• Gida
  • Labarai
  • Ƙasashen Duniya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Siyasa
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Mahanga
  • Rahoton Musamman
  • Wasanni
Thursday, October 1, 2026
New Citizen Hausa
  • Login
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni
No Result
View All Result
New Citizen Hausa
No Result
View All Result
Home Kuɗi Da Tattalin Arziki

Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji zai ƙara amincewar jama’a da tsarin haraji – Ministan Yaɗa Labarai

ABUBAKAR IBRAHIM by ABUBAKAR IBRAHIM
May 19, 2026
in Kuɗi Da Tattalin Arziki
A A
0
Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji zai ƙara amincewar jama’a da tsarin haraji – Ministan Yaɗa Labarai
Daga hagu: Shugaban Ofishin Ƙorafe-ƙorafen Haraji, Dakta John Nwabueze, lokacin ɗaya kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Alhaji Mohammed Idris ziyara a ofishin sa a Abuja a ranar Alhamis, 14 ga Mayu, 2026.

Daga hagu: Shugaban Ofishin Ƙorafe-ƙorafen Haraji, Dakta John Nwabueze, lokacin ɗaya kai wa Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai Alhaji Mohammed Idris ziyara a ofishin sa a Abuja a ranar Alhamis, 14 ga Mayu, 2026.

Gwamnatin Tarayya ta sake jaddada aniyar ta ta gina tsarin gudanar da haraji mai tsare gaskiya, tare da mayar da hankali kan buƙatun ’yan ƙasa, a wani ɓangare na Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan ranar Litinin a Abuja yayin ƙaddamar da gidan yana na hukumar da kuma cibiyar karɓar kiran waya kyauta ta ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji.

Ministan ya bayyana ƙaddamar da sababbin dandalan a matsayin wani babban mataki na ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin haraji a Nijeriya.

Ya ce: “Wannan wani babban mataki ne wajen ƙarfafa amincewar jama’a da inganta samun damar amfani da ayyuka tare da tabbatar da adalci a tsarin gudanar da haraji na Nijeriya.

“Ingantacciyar hanyar sadarwa da haɗin kan jama’a suna da muhimmanci wajen tabbatar da nasarar irin waɗannan sauye-sauyen tattalin arzikin.”

A cewar Idris, gwamnatin Shugaba Tinubu tana ci gaba da aiwatar da muhimman sauye-sauye domin ƙarfafa tara kuɗaɗen shiga, tabbatar da ɗorewar tattalin arziki da kuma bunƙasa cigaban ƙasa.

Ya ce: “Ƙarƙashin jagorancin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da jajircewa wajen gina tattalin arziki mai ƙarfi, mai ɗorewa kuma mai wadata ta hanyar muhimman sauye-sauye masu ma’ana.”

Ministan ya ce haraji yana taka muhimmiyar rawa wajen cigaban ƙasa ta hanyar samar wa gwamnati kuɗaɗen da ake amfani da su wajen bunƙasa ababen more rayuwa da kiwon lafiya da ilimi da sufuri da tsaro.

Sai dai ya jaddada cewa tsarin gudanar da haraji ba zai yi nasara ta hanyar tilastawa kawai ba, sai an gina shi bisa amincewar jama’a da gaskiya da adalci.

Ya ce: “Tsarin gudanar da haraji ba zai yi nasara ta hanyar tilastawa kawai ba. Dole ne ya samu goyon bayan jama’a tare da kasancewa bisa gaskiya da adalci da kuma ingantacciyar sadarwa.”

Idris ya bayyana cewa ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji wata muhimmiyar gada ce tsakanin masu biyan haraji da hukumomin haraji, domin tabbatar da cewa ’yan Nijeriya na samun damar gabatar da ƙorafe-ƙorafe cikin gaskiya da ƙwarewa.

Ya yaba da ƙaddamar da cibiyar karɓar kiran waya kyauta da kuma shafin gidan yana na hukumar, yana mai cewa hakan zai taimaka wajen sauƙaƙa sadarwa da samun bayanai da ayyuka.

“Ƙaddamar da cibiyar karɓar kiran waya kyauta tana nuna aniyar gwamnati ta kawar da matsalolin sadarwa tare da tabbatar da cewa ’yan Nijeriya za su iya neman bayanai da gabatar da tambayoyi da kuma warware ƙorafe-ƙorafen su ba tare da wata wahala ko ƙarin kuɗi ba.”

Ministan ya jaddada muhimmancin wayar da kan jama’a kan haraji domin ƙarfafa biyan haraji da kuma inganta kishin ƙasa.

“Wayar da kai kan haraji ba wai don tara kuɗaɗen shiga kawai ba ne, don gina al’adar haɗin kan ƙasa da ɗaukar alhaki tare ne,” inji shi.

