Binciken da Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya gudanar kwanan nan a masana’antu, ya tabbatar da cewa matsalar tsaro ce babban ƙalubalen da ke damun masu gudanar da hadahadar kasuwanci a Nijeriya.
‘Yan kasuwa a faɗin Nijeriya dai sun bayyana matsalar tsaro a matsayin babban ƙalubalen gudanar da harkokin su a watan Afrilu na shekarar 2026.
Sauran ƙalubalen da suka biyo bayan matsalar tsaro kuwa sun haɗa da haraji masu yawa, tsadar kuɗin ruwa, da kuma cajin bankuna, kamar yadda sabon rahoton Binciken Hasashen Kasuwanci na Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya nuna.
Rahoton ya bayyana cewa, “Amsoshin binciken watan Afrilu 2026 sun nuna cewa matsalar tsaro ke da kashi 74.1, sai yawan haraji ko haraji masu yawa ke da kaso 70.5, tsadar kuɗin ruwa ke na uku da kaso 67.4 na yawan waɗanda aka ji ta bakin su.
Daga nan kuma sai tsadar cajin bankuna mai kashi 62.8, da gasa 61.8 su ne manyan ƙalubalen kasuwanci guda biyar, wanda ke nuna cewa yanayin kasuwanci ya fi fuskantar matsin lamba daga haɗari da tsadar gudanarwa fiye da matsalolin ƙarancin buƙata.”
Babban bankin ya ƙara da cewa binciken ya nuna “akwai buƙatar inganta yanayin tsaro, samar da manufofin kuɗi masu sauƙi ga kasuwanci, da rage tsadar samun rance domin bunƙasa ayyukan kasuwanci da ƙarfafa amincewa.”
An gudanar da binciken daga ranar 6 zuwa 10 ga Afrilu, 2026, inda aka tattara bayanai daga kamfanoni 1,900 a fannoni daban-daban da suka haɗa da masana’antu, ayyuka, da noma, tare da samun kaso 99.4 cikin ɗari na masu amsa tambayoyin.
Duk da matsin lambar tsaro da tsadar gudanarwa, ’yan kasuwa sun ci gaba da nuna kyakkyawan fata kan tattalin arzikin ƙasa. Rahoton ya nuna cewa ma’aunin amincewar kasuwanci ya ci gaba da kasancewa a mataki mai kyau a watan Afrilu 2026, duk da cewa ya ragu idan aka kwatanta da watan da ya gabata.
Rahoton ya nuna cewa dukkan fannoni sun nuna kyakkyawan fata game da tattalin arziki, inda ɓangaren masana’antu ya fi nuna amincewa.
Masu amsa tambayoyin sun kuma yi hasashen cewa harkokin kasuwanci za su inganta a watan Mayu, Yuli, da Oktoba na shekarar 2026.
CBN ya bayyana cewa hasashen yanayin tattalin arziki gaba ɗaya ya tsaya a maki 3.9 a watan Afrilu 2026, yayin da hasashen wata mai zuwa ya kai maki 16.9, na watanni uku masu zuwa kuwa ya kai maki 27.0, sannan na watanni shida masu zuwa ya kai maki 34.6.
CBN ya ƙara da cewa kyakkyawan fatan ya samo asali ne daga “ingantattun manufofin faɗaɗa tattalin arziki (kashi 19 cikin ɗari), samun damar rance (kashi 13 cikin ɗari), da kuma tsammanin bunƙasar tattalin arziki ta fannoni daban-daban (kashi 13 cikin ɗari).”
Sai dai ’yan kasuwa sun nuna damuwa kan “matsalolin makamashi da ke ci gaba (kashi 35 cikin ɗari), matsalolin shugabanci (kashi 33 cikin ɗari), da kuma rashin tabbas na siyasar duniya (kashi 14 cikin ɗari).”
Binciken fannoni ya nuna cewa ɓangaren masana’antu ne ya fi nuna ƙwarin gwiwa a watan da ake dubawa da maki 8.8, sai noma da maki 2.7, sannan ayyuka da maki 1.5.
Rahoton ya kuma nuna bambancin yanayin kasuwanci tsakanin yankuna, inda kamfanoni a Arewacin Nijeriya suka fi nuna kyakkyawan fata fiye da na Kudancin ƙasar.
Yankin Arewa maso Gabas ya fi nuna kyakkyawan fata a dukkan lokutan da aka duba.






