen waje da kuma matakan tabbatar da daidaiton kasuwa sun taimaka wajen magance wasu manyan matsalolin da suka taɓa rage ƙwarin gwiwar masu zuba jari. Waɗannan matsaloli sun haɗa da ƙarancin kuɗaɗen waje, rashin tabbas wajen samun dala, raunin ajiyar kuɗaɗen waje da matsin lamba wajen biyan buƙatun ƙasashen waje.
Ɗaya daga cikin manyan hujjojin da ke nuna ci gaban shi ne biyan bashin kuɗaɗen waje da aka tara. A watan Janairu 2025, Gwamnan CBN, Olayemi Cardoso ya sanar da cewa Gwamnatin Tarayya ta biya bashin canjin kuɗaɗen waje na dala biliyan 7 bayan wani bincike da ƙwararru masu binciken kuɗi suka gudanar. Wannan bashin na daga cikin manyan matsalolin da suka rage amincewar masu zuba jari saboda yana haifar da damuwa kan ko masu zuba jari da kamfanoni za su iya samun dala domin mayar da kudin su, biyan buƙatu da kuma tsara harkokin su na dogon lokaci.
Haka nan matsayin ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya ƙara ƙarfi sosai. Adadin ajiyar kuɗaɗen waje na haƙiƙa ya ƙaru zuwa dala biliyan 34.8 a ƙarshen shekarar 2025, daga dala biliyan 3.99 shekaru biyu da suka gabata. Jimillar ajiyar kuɗaɗen waje ya kuma karu daga dala biliyan 40.19 zuwa dala biliyan 45.71 cikin shekara guda, sannan ta ƙara hawa zuwa dala biliyan 50.45 a tsakiyar watan Fabrairun 2026, kamar yadda CBN ya bayyana.
CBN ya danganta wannan ci gaba da ƙarin ajiyar kuɗaɗen da ake samu daga mazauna ƙasashen waje, ƙara gaskiya wajen gudanarwa, kyakkyawan tsarin kula da ajiyar kuɗaɗen, ƙarin shigowar kuɗaɗen waje da kuma gyare-gyaren da aka yi domin dawo da amincewa a kasuwar canjin kuɗaɗe.
Matsayin biyan buƙatun ƙasashen waje na Nijeriya ma ya samu sauyi mai kyau. A shekarar 2024, ƙasar ta samu rarar kuɗaɗen biyan ƙasashen waje na dala biliyan 6.83, bayan giɓin dala biliyan 3.34 a shekarar 2023 da dala biliyan 3.32 a shekarar 2022.
Asusun hadahadar kasuwanci da na jarin waje sun nuna rarar dala biliyan 17.22, wanda ya samu goyon baya daga rarar cinikin kaya ta dala biliyan 13.17, yayin da jarin masu zuba jari na kasuwannin hadahadar kuɗi ya ninka fiye da sau biyu zuwa dala biliyan 13.35. Ajiyar kuɗaɗen waje ma ya ƙaru da dala biliyan 6 zuwa dala biliyan 40.19 a karshen shekarar 2024.
Waɗannan alamomi suna da muhimmanci saboda darajar tattalin arzikin ƙasa yana dogaro sosai kan ikon ƙasar wajen biyan buƙatun kasashen waje, jawo jarin waje, shawo kan matsaloli da kuma ci gaba da tabbatar da amincewa da manufofin ta.
Gyaran da CBN ya yi ba su da bambanci da sauran shirye-shiryen gyaran tattalin arzikin ƙasar; suna samar da tubalin ɓangaren kuɗaɗe da ƙasashen waje da ke bai wa sauran gyare-gyaren damar zama abin amincewa ga masu zuba jari, masu bayar da lamuni da cibiyoyin tantance darajar tattalin arziki.
Sabon ƙarin daraja daga kamfanin tantace ƙarfin tattalin arzikin ƙasashe na S&P ya sake jawo hankali kan alaƙar da ke tsakanin gyaran kasuwar canjin kuɗaɗe da amincewar ƙasashen waje. S&P ya bayyana cewa sassauta tsarin canjin kuɗaɗe na daga cikin abubuwan da suka taimaka wajen bunƙasar tattalin arziki da inganta matsayin biyan buƙatun ƙasashen waje.
Tun da farko shi ma kamfanin tantace ƙarfin tattalin arzikin ƙasashe na Moody’s ya bayyana irin wannan ra’ayi a ƙarin darajar da ya yi wa Nijeriya a watan Mayun 2025, inda ya ce gyare-gyaren tafiyar da kasuwar kuɗaɗen waje sun taimaka wajen inganta ma’aunin biyan kuɗaɗen ƙasashen waje da kuma ƙarfafa ajiyar kuɗaɗen waje na Babban Bankin Najeriya.
A cewar S&P, ingantuwar martabar tattalin arzikin Nijeriya na nuna wasu sauye-sauye na tsarin tattalin arziki, ciki har da ƙaruwar ƙarfin tace mai a cikin gida, wanda ya taimaka wajen bunƙasar tattalin arziki da inganta ma’aunin biyan kuɗaɗen ƙasashen waje. Kamfanin ya kuma bayyana cewa matsayin Nijeriya a matsayin babbar mai fitar da ɗanyen mai da kuma sabuwar mai samar da man fetur da aka tace a cikin gida ya sa ƙasar ba ta fuskantar wasu haɗurra a yankin kamar yadda wasu ƙasashe makamanta ke fuskanta.