Ya yi gargaɗin cewa yaɗa labaran ƙarya da rashin ingantacciyar sadarwa suna hana sauye-sauyen gwamnati samun karɓuwa tare da haifar da rashin amincewa daga jama’a.

Ya ce: “Yaɗa labaran ƙarya da rashin isasshiyar sadarwa sukan haifar da rashin amincewa da kuma ƙin karɓar sauye-sauye. Wannan yana nuna muhimmancin amfani da kafafen yaɗa labarai yadda ya kamata da kuma ci gaba da wayar da kan jama’a.”

Ministan ya sake tabbatar da cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai za ta ci gaba da tsare aiki tare da Ofishin Tax Ombud da sauran hukumomin da abin ya shafa domin wayar da kan jama’a kan sauye-sauyen haraji da haƙƙin masu biyan haraji da hanyoyin warware ƙorafe-ƙorafe.

Ya ƙara da cewa ingantacciyar sadarwa za ta taimaka wajen fahimtar rawar da haraji ke takawa wajen tallafa wa Ajandar Sabunta Fata da ci gaban ƙasa.

Ministan ya taya Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji murnar ƙaddamar da sabbin dandalan tare da kira ga masu ruwa da tsaki da su ci gaba da haɗa kai domin gina tsarin haraji mai gaskiya da inganci wanda zai amsa buƙatun ’yan Nijeriya.

Taron ya samu halartar Ministan Kuɗi kuma Mai Kula da Tattalin Arziki, Mista Taiwo Oyedele; Shugabar Ma’aikatan Gwamnatin Tarayya, Misis Didi Esther Walson-Jack; Shugaba kuma Babban Jami’in Gudanarwa na Ofishin kula da ƙorafe-ƙorafen haraji, John C. Nwabueze; da sauran manyan jami’an gwamnati da masu ruwa da tsaki.

Tags: John NwabuezeMohammed IdrisTax Ombudsman Office
Previous Post

Yadda muka ta cafke tsohon Ministan Wutar Lantarki Saleh Mamman a Kaduna bayan ya tsere – EFCC

Next Post

Binciken CBN: Matsalar tsaro ce babban ƙalubalen gudanar da kasuwanci a Nijeriya

Related Posts

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Gangamin CBN a Kano: A daina wulaƙanta takardun naira, a riƙe su cikin inganci da nagarta – CBN

September 29, 2026
Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Mun keto daji mai haɗari, amma mun fita lafiya – Cardoso

September 25, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

CBN: Tasirin rage kuɗin ruwa zuwa kashi 23% ga ’yan kasuwa da ’yan Nijeriya

September 24, 2026
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Shekaru uku a CBN: Yadda Cardoso ya sauya fasalin CBN, ya saisaita manufofin kuɗi, ya daidaita tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya

September 22, 2026
Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Rufe rassan bankuna 476 a Nijeriya cikin shekaru uku sakamakon juyin zamani ne, bai haifar da sallamar ma’aikatan banki ba

September 16, 2026
Tsakuren muhimman bayanai daga jawabin Gwamnan CBN a Taron Shugabannin Kamfanoni na 2026 wanda BusinessDay ta shirya
Kuɗi Da Tattalin Arziki

Lambar yabo daga NES ta tabbatar da ingancin manufofin CBN wajen tabbatar da daidaiton tattalin arziki — Cardoso

September 13, 2026
Next Post
Manyan nasarorin da CBN ya samu cikin 2025

Binciken CBN: Matsalar tsaro ce babban ƙalubalen gudanar da kasuwanci a Nijeriya

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

No Result
View All Result

Archives

  • October 2026
  • September 2026
  • August 2026
  • July 2026
  • June 2026
  • May 2026
  • April 2026
  • March 2026
  • February 2026
  • January 2026
  • December 2025
  • November 2025
  • October 2025
  • September 2025
  • August 2025
  • July 2025
  • May 2025
  • April 2025
  • March 2025
  • October 2024

Categories

  • Hotuna
  • Ilimi
  • Kiwon Lafiya
  • Kuɗi Da Tattalin Arziki
  • Labarai
  • Mahanga
  • Nishaɗi Da Al'adu
  • Rahoton Musamman
  • Siyasa
  • Tsaro
  • Wasanni
  • Ƙasashen Duniya
No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Ƙasashen Duniya
    • Ilimi
    • Kiwon Lafiya
    • Rahoton Musamman
    • Kuɗi Da Tattalin Arziki
    • Mahanga
  • Siyasa
  • Nishaɗi Da Al’adu
  • Wasanni

© 2024 New Citizen

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
error: Content is protected !!